TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka ya karar da weekend din nan cikin saka da warwara, sai dai ko sau daya tunanin sa bai bashi cewa ya fasa zuwa ba dan shi mutum ne da yakan doshi abu ko da kuwa yasan da illarsa ballantana wannan da bai tabbatar ba, dan haka monday nayi ya shirya ya tafi, sai ya zamanto har ma ya riga shi kanshi Hassan din zuwa office din. Ya zauna ya jira har aka ce masa yazo, sannan aka sanar da Hassan zuwan Adam sai yace ya jira shi. Daga nan Adam ya zauna jira, shiru shiru shi dai yana zaune yana jira yana kuma lissafa yadda rayuwarsa zata kasance a matsayin drivern gidan masu kudi, yayi murmushi yana girgiza kansa yana tuna drivers din da suke gidansu yana kuma zaben wanne daga ciki zaiyi koyi da, but sai dai duk cikin su babu yaro karami kamarsa, babu mai background irin nasa dan haka babu wanda rayuwarsu zata zo daya.

Ba zaiyi koyi da kowa ba he is going to live as himself.

A haka aka leko aka kira shi. Ya shiga yana kallon fuskar mutumin da suka gaisa ranar nan amma da yake ranar da daddare ne sai yanzu ya samu ya ga cikar halittar sa da kwarjinin sa. A ina Ruqayyah ta samu wannan? Me yasa ya zabi Ruqayyah a matsayin matar aure? When? Where? How? Why Ruqayyah bayan duk yammatan da suke gari babu wadda zai ce yana so tace a’a? Sai kuma yayi saurin kawar da tunanin sa daga kan maganar, zuciyarsa tana kwabarsa da cewa “ina ruwanka? Kai da kazo neman aiki ina kai ina bin diddigin insa ogan ka ya samo budurwar sa?

Ya zauna akan kujerar da Hassan ya nuna masa sannan ya gaishe shi, ya amsa yana rubutu a takardar da take gabansa, sai Adam yaga kamar he is not as nice as he was ranar nan. Sai da ya gama rubutun sa ya dago kai sannan yace “barka da zuwa. Sorry I kept you waiting. Ban dauka zaka zo yau ba ban kuma dauka zaka zo da wuri ba, already akwai masu appointment so I have to see them first. Ina fatan ka gane” Adam ya gyada kai da sauri. Sannan Hassan ya tambaye shi full name dinsa. “Adam…….” Hassan “Adam who? Adam ya dauke kansa gefe yace “Adam Clement Young” ya fada yana studying Hassan yana so yaga yadda zaiyi reacting to the name amma sai yaga ya rubuta ba tare da yanayin fuskarsa ya chanja ba. Daga nan ya cigaba da jero masa tambayoyi, “age” “23” “tribe” “igbo” “state of origin” “imo” “religion” “islam” haka suka yi tayi yana jero masa tambayoyi akansa shi kuma yana amsawa, ya tambaye shi contact address dinsa sai ya bashi adireshin dakin da yake haya sai kuma ya tambayeshi permanent home address sai ya kuma bayar da same address. Hassan ya dago yana kallonsa sai shi kuma ya sunkuyar da kai, Hassan ya ajiye biron hannunsa yace “for this, you have to give me address din inda mahaifanka suke, gidan ku nake son sanin a ina yake” Adam yace “Kano” Hassan yace “kano wacce unguwa, wanne layi wanne number din gida?” Adam ya dago kai yace “that’s a very private question” Hassan ya bude baki cikin mamaki yace “you think so? I am about to give you a very private job na entrusting rayuwar only brother dina a hannunka, and you are telling me address din gidan ku is a private thing? I have to know as many things as possible akan ka kafin in iya baka wannan aikin”.

Adam ya gyada kai, ya yarda da abinda yake cewa but it is just that bai fiya magana akan parents dinsa ba sai in ta kure, kamar yadda ta kure yanzu dan gaskiya yana son wannan aikin sosai saboda chance din da ya gani a cikin aikin na komawa makaranta. Yana son karatu sosai. Dan haka ya fada “house number 14, badawa layout, Nassarawa local government, kano state”

Daga nan tambayoyin suka ci-gaba kamar ba zasu kare ba, “wannan mutumin da bin kwakwkwafi yake” Adam ya fada a zuciyarsa. Sai kuma ya yi kokari wajen ganin cewa ya fadi gaskiya to the best of his knowledge. Sai da suka gama sannan Hassan ya rufe file din gabansa and for the first time tunda ya shigo yayi masa murmushi yace “that will be all. Kayi kokari sosai, but I will have to run a background check on all what you said, ba zai dauki lokaci ba zan gama within this week next week insha Allah zan kira ka in gaya maka yadda ake ciki” Adam yaji gabansa ya fadi, ya dago da budaddun idanuwa yana kallon Hassan, Hassan ya daga kafada yace “yes now, ta haka ne zan tabbatar da gaskiya, ko akwai wani abu da kake boyewa ne?” Adam ya sunkuyar da kansa yana girgiza kansa, wani bari na zuciyarsa yana gaya masa cewa yace ya fasa neman aikin amma kuma ita magana ai kamar zarar bunu ce inta fita bata komawa. There is no going back. Fatan sa kawai in Hassan ya samu abinda yake fatan kar ya samu to kar ya gayawa Sumayya. Idan zai gaya mata to shi zai gaya mata da kansa.

Adam yana fita Hassan ya dauko wayarsa yayi kira “Hello. Kanawan dabo. Kana lafiya? Ya iyalin? Dan Allah dan wani taimako nake nema, zan turo maka info din wani yaro ina son kadan bincika min shi. Eh nan kano yace min unguwar badawa. Okay, just find out if there is anything that I should know about. Thank you.” Ya kashe wayar yana murmushi, rami ya gina wa Adam kuma ya fada ciki.

Tun sanda ya ganshi yana zagaya gidan Baba kuma ya fahimci gurin Sumayya yake zuwa kuma ya fahimci cewa ita ma Sumayyan kamar tana da interest akansa sai ya kudurce a ransa yana so yayi bincike akansa amma ya san ba zai bashi hadin kai ba shine ya yaudare shi da aiki dan yaga alamar yana bukatar aikin, yanzu sai yayi binciken sa sosai akansa, in ya samu alkhairi zai bashi aikin kuma yayi masa jagora zuwa ga Sumayya in kuma ya samu sharri sai yayi warning Sumayya kuma aikin ma ya bi ruwa.

Bayan ya tashi daga aiki ne ya koma gida ya tarar Aunty tana palo tana jiransa “kudin nan fa sai ka karo su Hassan. Kaya gasu an fara siya basu fi rabi ba amma kudi sun kusa karewa, ko boxes din ba’a siya ba. Ga sauran kayan al’ada da ake yi duk ba’a siya ba” ya shafa kai, “aunty, kayan nan wai me zata yi ne dasu? Ji nake dai sakawa zata yi a jikinta in tazo gidana ko? To ba gani ba muna tare? In tazo din duk abinda take so ai za’a siya mata” Aunty ta girgiza kai tace “ba shi kadai ne amfanin lefe ba, ai ana rabawa dangi, kusan rabin kayan ma rabarwa ake yi ballantana su da ba masu kudi ba ai kaga duk zasu so su rarrabawa dangi suma su samu albarkacin ta ko? Shi yasa nake siyan kayan kashi biyu akwai masu tsada sosai akwati daban za’a saka su a matsayin nata, masu dan saukin kudi kuma sai a siya da yawa a basu a ce a raba wa yan’uwa” yayi ajjiyar zuciya “mata dai da al’ada. Shikenan nawa za’a karo yanzu?” Ta gaya masa, ya bude baki yana mamaki tace “to boxes din ma set uku zan siya, biyu nata daya na rabo” ya rufe bakin yace “set daya ya ishe ta, set daya na rabon. Yarinyar nan ba sabawa tayi da irin wannan spending kudin ba, nafi so kuma ta cigaba a haka. In an siya da yawan ma sai dai tayi ta ajiiyar su sai a hankali zata saba da amfani da wasu abubuwan ma. Dan haka gwara a bari in tazo din ta fara sabawa a hankalin sai ake introducing dinta to sauran abubuwa” Aunty tace “in an siya mata a kayan lefen nata ai dole zata koya, in bata dasu ta yaya zata koya? Kuɗi fa sai ka fito dasu komai wayon ka” yayi dariya yace “shikenan Aunty, zan kawo gobe” tace “yauwa, kuma ina son inji yadda kuka yi da ita akan sauran hidimomin biki, nawa zaka bata?” Ya sake bude baki “bikin ai da saura ko” tace “sauran wata daya ba? Yanzu lokacin yadda yake gudu kafin ka gama lissafin ka wata dayan ya kare. Kaje ku zauna da ita ta fada maka shirye-shiryen ta sai ka lissafa ka bata abinda zai ishe ta” ya mike tsaye yana cewa “an gama Aunty” tayi dariya tace “zaka gudu ko? To ai ban gama da kai ba” yace “in na cigaba da zama sai kaina ya kunce saboda lissafin kudin da za ki cigaba da yi min”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button