TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Kuma wani abinda yafi damunsa a lokacin shine in mutane suna kyamar sa sai ya tuno da family dinsa, ya tuno da irin soyayyar da suke yi masa musamman iyayensa shine favorite dinsu Saboda kwazonsa a makaranta da kuma kyawun halittar sa, haka siblings dinsa, ya shaku dasu sosai and he misses them everyday. Sai yayi taji a ransa cewa yana so ya gansu, yana so ya koma gidan su. Sai dai ya kasa chanza ra’ayin sa akan addini, fata kawai yake yi cewa suma su gane gaskiya suyi joining dinsa.
Shekarar sa daya a wannan gidan ya fahimci cewa zaman ba zai yi masa haka ba, and that’s when his mother found him ashe nemansa take yi tsahon shekarar nan bata huta ba, tunda ta gane inda yake kuma bata huta ba ta cigaba da zarya tana rokonsa ya dawo gida, har siblings dinsa take kawo masa har cikin gidan da yake akan dan su ja ra’ayinsa ya dawo din amma bata saka ubansa a ciki ba saboda shi yayi fushi sosai.
Ganinsa da ake yi da mahaifiyar sa sai aka kara kyamatarsa a unguwa ana ganin kamar komawa zaiyi zuwa Christianity, wadansu ma cewa suke yi ya koma, wannan ya saka mai rikon sa ya kirawo shi ya buga masa warning cewa in uwarsa ta kara zuwa gurinsa zai kore shi daga gidansa. And that’s when he decided to leave Kano for good. Ya hada kayansa ya je har gidansu lokacin da yasan duk suna church ya sato motarsa ya saka kayan a ciki ya kama hanyar Kaduna. A hanya ne ya dauki waɗansu mutane zuwa Zaria suka biya shi kudin mota, sai kawai yayi deciding cewa he is going to be a taxi driver a haka har ya tara kudi ya kai kanshi makaranta.
But kudin sunki taruwa. Sannan yasan karatun ma kuma ba zai zo masa da sauki ba. That’s why he needed aikin gurin Hassan saboda yaji possibility na komawa school, but yanzu yana jin cewa he doesn’t need it anymore.
A ranar da Ruqayyah da Sumayya suka shirya zasu hada kai su tunkari Hassan da Maganar shirye shiryen biki, a ranar da rana sai ga kannensa mata sunzo gidan gabaki dayansu su biyar. A tare dasu akwai akwati guda biyu masu dan girma. Suka shigo da fara’ar su da kuma sallamar su, abinda Ruqayyah ta fara aiyanawa a ranta da taga akwatinan shine; “ba dai wannan ne lefen nawa ba”. Daga nan sai ta tashi ta shige daki tun kafin su shigo palon.
Inna Ade da Sumayya suka tarye su sosai suma da fara’a, suka gaggaisa Inna tana tambayar su Aunty suka ce tana lafiya lau kuma tana gaisheta. Sai suka fara neman Ruqayyah “ina amaryar tamu take? Sumayya ta waiga tace “tana jin shogowar ku ta gudu daki” Nafisa tayi dariya “ba dai kunyar mu take ji ba? In kuwa har kunyar mu take ji to kuwa na tausaya mata dan kuwa ni ana gama bikin a cikin bedroom dinta zan tare” Hassana ta harare ta tace “kar ku ce zaku takurawa takwara ta dan kungan ta shiru shiru bata da magana, gashi kuma bana nan ballantana in tare mata” Sumayya tace “wacece shiru shirun? Lallai ba ki san Ruqayyah ba alkunya takw yi muku amma in ta saba daku sai kunyi mamaki, watarana sai kunji kamar ku dauki ta ku dawo mana da abarmu” suka yi dariya Safiyya tace “abarku ku abarmu? Ai daga an daura ta zama tamu ku da ita sai tarihi” Inna Ade da take jinsu tana ta murmushi tace da Hassana “ke ce daya amaryar ko?” Hassana ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi, Inna Ade tace Allah ya sanya alkhairi kinji? Allah ya baku zaman lafiya bakiɗaya”.
Daga nan sai Inna Ade da Sumayya suka fara hidimar bakin su, suka kawo musu duk wani abin sha da abinci da yake available a gidan, su kuma bakin suka diba kadan suka ci banda Khadijah da tace ta koshi. Bayan sun gama ne Hassana tace “dama Aunty ce ta aiko mu, tace mu kawo muku wadannan kayan inji ta, akwati daga kayan amarya ne na fitar biki akwati daya kuma naku ne kuma ku saka da biki. Tata gudummawar kenan” Inna Ade ta rike baki tace “me yasa ta wahalar da kanta har haka? Da ta barshi ma Baban biyu duk zaiyi mana” Hassana tace “ita dai gashinan to ta riga shi samun ladan”. Inna da Sumayya suka yi musu godiya sosai sannan kuma Hassana ta kara da cewa “kuma tace mu tambaye ku menene tsarin ku na hidimar biki? Kuma in akwai wata al’ada da kuke yi bayan lefe ku fada kar azo ba’a yi ba tunda bamu sani ba” Inna Ade tace “aa babu wata al’ada wallahi, mu lefen ma da dan tamu ne ai zamu iya cewa Hassan ya barshi” Nafisa tace “ai kuwa lefe kan an riga an gama hada shi, jira kawai ake yi lokaci yayi azo a kawo” Inna Ade tace “maganar biki kuma ki gaya mata mu nan kamu kawai zamuyi sai yini, shikenan sai ku zo ku dauki amaryar ku” Hassana tace “ita amaryar ba zata yi komai ba?” Sumayya tace “jiya muka yi Magana da ita, ita wai kunyar angon ta ke ji ta kasa tambayarsa ko akwai abinda yake shirya musu” Hassana tayi dariya tace “lallai an gaishe ta, to ki gaya mata wallahi sai ta shafawa idonta toka ta cire kunyar nan, dan in dai yaya H1 ne na tabbatar babu abinda yake shiryawa. Gwara ita ta shirya sai ta gaya masa” Sumayya tace “to insha Allahu zan gaya mata” Hassana ta kuma cewa “Inna, kuma Aunty tace in rokar mata ku, dan Allah tana son za’a dauki amarya ranar juma’a da daddare, saboda assabar ne yinin da za’ayi a kano na amaryar yaya Hussain, to Aunty tana so a tafi harda ita Ruqayyah din mu kwana acan lahadi sai a dauko waccen amaryar a dawo” Inna tayi saurin cewa “babu komai ai insha Allah, in babansu ya dawo zan gaya masa kuma shima nasan ba zai ki ba. Sai a daura auren juma’a da safe in yaso da daddare sai a dauke ta”.
Daga nan suka cigaba da tsare tsaren bikin, maganar kawo lefe da sauran su. Nafisa ta mike, “ni ina ne dakin da yayar tawa take ne inje in ganta, dan ita nazo kuma ba zan tafi ba sai na ganta” Sumayya ta nuna mata kofar dakin da Ruqayyah take ciki sannan ta juya suka cigaba da maganganun su. Sai da suka gama sannan Sumayya ta mike ta shiga zata kirawo Nafisa. Tana shiga dakin ta gansu dare dare akan gado suna hura har da dariya, da alama tasu ta zo daya. Nafisa tana cewa “wallahi ina baki labari, shi yasa wannan karon da Aunty zata tafi dubai karaso siyayyar kayan lefen ki naki binta sai ta tafi da Zulaihat. Kinsan ita Aunty bata son tafiya ita kadai tafi son ta dauki wata a cikin mu ta yafi da ita, shi yasa muke shifting in ya tafi da wannan yanzu wata tafiyar kuma sai ta dauki wata. Kinga in akayi bikin ku kema sai ki shiga layi ake yin shifting din da ke” Ruqayyah baki har kunne, already har ta fara hango kanta a Dubai tace “eh wallahi, sai mu shiga layi dani da wannan yarinyar da Hussain zai aura, Fatima sunan ta ko wa?” Nafisa ta bata rai tace “yarinya? Gimbiya Fatima ba yarinya bace ba dan tare suka gama service da yaya Hassana. A England tayi karatun ta ma ita.” Murmushin fuskar Ruqayyah ya dauke, tace “Gimbiya Fatima? Ke ma bakin Hussain kike bi kike ce mata gimbiya?” Nafisa tace “to ai gimbiyar ce, ya ce fa a gurin maimartaba sarkin kano kuma naji ance ita ce favorite dinsa. Kinsan kuma yadda suke da kudi, shi yasa yaya H2 ya zage dantse sosai gurin hada kayan lefenta dan kar azo aji kunya. Jiya ma naga sunzo sun bude gidan sun shiga, wata kila a cikin satin nan zasu fara kaso kayan dakinta. I can’t wait to see irin kayan da zasu yi mata” idanuwan Ruqayyah suka chanja kala “you mean she is a real princess?” Nafisa tace “ta gasken gaske ma kuwa”
Twenty : Shattered Dreams 2