TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Aunty Amina ta share hawayenta, dama Hussain shi take tunani, tasan shi da rigima, tasan shi zai bata problem, tace “to Hussain ya kake so muyi? Eh? Ya kake so inyi da raina? In bamu koma Gombe ba ina zamu je? Wa zai rike mu? Ni dai kasan ba zan iya ba, kasan ba aiki nake yi ba ba sana’a nake yi ba, kasan kuma ba dogon karatu nayi ba ballantana in saka ran zan samu aikin da zan rike ku dashi. Ku kuma baku kawo karfi ba tukunna, kuma mai taimaka muku kuke bukata a yanzu, kuna bukatar wanda zai shige muku gaba ku cigaba da karatun ku. Yan uwanku yaya zakuyi dasu? Duk fa primary suke Hassana ce kawai take ajin farko a secondary. Hussain dole muna bukatar taimako, ba kuma zamu samu taimakon nan anan ba sai mun koma cikin yanuwanmu”.

Ya mike tsaye yana girgiza kai yace “duk wanda yake bukatar taimaka mana a cikin yanuwanmu ai zai iya taimaka mana muna zaune anan. Kuma ma ai bama bukatar taimakon kowa aunty. Mu, ni da Hassan zamu rike kan mu zamu rike ku” Hassan ya mike yana kallon sa yace “ta yaya? Ta yaya zamu rike kan mu Hussain? Gaya min me muke dashi? Ko da karambani zamu rike kan namu? Ana maganar reality ne fa anan, ana maganar future din mu ne data yaran nan kannen mu” Hussain yace “in ba zaka iya ba kawai kace ba zaka iya ba ba sai kayi min dogon sharhi ba” ya wuce shi ya dawo gaban Amina. “Aunty ki yarda dani dan Allah. Wallahi zan iya” tayi ajjiyar zuciya tace “zaka iya? Ta yaya?” Ya zauna a kan kafafuwansa yace “kasuwanci zan shiga, ba da akwai kudade a hannun mu ba? da akwai wasu a bank? Ga kuma motoci har guda uku a waje? Kuma ga filayen da Abba ya siya ya ajiye? Mu siyar dasu ku bani kudin in shiga business dasu……….”

Hassan ya dawo kusa da Aunty da sauri yace “hauka ma kenan. Yanzu in business din zamuyi Hussain sai mu dauki dukiya mu baka? Kai din? In ka lalata ta kuma shikenan sai mu dawo mu zuba tagumi? Gaba ake dubawa Hussain. Komai a hankali a kuma nutse ake binsa, kullum sai na gaya maka wannan amma kai baka ji”

Hussain yayi masa kallo daya ya dawo da dubansa kan Aunty yace “Please Aunty, ki bani wannan damar dan Allah. Wallahi zan iya, ki rabu da Hassan. Shi yana living ne in the future ni kuma ina living now, in dama tazo wa mutum kawai yayi amfani da ita ba sai ya jira wata damar tazo sanda yayi masa dai dai ba.

Yanzu ne damar mu Aunty, ki bani wannan damar dan Allah.

Aunty ta jima tana kallon sa, tasan halinsa sarai, tasan karambanin sa da daukan abinda yafi karfinsa ya dora wa kansa, tasan kuma kokarin sa dan duk sanda ya fadi baya zama a kasa yayi kuka mikewa yake yi ya cigaba da tafiya. Duk abinda yake bashi wahala kuma sai yayi ta maimaita wa har sai ya iya.

Ta tuna farkon sanda aka siyo musu kekuna, ana kawowa Hussain ya dauka ya hau ai kuwa ya fado ya kukkurje, amma bai hakura ba, yayi ta hawa keken nan yana faduwa har sai da ta dauke saboda tausayin sa sai babansu yace ta bar masa ai a haka ake girma. Hassan kuwa sai yayi ta studying keken nan yana gwada yadda komai nasa yake aiki har sai da ya fahimce shi sannan ya hau, shima kuma a hankali yadda ko ya fadi ba zaiji ciwo ba, kuma bai fadin ba, sai yake tukawa a hankali yadda in yaga zai fadi sai yayi sauri ya sauka, ko kuma yake bin jikin bango yana dafawa.

A karshe sai ya zamanto Hussain ya riga Hassan iya keke, amma kuma duk ya ci uban keken nasa ya babballashi. Sanda Hassan ya iya nasa keken, keken Hussain ya riga ya lalace.

Amma kuma akwai wani abu a dangane da Hussain tun yana yaro, yana balain, tsananin son sana’a. Duk wani abu indai ance abinda zai kawo kudi ne to Hussain ya sanshi kuma yana sonshi. Hussain har fruits din bishiyar umbrella din gidansu yake cira ya siyar wa da yaran unguwa. Hussain in yaje da abu makaranta wani yaron yace yana so yakan iya siyar masa ya kara riba sannan ya fito waje ya sai wani. Amma fa kudin in ya samu rabarwa mutane yake yi.

Ta tuna wata rana da ya dawo daga school da ulu da kwarashi, ta tambaye shi inda ya samu sai yace “Nanny din mu ta makaranta na gani tana saƙa, tace min ana samun kudi sosai in akayi saƙa, shine na bata kudi ta siyomin zan ringa yin saƙar hula ina bata tana siyar min” sai da baban su ya zane shi akan sakar nan sannan ya daina.

Babansu ya taba tambayar su abinda zasu zama in sun girma. Hassan yayi shiru yana tunani sannan yace “ban sani ba Abba, sai nan gaba in nayi tunani” ana tambayar Hussain sai ya washe baki yace “Dangote”.

Ta dawo da tunaninta kansa da har yanzu yake durkushe a gabanta yana roko, ya kamata ta bashi dama, amma ya kamata tayi tunani, saboda kamar yadda Hassan ya fada wannan future dinsu ne basu kadai ba harda yan kananan yaranta mata. Dole zata yi tunani kafin tayi taking wannan risk din kuma dole zata yi shawara. Shawara da abokin shawarar ta sarkin tunani. Hassan.

Tace “shikenan Hussain ka bani lokaci inyi tunani, duk abinda na yanke kuma shine final babu jayayya”

Ba haka yaso ba, amma yadda take so dole hakan za’ayi.

Bayan ya fita sai ta juyo ta kalli Hassan, a take ya girgiza mata kai.
Ta sauke ajjiyar zuciya tace “bana son discouraging dinsa, ka bani shawara yaya zanyi?”
Ya gyara zama yana kallon carpet yace “dukiyar marayu ce aunty, ina ji masa tsoro, kinsan halin Hussain in ya kafa kasuwancin ma raba wa mutane zai tayi” Ta gyada kai cikin fahimta, ya cigaba da cewa “a shawarce ina ganin a raba, a fitar masa da kasonsa a bashi ya kafa kasuwancin dashi yadda ko sun rushe ba zai rusa mu gabaki daya ba, mu dashi zamu samu abinda zamu dogara dashi. Idan kuma ya zama successful sai a kara masa wata”

Aunty taji dadin wannan shawarar, amma kuma a ranta bata son rabon gadon nan saboda tana ganin kamar raba kan ƴaƴanta ne, taso a ce komai zasuyi tare zasuyi. Amma kuma shawarar abar dubawa ce.

Haka akayi, aka raba gado aka bawa Hussain nasa, sauran kuma suka ajiye suna amfani dashi gurin harkokin rayuwarsu. Hassan yayi amfani da wani kaso a cikin nasa gurin nema wa kansa makaranta.

A lokacin da shekara ta zagayo Hussain ya kira su yana nuna musu lissafin abubuwan da yayi da kudin da ya samu sai su ka ga cewa kudin da yake dashi a yanzu ya ninka wanda yake dasu a waccan shekarar sau huɗu har da doriya. Suka rike baki suna mamaki, shi kuma ya gyara zama yana murmushi yace “na gaya muku ai, Dangote zan zama”

Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only

Sai na jiku….???????? TAGWAYE ????????

By

Maman Maama

Free episode

Episode Four: Gimbiya Fatima

Hayin Rigasa,
Kaduna state
Yammata biyu na gani suna shigowa cikin gidan su wanda katangar sa ta kasa ta zube dan haka aka zagaye shi da tsohon langa langa, sai dakuna guda biyu a tsakiyar gidan suma dakunan na kasa ne amma anyi musu plaster da siminti, a gefe akwai bandaki shima rabinsa na langa langa ne kuma babu rufi, tsakar gidan gabaki dayansa kasa ne da bishiya a gefe a kasanta akwai murhu da tukwane da sauran kayayyakin da suke nuna anan ake girki, sai kofar dakunan da akayi yar karamar baranda, wadda simintin ta duk ya mutu yayi ramuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button