TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Yinin ranar nan murmushi ya kasa daukewa daga fuskar Ruqayyah, kowa in ya ganta sai yaga ta burge shi ga kyau, ga kwalliyar da ta ci ta gani ta fada, ga gyaran jiki da taje ta kashe kudi aka yi mata sannan ga farin ciki lullube da zuciyarta da kuma fuskarta. Yau ce ranar da burikanta suka fara cika, yau ce ranar data taka wani matsayi wanda zai zamo mata jagora zuwa ga matsayi na gaba a rayuwarta.

Sumayya kuma tunda aka gama daura auren taji jikinta yayi sanyi matuka, ita kawai lissafin rabuwa da yar uwarta rabin jikinta take yi, bata jin tun da aka haliccesu sun taba rabuwa ta cikakken kwana daya amma wai yau Ruqayyah zata tattara ta koma wani gidan da zama kachokan. Tsakanin su sai dai ziyara, ziyarar ma tasan Baba ba barinta zai ke yi tana yi akai akai ba kamar yadda bata ga alamar Hassan zai zamo mai barin mata tana yawo koda yaushe ba. Sai data shiga toilet tayi kukan rabuwa da yar uwarta, amma ita yar uwar tata ko a jikinta, hirarta kawai take yi a cikin kawayen aronta suna ta dauke dauken hotuna tare da shirin dinner din da za’a yi ranar Lahadi da daddare. Already dama Hassan ya kawo mata cards na mutum hamsin, wanda sai da suka yi rigima da Sumayya dan boyewa tayi ta hana yan uwansu da suka zo biki “zuwa zasuyi wallahi su tsinka ni a cikin mutane, wasu fa ko cin abinci da chokali basu iya ba, gwara mu aro mutanen da zasu je a matsayin yanuwana shikenan mun huta. Mu dan dauki kudi mu basu sannan mu basu kudin liki” amma Sumayya taki yarda, dan me bayan ga yan uwanka sannan zaka tafi kaje kayi hayar yan uwa? Ita bata ga logic a cikin maganar ba. Ta gayawa Inna Ade ita kuma ta kira Ruqayyah tace mata “bani katinan” dole ta dauko ta miko mata tana kunkuni. Inna Ade ta bata guda ashirin na kawayenta sannan sauran ta rabawa duk wanda take ganin in ya dace yaje yaci arziki ya bar arziki a mazauninsa.

Juma’a din tunda yamma aka fara shirye shiryen kai amarya, Ruqayyah ta hada kayanta kaf a guri daya, ita bata yi wani alkunya ma ba na kin hada kaya ta bar Sumayya ta hada mata a’a tare suka hada ɗin, tana tunawa Sumayya akan duk abinda ta manta. Ita bata ga wani abinda zai saka ta bata ranta ko tayi wani kuka ba a ranar da ya kamata tayi farin ciki fiye da wanda take yi a kowacce rana, a ranar data yage rigar talauci ta lulluba ta arziki?

Tun da yamma Inna Ade ta aika aka kirawo Hassana zuwa dakin Baba, suka tafi tare da Sumayya, tun kafin suje Ruqayyah ta riga tasan dalilin kiran, tasan fada ne za’a yi mata a kan zaman aure ita kuma tana ganin kamar bata lokacin su zasu yi su kuma bata bakin su, su fa irin zaman auren talakawa suka sani dan haka akan irinsa zasuyi ma ta fada, wannan kuwa aure na na masu abin hannunsu wadanda basu dawata sauran damuwa a duniya sai dai suci mai kyau su sha mai kyau su kuma kwanta a mai kyau. Ita tuntuni ta gama yiwa kanta fada akan yadda zata yi wannan zaman auren, ta riga ta kama bakin zaren Hassan ta fahimci cewa ba zata iya yi masa musu ba saboda yayi mata kwarjini dayawa amma zata iya cigaba da lullube kanta da hijabin daga riga ya santa dashi sannan tana jan zaren sa a hankali ta karkashin kasa kamar yadda tayi masa a lokacin karbar kudin hidimar biki. Let someone else take the fall, someone else, in dai har ba ita bace ba. Anyone.

Suna shiga dakin sai taji Baba ya fara tsokanar ta, abinda ta jima bata ji yayi ba, da alama shima yana alhinin rabuwa da yar tasa ne. Sai da ya saka su duk yi dariya gabaki dayan su sannan ya fara magana.

“To Hassana, alhamdulillah, gashi kamar yau Allah ya bamu ku keda yaruwarki amma gashi cikin kudirarsa yau zaki bar gidan nan zuwa gidan mijin ki. Babu abinda zamu cewa Allah sai dai godiya tunda munsan kudirarsa ce kawai ta hada ku keda Hassan sannan ta saka soyayyar ki a zuciyar Hassan din. Dan girman Allah Ruqayyah kar ki bamu kunya, ina tsananin ganin girman yaron nan wallahi kuma in da zaki bi ta ta shi na tabbatar ba karamin zaman lafiya zaku yi ba tunda yana son ki sosai. Da farko shi aure bautar ubangiji ne, ita kuma bauta ita ce abinda ake yi dan a samu shiga aljanna, ita ce kuma abinda idan an ƙi yi sai a halaka a fada wuta Allah ya kiyaye, wannan kadai ya nuna miki darajar abinda kika yi, aure. Aure sunna ne, amma abinda ake yi a cikinsa farilla ne, dole ne ki bi mijinki Ruqayyah indai kina son lahirar ki tayi kyau, dole ki sauke wannan bakar zuciyar taki da wannan saurin fushin naki kiyi masa biyayya Hassana idan ba haka ba ina tausaya miki, ina tausayawa duniyar ki da lahirar ki baki daya”

Baba ya jima yana ta yiwa Ruqayyah fada, fadan daya saka Sumayya kuka amma ba Ruqayyah ba. Bayan ya gama yayi mata adduoi na fatan zaman lafiya a gidan mijinta sannan yayi musu sallama ya fita.

Bayan ya fita ne Inna da yanuwanta da suka zo daga zamfara suka dora da nasu, suka yi mata doguwar nasiha akan zaman aure da kuma hanyoyin da za’a kyautatawa miji ta hanyar magana mai dadi, godiya, ladabi da biyayya, nuna soyayya da kulawa “ki mayar da duk abinda ya shafe shi ya zama top priority dinki, yan uwansa su zama naki, shimfidar ki ta zama abinda kullum yake muradin komawa ga, abincin ki ya zamanto shi kadai yake iya ci yaji dadi, wadannan sune manyan abinda namiji yake bukata. In dai har kin rike wadannan to kuwa ba kya bukatar boka ko Malam akan mijinki. Zaki juya kayan ki yadda kika ga dama musamman idan yana sonki” Daga nan kuma sai suka dauko nata tsarabar da suka taho mata da ita suka fara bata, dake dake ne da kulle kulle iri iri, wasu a leda wasu a robobi da kwalabe ko wanne an rubuta yadda za’a yi amfani dashi. Gwoggo Habibah tace “bamu baki su bane ba saboda bamu san kalar halittar ki ba kema kuma baki san ta mijin ki ba, dan haka sai kinje gidan kin kwana biyu kin fara gane yadda abin yake sannan zan kira ki in kara miki bayanin abinda kike bukata da kuma yadda zaki yi amfani da shi sosai. Ko wacce mace da irin halittar ta haka suma mazan, in akaje akayi ta bawa yarinya abubuwan da suka fi karfinta sai azo a zamu matsala kuma. “

Bayan sun gama nasu sannan sauran yanuwa kowa yazo ya dora da nasa, hakuri, biyayya, girmama wa, soyayya, su akayi ta maimaita wa Ruqayyah har sai data ji ta haddace kalaman tsaf a kwakwalwar ta. Abinda Ya rage mata shine yin amfani na kalmomin.

Bayan magrib akazo daukan amarya. Aunty ce da kanta tare da hajiyan Kano, kanwar baban su Hassan su suka jagoranci sauran mata zuwa dauko Ruqayyah, Ruqayyah har tayi wankan ta ta shirya cikin wata green atamfa mai adon pink wadda tayi matukar karbar ta, dinkin yayi kyau sosai a jikin ta, sai a lokacin taga Sumayya tana kuka sannan nata jikin ya fara sanyi, sannan ta fara tunanin zata yi missing Sumayya da sauran yan gidansu, sai kuma tayi saurin kawar da maganar ta hanyar gayawa kanta cewa ai zata ke yawan zuwa tana ganinsu, suma kuma haka musamman in suka je gidan nata suka ga daular da taje ciki. Kuma zata saka Hassan yazo ya roki Baba ya bar Sumayya ta koma can da zama.

Sai a lokacin taga ana fito kayan gararta, ita bata san ma cewa anyi mata garar ba kuma bata da idea a inda Baba ya samo kudin yin garar. Ta daiji Aunty tana cewa “haba malama Sa’adatu, dan me zaku takura kanku kuce lallai sai kunyi gara? Ai da kun barta kawai” Inna Ade tace “aa auntyn yara, ai babu wani takura kai wallahi, kayan dakin ma dan dai an saka lokacin ne gajere Amma da babansu duk zaiyi dai dai iyawarsa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button