TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A gefen barandar akwai jerin alluna da gwangwanin tauwada.

Jikin yammatan sanye yake da uniform. Kansu daya, kamannin su daya, yanayin su daya dan sai ka kalla sosai, ko kuma wanda ya riga ya sansu sannan ake iya gane banbancinsu.

Dariya suke yi suma, karar dariyar su ta hade da karar kofar gidan da suka bude, wanda ko soro babu, hannayensu sarkafe dana juna suna tafiya ƙafafuwan su suna hardewa cikin na juna.

“Ruqayyah baki da kirki wallahi, hahhaha, kinga yadda kika ruda shi kuwa ya kasa gane ina ne kofar fita daga ajin?” Wadda aka kira da Ruqayyah ta rike ciki tana dariya, sannan tace “kinga ai gobe ma ya kuma dan kaniyar sa….., Ko waye ya gaya masa ni sa’ar sa ce? Harda wani “wallahi Rukee da gaske nake sonki nake yi, ni ban taba kula ko wacce mace ba sai ke” ta karashe maganar cikin kwaikwayon muryar maza.

Suka sake kwashewa da dariya, dayar tace “baki da tausayi wallahi, kika sani ko da gasken yake?” Ruqayyah tace “to ke Sumayya, wadda aka haifo da layar tausayi a wuyanta ba sai kije ki ce kina sonsa ba? Ai ba lallai ne ya gane bani bace ba. Ni wannan me zanyi dashi? Me na sama yaci ballantana ya bawa na kasa?” Sumayya ta tura baki tace “ai ba ce miki nayi ina sonsa ba, ni cika min hannu ke da ba’a fada miki gaskiya” Ruqayyah ta warce hannunta tare da hankada Sumayya gaba “in kina son Allah da annabin sa, daga yau kar ki kara gayamin gaskiya”.

A lokacin mamansu ta fito daga daki, doguwar macece kyakykyawa, baka, daga ganinta kasan anyi kyakykyawa a zamanin yarintarta. Amma a yanzu fatarta duk ta yamushe tamkar tafi shekarun ta, bakinta a bushe, hannayenta rudu rudu da jijiyoyi. Gefen rigarta a yage. Ta tsaya da labule a hannunta tana kallonsu tace “to sarakan rigima, ku dai kamar masu ganin hanjin juna ba kwa minti biyar tare sai kun yi fada. Me ya faru kuma?” Ruqayyah tazo ta wuce ta kusa da ita tana kunkuni ta shige dakin da yake kusa da inda maman nasu ta fito, Sumayya ta karaso gabanta tace “Inna Ade barka da gida. Mun dawo. Akwai abinci?”

Inna Ade tayi ajjiyar zuciya, haka suke tunda ta haife su, sunfi shiri da junansu akan kowa kuma sunfi fada da junansu akan kowa, sannan ko wanene kai baka isa kaji sirrinsu ba. Ta amsa gaisuwar Sumayya Sannan ta nuna mata kwano a gefe wanda tun daga wajensa zaka ga ya farfashe, murfinsa daban.

Sumayya ta dauka ta shiga dakin da Ruqayyah ta shiga. “Rukee ga abincin mu. Za muci yanzu ko sai munyi sallah?” Ruqayyah ta ajiye hijab din da take ninkewa a gefen yamusashshiyar katifar su, ta bude kwanon abincin sannan ta saki murfin ya fadi a kan sumuntin dakin tace “again! Yau ma shinkafa da mai da yaji? Yau ko waken babu?” Ta karashe maganar kamar zata yi kuka. Sumayya takaraso tana kallon abincin sannan ta tabe baki tace “ni yunwa nake ji, damuwata shine ba lallai abincin ya ishe mu ba”

Ruqayyah ta cigaba da cire uniform dinta tace “ki haɗa da nawa ki cinye duka, ni ba zanci wannan abincin ba, ni na gaji da cin irin wadannan abincin. Ni na gaji da talauci, ni so nake muyi kudi, na gaji da gidan nan, na gaji da kayan da muke sakawa na gaji da inda muke kwanciya. Na gaji da rayuwa” ta saka kafa tana haurin katifar tasu, sannan ta zauna dabas a gefe ta hade kai da gwuiwa.

Sumayya ta bita da kallo da sakakken baki, sannan ta zauna a gefenta ta jawo kwanon ta juya abincin ta fara ci sannan tace “kinga, kin san dai in baki ci abincin nan ba babu abinda zaki ci ko? Kinsan tabbas da daddare tuwo za’a yi kuma nasan shima cewa zaki yi ba zaki ci ba, ƙin cin fara da mai ba zai saka gasassun kaji suyi fiffike su zo gabanki ba ko?” Jin bata ce komai ba ya saka ta kara cewa “In baki ci abinci ba kuma kinsan ba zaki samu karfin zuwa makaranta kiyi exams gobe ba”

Hakan yasa Ruqayyah ta miki hannu a hankali ta saka a cikin kwanon abincin, sannan ta debi loma ta saka a baki tana taunawa kamar mai cin kashi. Babu abinda bata so irin abinda zai kawo mata cikas a cikin ssce exams din da suke yi a yanzu, dan tana ganin zuwa makaranta shine kadai hanyarta na cikar burinta, burinta na zama mai kudi.

               ********************************

A bangaren samarin, bayan sunje warehouse din da suka tafi, sun gama duk abubuwan da zasu yi sun dauko hanyar dawowa sai suka biya ta gurin da ake ginin sabon companyn da za’a bude musamman saboda sarrafa rake a mayar dashi zuwa sukari. Wannan shine Company na uku da Hussain zai bude a cikin shekaru biyar da bude companyn sa na farko.

Bayan sun gama sun shiga mota ne yace “bayan wannan kuma sai na fulawa ne zai biyo baya. Shine abinda zai kaini Beijing gobe saboda injinan da nake son siyowa na harkar noma da gyaran alkama har zuwa na sarrafa ta zuwa fulawa duk anyo su sabon design, munyi magana dasu sun turo min hotunan su na gani shine nake so in je ayi launching dinsu a gaba na, injinan suna zuwa H & H Flour Mills zai tashi. Kasan Sawun dangote nake takawa” ya karasa cikin sigar tsokana, Hassan ya dauke kansa gefe yana driving dinsa hankali a kwance, amma idanunsa sun nuna cewa tunani yake da yawa a zuciyar sa, ba tare da Hussain ya lura ba ya dauko wata magazine yana bubbudewa da sauri sauri har yazo inda yake so sannan ya nuno wa Hassan “there! Ya kaga wannan babyn?” Hassan yayi wa motar da take cikin page din magazine din kallo daya ya dauke kai gefe yace “ita ce sabuwar da za’a chanza?” Hussain ya ajiye magazine din yace “noooo, ni da akwai wadda nake jira, har yanzu basu sake ta ba, wannan Gimbiya ta nake so inyi wa kyautar ta ranar birthday dinta” Hassan yayi saurin jefa masa wani kallo yace “kyauta? Hussain me yake damunka ne? Anya kuwa ka duba kudin motar nan?” Hussain yayi dariya yace “na gani mana mr tsimilmila. Fatima fa zan bawa, wannan ba komai bane ba indai a kanta ne”

Hassan ya girgiza kansa yace “Hussain. Naga alamar yarinyar nan ta kwace min gurina tun kafin ta shigo a zuciyar ka. Ina jin in akayi auren nan in ina son ganin ka sai na sayi form a gurin ta na cike” Hussain ya sake dariya yana kara kwanciya a kan kujerar sa, ya lumshe ido sannan yace “ba a haife ta ba ba kuma za’a haife ta ba. Yarinyar da zata raba ni da kai bata zo duniya ba ba kuma zata zo ba.” Hassan yace “kana raina power ta mata Hussain. Shaidan da kansa ya ce yana tsoron kaidin mata ballantana mu da bamu san ma me duniyar take ciki ba. Mace tana iya raba tsakanin uwa da danta, ko tsakanin uba da yayansa, ballantana mu da muke brothers” Hussain yana taping hannunsa a kan cinyarsa yace “yanzu so kake in rabu da ita kenan?” Hassan yace “no, ba haka nake nufi ba, just be careful, be very careful akan mata” Hussain yayi murmushi yace “mr be careful. I am being careful ai, I have always been. Yarinyar nan fa shekarun mu uku, almost hudu tare da ita, duk wani abu nata daya kamata in sani na riga na sani, wanda ban sani ba kuma in an yi bikin mun shiga daga ciki zan sani” ya karashe maganar da dariya a muryar sa, Hassan ya bata rai yace “kasan problem dinka? Babban problem dinka a rayuwa shine komai a gurin ka abin wasa ne, komai a gurin ka is not serious, ita kuma rayiwa ba haka take ba”

Hussain ya dago kai yana kallon sa yace “ka san wani abu Hassan? Ita rayuwa nan guda daya ce, shi ran nan nan guda daya ne. In ya kare babu refilling. So ko dai kayi enjoying rayuwarka kafin ta tafi ta barka ko kuma kayi spending your entire life being careful ba tare daka mori all the goodies of the life ba, sai kawai rana daya kaga time ya kare maka a lokacin da kake tsakiya da tsara abubuwan da zaka yi nan gaba. What we have is today, what we are sure of is now, ba ayi mana alkawarin gobe ba. Zata iya kasancewa ina bude kofar motar nan zan fita mota tazo tabi ta kaina in mutu and that will be the end of me, babu abinda zai rage nawa sai memories na abinda na aikata, abinda na aikata ba wai abinda na zauna ina ta tunani ina planning cewa zan aikata sati mai zuwa ko wata mai zuwa ko kuma shekara mai xuwa ba. Bani da tabbas din zan kai wannan lokacin. Kuma ba zan iya chanza komai na daga kaddarar rayuwata ba so why worry? In na tafi bayan aiyukana da zanje in tarar a can abinda zan bari a duniya bayan memory na a zuciyoyin masoyana sai kuma sunana. And that’s what am working on. Ina so in kafa H &H irin kafuwar da zai jima kafin sunansa ya goge a garin nan, ina so kuma inyi aure, auren nan daga zuriya mai karfi irin zuriyar masarautar kano, in hada jini dasu in samu yaya yadda zan bar bayana. Wannan shine burina, wannan kawai shine burina”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button