TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
A jikin mota ta ganshi a tsaye ya rungume hannunsa. Farin yadi ne a jikinsa mai taushi wanda ya karbi kafar jikinsa sosai ya kuma fito da kyawun gyararriyar sumar kansa wadda ta sha gyara kuma take a bude. Bakin takalmi, bakin agogo da bakin tabarau, sai kuma kyakkyawan murmushi a fuskarsa. Zuciyarsa kuma cike da soyayyar hassanar sa.
Tayi masa murmushi itama. Sannan ta tako sannu a hankali tazo inda yake ta dan durkusa kadan ta gaishe shi. Ya amsa yana kara fadada murmushin sa. “Barka da fitowa uwar yayan Hassan” ta rufe fuska da hannunta. Yayi dariya yana karewa siraran dogayen yatsun hannunta kallo ya gyara tsayuwarsa yace “kinyi kyau sosai. Sai dai matsalar daya ce” ta bude fuskarta amma idanuwanta a kasa tace “wacce matsala kenan fa?” yace “wannan kunyar nake rokon alfarmar a rage ta ko yaya ne a bani dama inga cikin idanuwanki. Kullum su nake gani cikin baccina amma kuma a zahiri an hana mini ganin su” ta fara kokarin sake rufe fuskar ya hade hannayensa a guri daya yace “dan Allah, a tausayawa marayan Allah”.
Tace “maraya?” Ya cire glass din idonsa Yace “eh. Baki sani bako?” Tace “Allah yaji kansa” yace “Allah yaji kansu zaki ce. Duk su biyun babu” tace “ohhh, ya Salam, na dauka ai…..” Yace “Aunty? Ba ita ta haife mu ba, amma uwa ce a gare mu, haihuwar mu ne kawai baya yi ba”.
Ko cikin abokan sa ba kowa ne yasan cewa ba Aunty ce ta haife su ba amma wannan ai Hassana ce, wannan aurenta zaiyi kuma aure akan gaskiya ake gina shi.
Tayi masa gaisuwa sai ya bata brief labarin asalinsu da kuma cikakkiyar dangantakar su da Aunty, ya kuma lissafa mata sunayen kannensa mata sannan ya gaya mata irin soyayyar da yake wa yan’uwansa.
Itama kuma sai ga bashi labarin nata asalin da sunayen nata family members din da stage din karatun kowanne. A lokacin ne ta ga time din shigar da maganar Baba yayi. Tace “ammm akan maganar Baba” sai ta dago kai kamar yadda tayi plan cewa zata saka idonta cikin nasa ta gaya masa ya chanja wa baban ta aiki. Amma the moment da suka hada ido sai komai nata ya ruguje, wannan mutumin ba wannan mutumin bane daya same ta a toilet yace mata “help me Please” wannan wani mutumin ne daban. Wannan is so strong and so sure of himself. Wannan mutumin will not be controlled, not by her, not by anyone.
Ta sauke idonta kasa tana jin komai yana rushe mata, plan dinta duk ya ruguje, yace “uhum, ina jinki, me zaki ce min a game da Baba?”cikin sanyin murya tace “cewa zanyi dama an gode madallah da aikin da ka bashi” yace “noo. Babu godiya ai a tsakanin mu. Baba ai babanane, tunda nawa baban ya mutu kinga ai yanzu na samu Baba ko?”
Ta kuma cewa “an kawo mana sako kuma, mungode” ya dan bata fuska yace “sako kuma? Tace “eh” a ranta tana tunanin bashi din bane ba kenan, sai ta kara da cewa “Hussain yazo jiya, da dare kuma sai ya aiko mana da wayoyi ni da Sumayya da kuma kaya”
Hassan yayi dariya yana bayyana farin cikin sa yace “ya kyauta sosai. Ko gaya min bai yi ba. Hussain yana da kirki sosai yana kuma da kyauta sosai. Kinga ya rigani, ina ta lissafin siyan wayar amma bana so inyi laifi a gurin Baba tunda ban sani ba ko ba ya son kuyi waya yanzu”
Ta harare shi ta gefe yadda ba zai gani ba sannan tace “ai kuwa yayi fadan, sai da kyar ya bari” yace “to Alhamdulillah tunda ya bari ɗin, yanzu an kunna ta kenan a bani number in samu ta rage dare? Kinsan abinka da gwauro” tace “bamu bude bama, sai mun siyo sim card” yace “gobe zan aiko, da sassafe ma kuwa”
Sun dan jima suna hira, ita kanta Ruqayyah tasan taji dadin hirar Hassan yadda yake komai a nitse, sai kuma yace “naga alamar akwai sauro, gwara in barki ki koma gida kar ya cizar min ke ko?” Da haka suka yi sallama ya raka ta bakin kofa ta shiga sannan ya juyo.
A lokacin ne wata taxi ta shigo layin, mai taxin ya dan wuce motar Hassan kadan sannan yayi packing. Ya fito a dai dai lokacin da Hassan yake kokarin bude kofar motar sa. Ya mika masa hannu, sai da Hassan ya kare masa kallo ya ganshi dan karamin saurayi da ba zai wuce ashirin zuwa ashirin da biyar ba, ya mika masa nasa hannun suka gaisasai ya nuna gidan su Ruqayyah yace “dan Allah nan ne gidan su wasu twins masu kama daya?” Hassan ya gyara tsayuwarsa yana studying saurayin yace “eh nan ne ya akayi?” Saurayin yace “Okay dama gidan nake nema shikenan na gode” Hassan ya kuma cewa “me yasa kake neman gidan su?” Saurayin yace “ohhh, dama muna haduwa ne dasu yawanci a school dinsu, to kwana biyu ban gansu ba shine nazo in duba su kuma mu gaisa” Hassan yace “really? Da wa zaka gaisa a cikin su?” Saurayin yace “Ruqayyah nasan ba zata kula ni bama, so…..da Sumayya zamu gaisa” Hassan yayi murmushi ya nuna masa kofar gidan yace “bismillah” sannan ya shiga motarsa ya bar unguwar zuciyarsa fara kal. Hassanar sa mai kamun kai ce ita, Hassanar sa mutuniyar kirki ce.
Wannan littafi na siyarwa ne, in kina son siya ki nemi wannan number din 08067081020
Episode Fifteen : The New Driver
Adam ya bi motar da kallo har ta kule, shi dai bai ga alamar wannan mutumin daga wannan gidan ya fito ba dan bai ma yi kama da unguwar ba ballantana gidan. Waye shi? Kwalliyar da yayi da kamshin da yake yafi kama dana wanda yazo zance, amma zance gurin wa? Ya kalli nashi kayan jikin, basu mutu ba amma kuma ba zasu tsaya a jere dana wanda ya bar gurin ba.
Ya dan tsafa kansa yana kallon gidan, shi bai taba zuwa zance ba, sai kuma ya tambayi kansa in da gaske zancen yazo. Shi dai yasan yaran sun tsaya masa a rai, kamannin halittar su da bambancin halayyar su yana bashi mamaki kuma yana kara sawa yaji tsoron Allah a zuciyarsa. Wannan ya sa ya kasa cire su a ransa, sai ya mayar da makarantar su gurin zuwan sa kullum idan lokacin daukan dalibai yayi, a haka watarana ya gansu wata rana kuma sai dai yayi ta rarraba ido ba tare daya gansu ba, haka zai hakura ya koma gida.
To yanzu kuma kusan sati uku kenan kullum in yaje school din baya ganinsu, sai kawai yaji zuciyarsa babu dadi, haka kawai yaji shi lallai yana so ya gansu duk da cewa bashi da wani dalilin ganin nasu. Wannan yasa yanzu yana tashi daga aiki ya taho unguwar su yazo dai dai inda yake sauke su ya fara tambayar ko akwai wanda ya san su. Bai sha wahala ba “ohh Sumayya da Ruqayyah kake nufi? A can layin suke amma bansan gidan su ba, sai dai in kaje can din ka tambaya” yana shiga layin ya tambaya sai aka nuno masa gidan, sai kuma yaga wannan hadadden saurayin yana kokarin barin gurin.
Yayi ajjiyar zuciya yana tattaro duk courage dinsa. Bai san me zai ce musu ba, bai san kuma yadda zasu karbe shi ba. In sun tambaye shi dalilin zuwansa bai san me zai ce musu ba. But he is going to try, ko Ruqayyah zata wulakanta shi yasan Sumayya ba zata wulakanta shi ba, kuma shi bai damu da wulakanci ba, in da sabo ya saba, babu abinda bai gani ba. Ya ci dubu sai ceto.
Ya kira yaro ya tura shi, “kaje kace wai Sumayya tazo inji Adam” sai yaji abin odd, sai yayi murmushi sannan ya jingina da jikin motar taxi dinsa.
Yaron yana shiga ya bude muryarsa ya kwada sallama sannan ya fadi sakonsa “kutumelesi! Wannan dan rainin hankalin me ya kawo shi gidan mu? Uban waye ya nuna masa gidan mu” Inna Ade tace “ke Ruqayyah! Menene haka? Ban hana ki irin wannan maganganun ba?” Ta juya kan Sumayya “waye kuma Adam? A ina kika samo shi shi kuma?”