TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Sumayya ta tashi zaune tana cewa “to baki sani ba ai koya gama shirya komai. Amma dai zanyi masa maganar ai. Ke ma tun tuni nake miki maganar kawayen nan a samu a gaya musu, a fitar da anko kin ƙi” Ruqayyah ta tabe baki tace “ni so nake yi in na samu aka sai musu ankon sai a kai musu har gida, ai yafi a mutunce. Zan baki list din wadanda za’a siyawa sai ki fada masa number din, in aka yi musu kala biyu ai ya ishe su ko? dasu za’a yi duk events din”.
Washegari da wuri Adam ya shirya ya tafi office din Hassan, tun kafin 12 din tayi dan kar yayi late ya kara laifi akan wanda yasan already ya riga yayi, dan yasan Hassan ya samu labarin da baya so ya samu din. Yau bai jima yana jira ba, 12 din tana yi aka aiko kiransa. Ya shiga da sallama sannan ya zaune, still fuskar Hassan ba yabo ba fallasa ya mika masa hannu suka gaisa sannan yace “kamar yadda nace maka zan sa a yi min background check to anyi din kuma zance kusan komai yayi dai dai da abinda ka gaya min except your name, ance ba sunan ka Adam ba, traditional name dinka Gbenga, Christian name dinka Joseph. To bansan inda ka samu Adam din ba” Adam yace “it is my Islamic name” Hassan ya daga kafada yace “but baya reading a duk takardun ka” Adam yace “zan gyara ai, so nake in na samu shiga makaranta zan gaya sai in cigaba da using” Hassan yace “it is okay, kawai dai so nake inyi confirming cewa kai din ne ba using info din wani kai ba, duk da dai description din duk irin naka ne sai dai wancan is a Christian kai kuma musulmi. Or aren’t you?” Adam ya bata fuska, ransa ya fara baci yace “I am” Hassan yace “an samu misinformation kenan. Sai na dauka cewa ko ba dai dai naji ba sanda kace min you are a muslim, saboda wancan is a Christian daga shi har parents dinsa”. Ran Adam ya kara baci yace “to amma shi mai baka info din bai gaya maka cewa Joseph yayi converting to Islam ya chanja sunan sa zuwa Adam sannan ya bar gida two years ago ba? Maybe you should dig dipper” Hassan ya danyi murmushi kadan sannan yace “nasan wannan, just want to confirm, kuma an gaya min Joseph yana da bad temper” Adam ya mike tsaye yace “so does Adam” sannan ya juya ya fice daga office din tare da bugo kofar.
Ransa a bace yake har yaje gida, bai san neman aikin zai zamar masa terere ba da bai fara ba tuntuni. Yasan dole zai digging that part of him tun sanda ya gaya masa zaiyi bincike a kansa but bai san zai zauna yayi ta jifansa da kananan maganganu ba, tunda har ya binciko Christian name dinsa kuma ya gaya masa Adam is his Islamic name ai ba kuma sai ya bashi labarin cewa he is a convert ba. Wannan tambarin shi yasa ya bar kano, ya bar iyaye sa da siblings dinsa da friends dinsa gabaki daya saboda ya kasa belonging, to the christians suna kallonsa a matsayin wanda yayi wa addininsa ya kuma yi musu butulci dan haka har farautar rayuwarsa suke yi, to the Muslims kuma suna kallonsa a matsayin wanda yake da wani bakin penti da komai yawan sallarsa da ibadar sa ba zai iya goge shi ba. Wannan yasa ya bar kano ya dawo Kaduna, to burry his past.
Asalin iyayen Adam mutanen jahar imo ne, neman kudi ne ya kawo babansa kano, anan aka haife shi a matsayin first born sannan aka haifi brother dinsa Samuel sai kuma sisters guda biyu Gloria da Martha. Lokacin da aka haifi Adam mahaifinsa bashi da kudi sosai, sai daga baya dukiyar sa tayi ta habaka kamar an sakawa flour yeast, dan haka Adam ya tashi ne tare da sauran yaran unguwa, wadanda yawancin su hausawa ne kuma musulmai. Duk gidan da Adam yake shiga wasa gidajen musulmai ne, makarantar da yake zuwa malaman da daliban yawancin su musulmai ne, a na kuma koya musu islamic studies har shi da ba musulmi ba. Kuma wasu lokutan idan abokansa zasu je islamiyya yana binsu ya zauna a aji tare dasu yaji karatun da ake yi musu, Tun daga nan yake son musulunci.
Alokacin takaicinsa shine sunday tayi mamansa da babansa su tafi dashi church suje ayi ta waka da kida da rawa, shi a zuciyarsa sai yake ganin a dira goshi a kasa kamar yadda musulmai suke yi a sallah yafi kama da ibada akan ayi rawa ayi waka. Shi kalaman da yake ji ana karantowa a cikin Alqur’ani sunfi yi masa kama da kalaman ubangiji akan abinda pastors dinsu suke fada musu a church. Behavoirs din da yake gani a gurin musulmai tafi yi masa kama data mutanen kirki akan wadda yake gani a gurin iyayensa da sauran Christians.
Tun daga nan ya saka musulunci a ransa, har ya girma ya shiga secondary school, a nan ne ya fara fitowa da abinda yake zuciyarsa yana nunawa a fili. Kullum ya samu musulmi sai yayi tayi masa tambayoyi akan addini, in ya shiga cikin abokan da basu san shi Christian bane ba sai yayi basaja ya bisu suje masjid suyi sallah. Anan ya iya sallah complete dinta, ya iya karatun wasu daga cikin surorin Alqur’ani kuma yake karantawa a cikin sallar kamar yadda yaga anayi. And he finds peace duk sanda yayi sallar. He finds peace in the masjid.
Tun daga nan ya sani har zuciyarsa cewa musulunci shine addinin gaskiya ba Christianity ba, yasan cewa kuma one day he is going to walk in cikin wani masallaci ya samu imam din yace a musuluntar dashi. Already yasan abinda ake reciting in za’a musulunta din ma kuma ya iya. Already har ya zabi sunan Adam a matsayin sunan da zai zaba. Ya daina zuwa church. Tun daga nan trouble dinsa ya fara, tun daga nan iyayensa suka gane halin da yake ciki.
Farkon abinda suka fara yi masa shine cire shi daga school sannan suka dauke shi gabaki daya suka mayar dashi gidan pastor, akayi ta masa wa’azi irin nasu ana yi masa adduoi irin nasu aka rarrataya masa cross iri iri a jikinsa but duk abinda suke yi shiga yake yi ta kunnen hagu yana fita ta dama. The more suka yi masa magana akan Jesus Christ da Bible da Christianity the more yake kara fahimtar cewa it is wrong. Yana kara jin cewa he never belong there, haifarsa kawai akayi a can.
Bayan ya dawo gida iyayensa suka fahimci babu chanji sai suka sake daukarsa suka mayar dashi imo gurin kakanninsa suna ganin cewa zama cikin musulmi ne ya jawo musa halin da yake ciki. A can imon kakanninsa suka dora daga inda iyayen suka tsaya, suka kara da binne binne da tsaface tsaface da preaching, pampering, promises amma a banza, a lokacin ne babansa yayi masa kyautar motar da yake ja yanzu saboda yaga yadda yake son mota da kuma alkawarin in dai ya cire musulunci daga ransa zai kai shi kasar waje yayi karatu acan saboda yasan yadda yake son karatun. Anan ne Adam ya nuna musu ya sauko, ya fara binsu zuwa church ana ayyukan ibada tare dashi, ganin haka yasa iyayensa suka dauko shi suka dawo dashi kano tare da su. A lokacin mahaifinsa yayi arziki sosai da sosai
Abinda Adam ya fara yi a ranar da suka dawo shine ya shiga cikin masallacin unguwarsu ya durkusa a gaban limamin masallacin yace “ina so a musuluntar dani” and that was it.
Babansa a ranar cewa yayi sai ya yanka shi. Limamin unguwar sune ya dauke shi ya boye shi sai ga uban da police wai an sace masa da. Inda ya samu sassauci kawai shine he was 19 years then dan haka he can stand up for himself legally, dan haka ya zamanto his words against his father’s words. Ya fada cewa shi baya son komawa gidansu saboda babansa yace zai kashe shi tunda ya musulunta kuma yasan zai iya aikatawa. Wannan yasa dole aka barshi a gidan Imam din but still his father started to hunt him, har makaranta ya aika yan daba su kamo masa shi Allah ya taimaka masa ya gudu, sai liman din ya dauke shi daga unguwar ya mayar dashi hotoro gurin kaninsa. Ananne ya samu ya fara karatun addini ya kuma kammala secondary school dinsa, but anan ne ya fara fuskantar kyama daga gurin musulmai da kuma christians, hatta gidan da ake rikon nasa kyamatarsa suke yi basa barin yayansu su zama close to him. Akwai wata budurwa a gidan da mamanta ta taba zanewa saboda ta shiga dakin da yake ta kai masa abinci.