TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A hanya ne yake ce musu. “Ya kuka ga gidan? Yayi muku? Suka yi dariya, Sumayya tace “yayi mana, sosai ma kuwa. Mungode mungode Allah ya saka muka da alkhairi Allah ya biya ka da aljanna” yace “ameen na gode nima da addu’a. Yanzu abu daya nake nema daga gurinku shine ku taimaka ku lallaba min Baba ya yarda ya karbi gidan nan. Ku hada kanku ku nuna masa kuna so ya karba. Kunji”

Duk suka amince, ya juya yana kallon Ruqayyah da take ta zabga murmushi yace a hankali “do you like it” tace “sooo much. Yayi kyau sosai. Mungode Allah ya saka da alkhairi” yace “bana hana ki yi min godiya ba? Duk abinda nake dashi naki ne, to menene in mutum yayi amfani da abinsa?” Taji wani irin dadi a ranta, duk abinsa nata ne, tabbas bata da sauran wata damuwa a duniya.

Bayan ya ajiye su ne yace musu, “bayan gida kuma, akwai Napep da Hussain ya bashi shima saboda transport da kuma ko zai kezagayawa dashi, na san Baba baya son zaman banza” ya karasa maganar yana fadada murmushin sa. Sumayya ta taya shi murmushin “lallai kasan Baba. Ai kuwa Hussain ya kyauta sosai ayiwa Baba Godiya”

Sama sama Ruqayyah take jinsu. Tunda kalmar Napep ta shiga kunnuwan ta taji kunnen ya toshe. what? Baban nata ne zaike yin hayar Napep bayan ya taso daga aikin gadi? Ta juya ba tare da tace da kowa komai ba ta shige gida. Hassan yana sallama da yaran vai lura da shigar ta ba sai daya waigo yaga bata nan. Ya ji babu dadi, ya so su dan taba hira kadan amma kuma sai ya bata uzuri da maybe ta gaji ne, gashi kuma dama tace kafarta tana ciwo.
.
Ruqayyah tana shiga gida ta fara masifa “Napep fa yace, wannan wanne irin cin mutunci ne da cin fuska. Me nayi wa Hassan da zai ke wulakanta ni irin haka? Wannan ce sakayyar da zai yi wa taimakon da nayi masa?” Sumayya data biyo bayan ta tace ” ke baiwar Allah! Yanzu menene laifin Napep din? Menene laifin wanda yaso mahaifin ki da arziki?” Tace “arziki? Ina arzikin yake? Napep din ne arziki? Mutumin da na tseratar da rayuwar sa shine zai jefi ubana da keke Napep? Ji nake a sanadiya ta ne ya samu ransa, kuma ya samu dukiyar sa daga hannun wadanda suka sace shi. Ji nake naira billion daya aka xe an karba daga hannun barayin kuma an bashi kayarsa? Me ya bani a ciki? Me ya taba bani? Sim card din?”

Sumayya tace “wannan ra’ayin sa ne ya baki ko ya hana ki, ganin damarsa ce. Amma ya kamata ace abinda kika samu daga gare shi ki gode Allah. Yaushe rabon da kinkwana da yunwa? Yaushe rabon da kici mai da yaji? Ji nake duk a dalilin haduwarki dashi ne? Yanzu kayan da suke jikinki ta dalilin wa kika samu. Ina laifi? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki aiki ya daina leburanci da turin baro? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki Napep yace yayi sana’a dashi? Gidan daya siya mana kuma fa? Mai tilesda ac da ban dakin water system? Shima duk bai kyauta ba?”

Ruqayyah tace “wannan kuturun gidan kike magana akai? Ai wannan gidan is nothing in aka duba irin dukiyar sa, wannan gidan ai bai kai gidan da a za’a nuna ace ga gidan surukan mutumin daya mallaki kamfanoni ba. Ban taba lissafin cewa zan auri mai kudi ba sai da na hadu dashi, ban kuma san cewa marowacin mai kudi zan aura ba sai yau. Wallahi yayi da yar halak, ba dai za’a yi bikin ba? Ba dai zan shiga gidan sa a matsayin matarsa ba, wallahi sai na chanza masa takunsa tunda dai ace duk motocin da yake ta shiga yana fita dasu ya rasa wadda zai bawa mahaifina sai ya bashi Napep. Wallahi har wannan gidan sai ya chanza in dai yana son zaman lafiya”

Ta wuce Sumayya kamar kububuwa. Duk maganganun su Inna Ade tana tsaye akan baranda tana jinsu. Sai da Ruqayyah ta zo zata wuce ta sannan tace “zo nan Hassana” ta dakata da tafiyar da take yi amma bata juyo ba ballantana Inna Ade ta saka ran amsawa. Inna Ade tace “yanzu rashin godiyar Allahn naki har ya kai haka Ruqayyah?” Ruqayyah tayi magana kasa kasa sannan ta juya zata shige daki. Inna ta saka hannun ta na hagu ta finciko ta baya sannan ta saka na dama ta wanke ta da mari tace “watakila wannan ya dawo dake cikin hayyacin ki”.

Hussain yana ta shirye shiryen sa. Gida ya kammala, an gama finishing touches da komai. Takanas aka yo masa yawa daga masarautar kano akan cewa kar ya saka wa Fatima komai a dakunan ta. Bai so haka ba, amma sai ya bar musu ya fara zuba kaya a nasa dakunan, the best of the latest of komai yake sakawa. Hassan ya fada tuntuni cewa shi zai yiwa da Ruqayyah kayan daki. Amma kuma Hussain ya ga shiru, kullum in yayi masa magana ko kuma yayi masa tayin wani design na kaya sai yace ai zaiyi ne “tunda nace maka zanyi ka bar ni mana, ina ta planning irin wadanda zan saka da wanda zan saka mata, ba lallai ta so irin naka ba kasan taste dinta ba irin na gimbiya bane ba” Hussain yace “ka tambaye ta ne kaji wanne taste ne da ita? Ko kuma dan sunan ta Hassana sai ya zamanto tana da ra’ayi irin na Hassan?”

Daga nan bai kuma bi ta kan Hassan yakira kamfanin daya bawa kwangilar nasa aikin yace su shiga gidan Hassan su saka komai “kaya masu kyau zaku saka a ko’ina, karku gaya masa, in kuma yazo ya same ku kuna aikin kuce masa ni na saka ku” ai kuwa kamfani suka zage dantse suka fara kure adakar su a gidan Hassan. Gashi dai gidan ba za’a kira shi da katon gida ba amma kuma sanda suka gama aikinsu sai ya zamanto kyan da gidan yayi ba karami bane ba. Babu abinda zaka kalla ba tare da ka kuma kallo ba.

Sanda Hassan ya samu Hussain da fadan me yasa ya taba masa gidan sa sai yace “ba kai na sakawa ba, Ruqayyah na saka wa. It is my wedding gift to her, it is just my little way of saying thank you for saving my brother”.

Kuyi hakuri in kunga typos……

Wannan littafin na siyarwa ne, duk mai so tayi min magana ta wannan number din 08067081020.

No calls please, WhatsApp only.
Please no calls, WhatsApp only.Eighteen : His Religion

Ranar da Hassan ya bawa Adam complimentary card dinsa, a hanyar sa ta komawa gida yana ta bitar hirar su da Sumayya yana murmushi, yana mamakim kansa yadda har ya iya ce mata he likes her. He saw the look in her eyes kuma ya fahimci abinda take tunani, alaka tsakanin su zata yi wahala gaskiya, bazai ce impossible ba saboda yasan babu wani abu da yake impossible agurin ubangiji, idan Allah yayi zasu kasance tare to ko sama da kasa zasu hadu tabbas sai sun kasance din.

Rayuwar sa kadai ta isa misali a gurinsa na cewa nothing is impossible indai aka saka Allah a ciki. Bai taba tunanin zai yi wannan rayuwar ba, sanda ya fara ta kuma bai taba tunanin zai yi surviving ba amma gashi nan yanzu har ya saba. Da dadi ba dadi he still prefers wannan rayuwar akan wacce ya baro a baya.

Yanzu gashi cikin ikon Allah da kudirarsa sai gashi ya fada hannun ogan h and h, gashi har yace yaje ya same shi a office zai bashi aiki, wai aiki a matsayin driver. Still yana feeling excitement in ya tuno da yadda aka tsara masa aikin, irin benefits din gaskiya abin ya burge shi sosai. Dan haka monday da sassafe yana tunanin shi kansa Hassan din sai dai yaje office ya same shi yana jiran sa. Fatan sa kawai kar ya ganshi cikin hasken rana ya fahimci ko wanene shi yace ya fasa bashi aikin. Kamar yadda yake tsoron ranar da baban Sumayya zai kama shi yace kar ya sake dawo masa gidan sa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button