TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta sunkuyar da kanta ai taji shima yayi shiru bai kuma cewa komai ba, ta dago kai sai taga bacin rai a fuskarsa, ya juya yana cewa “it is okay, bara in tafi before I put you in trouble” yayi taku biyu tace “Adam” sai ya dakata amma bai juyo ba, ta karasa inda yake ta zagaya ta gabansa tana noticing kirar jikinsa, tace “Igbo, hausa, fulani, yaroba, Igala, kanuri duk ba shine mai muhimmanci ba, babu wanda yafi wani muhimmin a gurin ubangiji sai wanda yafi tsoronsa” ya gyada kai yace “na sani, but a gurin ubangiji kika ce ai, ni kuma a gurinki nake tambaya, can you…….marry an Igbo guy”.

Ta kuma sunkuyar da kanta kasa, maganar aure ba karamar magana bace ba, sai ta juya maganar tace “ba la san hausawa yanzu cewa suke auren wani yaren yafi dadi ba? Yace “hausawa ne suka fada ko ke ce kika fada? Ni view dinki nake son ji ai bana haudawa ba” da daga kai tana kallonsa a cikin hasken farin wata, ita dai tasan he is the most handsome man data taba gani a rayuwarta, fuskarsa irin fuskarnan ce da in ka kalla ba ka iya cire ta daga ranka.

Tace “my view, tribe doesn’t matter, what matters is the person himself. In dai kasan mutumin da zaka aura kuma dabiun sa sunyi maka kuma shima haka, tribe dinku doesn’t matter” yayi murmushin daya kara wa fuskarsa kyau yana kallon cikin idonta yace “then, nayi miki?” Tayi kokarin cire idonta daga cikin nasa amma sai taji ta kasa, sai taji bata so, she want to live there forever. Kasa kasa tace “I can’t say, I don’t know you” shima kasa kasa yace mata “I know you and I like you” taji maganar sa ta shige ta har cikin ƙafafuwan ta sai tayi saurin cire ionta daga nasa ta zagaye shi tana tafiya zuwa gida tace “good night Adam” bai juyo ba yace “good night Sumayya”.

Taji sautin dariya a cikin muryarsa itama sai tayi murmushi. A tsakar gida still da murmushi a fuskarta suka kusan cin karo da Ruqayyah. Yace “na jiki shiru, nace bara inbi sawu inji ko lafiya” Sumayya ta wuce ta tana cewa “ya tafi ai yariman naki, tun dazu” Ruqayyah ta bita a baya “and? Ina sakon?” Sumayya tace ba tare data kalle ta ba “bai bani ba komai ba, gaisawa kawai muka yi, sai dai ki kira shi ki sake tambayarsa ko ya kuma mantawa ne”. Ruqayyah tayi tsaki tana kananan maganganu ta wuce Sumayya ta shige daki.

Sumayya bata gaya mata zancen zuwan Adam ba kuma bata da niyyar gaya mata din saboda tasan zata iya gayawa Inna, ita kuma tafi son in Inna zata ji ma ya kasance daga bakinta zata ji bana wani ba.

A dakin su ta kwanta still da murmushi a fuskarta, idonta a lumshe tana tuno murmushin Adam, Ruqayyah ta kalle ta tayi tsaki tace “this one that you are smiling kamar wadda aka yiwa kyautar mota” Sumayya ta sake murmushi tace “abinda aka bani yafi mota muhimmanci a gurina. But I guess ke ba zaki fahimta ba”.

Saturday family din Aunty baki dayansu banda Hussain da baya kasar suka tafi Gombe, a can suka yi weekend, a cikin weekend din ne kuma suka shigar da maganar neman auren da Hassan yake yi suka nemi alfarmar azo a nema masa officially. In kuma anje naman an bayar din suna so a saka rana ta zama daya data Hussain da kuma Hassana.

Ranar Monday suka dawo da safe, Hassan ne ya sama suka yi fitowar sassafe saboda yana so yaje office akwai abubuwa da yawa a gabansa. A office din ne bayan ya gama abubuwan da yake yi sai yaga kiran wani agent da ya saka ya samo masa gida. Ya daga a ransa yana tunanin an samu kenan. Dan yasan in baa samu ba mutumin ba zai kira shi ba tunda specifically ya yi masa bayaniy irin gidan da yake so, hatta girman gidan, yawan dakunan da tsarin dakunan sai daya lissafa masa. Shi komai nasa a tsari yake yin sa and he sticks to wannan tsarin nasa. Ba dan emergency yake neman gidan ba ma da gina wa zaiyi yadda zai yi exactly irin yadda yake so.

Tun sanda Allah ya hada shi da Ruqayyah da family dinta yake tunanin mai ya kamata yayi musu, farko yayi tunanin kudi, sai kuma ya fahimci Baba ba mutum ne mai son ake bashi kuɗi haka nan ba, ya san in zai karba ma sai sun kai ruwa rana kamar yadda suka yi ta yi akan aiki, kuma shi yana ganin girman sa sosai baya son yayi tayi masa musu.

Wannan yasa ya yanke shawarar siya masa gida saboda ganin yanayin yadda gidan nasu yake ciki. Dama yana da kuɗin sa da yake tarawa, kudin albashin sa a matsayin sa na chief of staff na H &H group of companies. Tun sanda Hussain ya bude kanfanin sa na farko ya bashi wannan matsayin kuma shi yake running kusan komai, ma’aikata da yawa basu san Hussain ba Hassan suka sani. Da yawa daga cikin su kuma suna yi masa kallon kamar shine mai gurin shi kuma bai taba tsayawa yayi wa wani bayani ba saboda yana ganin babu bukatar yin bayanin.

Albashin sa account dinsa yake shiga kawai, baya taba using dinsa sai dai in zai siya wa kansa wani personal abu kamar kayan sawa ko kuma in zaiyi wa wani kyauta, amma duk kudin da ake kashewa a gidan su, duk bukatun Aunty da yammatan ta, duk motar da take cikin gidan na Hussain ne, shi yake komai amma ta hannun Hassan, check book ya samu duk yayi signing ya ajiye a dakin sa yace da Hassan “duk abinda ake bukata kawai ka cike ka fitar ba sai an neme ni ba, ni bani da lokaci kar inje inke manta important things”.

Amma Hassan bai taba cirar ko da kwandala yayi buƙatar kansa ba…..

Da lissafin sa shine zai yi amfani da kudinsa gurin siyawa kansa gidan da zasu zauna shida iyalinsa in yayi aure, amma kuma sai ga Hussain ya sai gida ya fara gina musu tare. Abinda ya saka baiyi rejecting ba shine idea din tayi masa kyau na zamansu tare, iyalinsu tare sannan kuma a kusa da su Aunty. Yana ganin wannan zai karfafa zumunci a tsakanin yayansu da matansu. Amma duk da haka sai ya kuduri aniyar gina gida da kudinsa ya ajiye shi a matsayin nasa in yaso ko haya ya bayar. Tunda dai gidan da zasu zauna din na Hussain ne dan bai furta yace ya bar masa kyauta ba, kuma baisan abinda gaba zata haifar ba.

Sai dai kuma yanzu ga Hassana ga iyayenta da kannenta, wanda Hassan yake jin yanzu kamar sun zama responsibilities dinsa. Dan haka yayi niyyar daukan kaso mai tsoka a cikin ajjiyarsa ya siya musu gida. Shi nashi ginin can wait.

Ya daga wayar yana cewa “an samu kenan” mutumin yace “an samu oga Hassan, naga kamar yayi dai dai da bukatar ka sai dai in ka samu lokaci sai inzo muje in kai ka ka gani kafin ayi finalising” Hassan ya yarda da hakan, gwara yaje ya gani da idonsa kar ya sayi abinda bashi yake so ba.

Washegari da sassafe kafin yaje office agent din yazo ya dauke shi suka je ganin gidan. Madaidaici ne kamar yadda ya bukata. Cikin gidan akwai dakunan bacci guda uku da kuma madaidaicin falo kowanne daki kuma da bandaki a ciki. Sai tsakar gidan da aka rufe kasan sa da interlocks, sai kitchen da bandaki a tsakar gidan. Akwai kuma dan siririn soro, a cikin soron akwai daki wanda yake da kofa guda biyu daya ta soro daya ta tsakar. Ya gyada kai cikin gamsuwa, komai yayi yadda yake so kawai dai yaso a samu shago a kofar gida inda yayi niyyar zubawa sulaiman kayan provisions ya ringa siyarwa inya dawo daga school. With that and salary din daya yi doubling ya bawa Baba, da kuma shi a matsayin sirikin gidan, yana ganin they are set for life.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button