TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Suna shiga idanunta suka sauka a kan gidan Hussain, ta saki baki tana kallo sai taga kuma gidan Hassan, sannan sai taga sunyi packing a kofar Hassan, ta juya tana kallon gidan Hussain sai kuma ta sake dawowa ta kalli gidan Hassan, tagan shi a bude mutane suna ta hada hada, daga ciki ta jiyo an rangada guda.
Gabanta ya fadi, ta juyo da budaddun idanuwa tana kallon Adam fuskarta da alamun tambaya. Yace “can gidan oga Hussain ne, he Calls himself “dangoten Kaduna” . Nan shine gidan Ruqayyah, gidan oga Hassan kenan. Nan zaki shiga”. Sumayya bata jira sauran wani karin bayani ba ta bude kofar mota ta fita da sauri, ko rufewa bata tsaya tayi ba, yace “hey, babu thank you balle goodnight? Kin bar jakarki a ciki” bata ko kalle shi ba ta shige gidan da sauri.
Tun a bakin kofa ta jiyo gunjin kulan Ruqayyah, gabanta ya fadi. Innalillahi, wannan wanne irin rashin ta ido Ruqayyah take nuna wa? Ba tare da tunanin komai ba ta ratsa mutanen da suke palon har zuwa gaban Ruqayyah da har yanzu take durkushe a kasa tana ta risgar kuka da iyakacin karfin ta. Nafisa tace “alhamdulillah, ga Sumayyan nan ma, zo ki yi mata magana ko zata yi shiru” Sumayya ta durkusa a gaban Ruqayyah sannan ta tallafi fuskarta a hannayenta tana jin yadda fatarta tayi zafi, ba tare data ce mata komai ba sai ta kama ta ta mikar da ita tsaye ta rungume ta a jikinta ta fara tafiya tace “ina za’a kaita?” Nan take aka yi mata jagora zuwa Bedroom din Ruqayyah da yake sama. Ta zaunar da ita a bakin gado kamar yadda ake zaunar da ko wacce amarya sannan ta goge mata hawayen fuskarta ta ja mayafi ta rufe mata fuskarta ta kuma zauna a kusa da ita ta rike hannun ta a cikin nata, a hankali Ruqayyah tace “Sumayya, Hassan ya yaudare ni” Sumayya tayi shiru bata bata amsa ba saboda mutane da suka fara shigowa, suna ta tsokanar Ruqayyah da sunan amarya mai kuka, yan uwansu da suka kawo ta suka yi mata sallama abokan wasa suna tsokanar ta, kusan kuma duk wanda yazo yi mata sallama sai ya yabi gidanta “Ruqayyah ki godewa Allah, kinga kyawun gidan ki kuwa? Masha Allah. Wannan miji naki ba karamin sonki yake ba, ki rike kayan ki hannu bibbiyu Allah kuma ya baku zaman lafiya” Sumayya ce mai amsawa da ameen.
Sai da aka ragu saura kawayensu da suke palon kasa suna ta dauke dauken hotuna dan a samu na burga sannan Sumayya ta rufe kofar dakin ta dawo kusa da Ruqayyah ta zauna tace “Ruqayyah me nene hakan kika so ki aikata? Wannan wanne irin abin kunya kika so ki jawo wa kanki ki jawo mana?” Ruqayyah ta bude fuskarta data kumbura cikin dasashshiyar murya tace “abin kunya? Abin kunya kike magana akai? Shin baki kalli gidan can ba? Kin tambayi kanki gidan waye kuwa?” Sumayya tace “ba kaina na tambaya ba, mai motar daya kawo ni na tambaya kuma ya gaya min cewa gidan Hussain ne and so what? Me yasa za ki juya ki kalli gidan Hussain bayan ga gidan Hassan kina cikin sa? Me yasa ba zaki kalli abinda yake hannun kin a matsayin mallakin ki ba sai kike juyawa kina kallon abin hannun wani? Ba ki ji abinda yanuwan mu suke fada ba? Cewa badu taba ganin gidan da yake da kyawun naki ba? Ni ma kuma haka, ban taba shiga gida mai kyan wannan ba, ban taba zama a kan gadon mai kyan wannan ba. Which of the favors of your God do you deny?”
Ruqayyah tace “amma ba kya ganin kasancewar gidan Hussain yafi na Hassan yana nufin ba Hassan ne mai Company ba?” Sumayya tace “and so what? Hassan kika aura ko kuma Company kika aura? Ni I don’t get you Ruqayyah. Na kasa gane kanki. Me kike so ne? Hassan mutum ne mai nagarta da kamala da sanin ya kamata, mai addini mai asali mai kyawun sura, mai lafiya mai aikin yi da rufin asiri, no ba rufin asiri ba, mai arziki. What more do you want” Ruqayyah ta mike kamar an mintsine ta tace cikin daga murya “but he made me believe cewa Companyn sa ne. He made a fool of me” Sumayya tayi saurin yi mata alama da tayi shiru, ta na leqa window sannan tace “yaushe? Ban sani ba ko kunyi maganar sanda bana tare daku amma ni ban taba jin ya jingina kansa da H and H ba, ni ban ma taba jin ya ambaci sunan kamfanin ba” Ruqayyah ta dafe kanta tan zama a bakin gado tare da cigaba da kuka tana jin kanta kamar zai tsage, Sumayya ta dawo ta zauna kusa da ita tace “kin taba zama kinyi tunanin ma’anar H and H?” Ruqayyah ta juyo tana kallonta amma bata ce komai ba, ita bata taba tunanin me yake nufi ba. Sumayya tace “ni ma ban sani ba, but ina tunanin Hassan da Hussain yake nufi” Ruqayyah tayi saurin cewa “meaning nasu ne su biyu right?” Sumayya tace “maybe, maybe not, but you will soon find out tunda kin auri daya daga cikin su. Am sure zai gaya miki koma na waye a cikin su. But Please Ruqayyah ki kwantar da hankalin ki, dan Allah kar ki nuna masa cewa hakan wani abu ne”
Ruqayyah ta rike hannunta tana hawaye “dan Allah Sumayya ki kwana anan. Ni goben nan tsoron zuwa Kanon nan nake ji, ban san me zan gani ba acan. Dan Allah ki zo muje tare” Sumayya ta goge mata hawayenta tace “tare zamu tafi, na taho da kayana ma jakata can a mota, tare zamu tafi ba zan tafi in barki ba. We are going to get through this together” ta samu ta lallabata ta kwanta sannan ta fita neman Adam ta karbi jakarta. Sai kuma ta sanarwa da kawayensu na kasa cewa Ruqayyah bata jin dadi ta kwanta bacci. Amma sai suka bita da tambayar “nan ne gidan Ruqayyah? Can kuma gidan waye? Ko gidan dan’uwan mijinta ne da ake bikin su tare? Waye mai Companyn ne wai a cikin su? Ruqayyah tace mana mijinta ne CEO haka ne?”
Da sauri Sumayya tayi excusing kanta tace bako ne da ita a waje ta fita, a ranta tana tunanin tabbas baki shine yake yanka wuya, Ruqayyah ta saka igiya ta daure wuyanta ta mika wa mutane bakin igiyar.
Bayan saukar Sumayya ne wayar Ruqayyah tayi kara, ta daga kai da kyar tana kallon sunan Hassan a jikin screen din “mijina” kamar yadda tayi saving. Tayi tsaki tana jin wutar data kwanta a kirjinta tana dada ruruwa. “Munafiki” ta fada a fili sannan ta kife wayar ta juya bayanta. Can kuma sai ta juyi ta daga wayar ta saka a kunnen ta “hello” ta fada da murya mai sanyi. “Hassana” ya fada da murya mai cike da conceri. “Yanzu Aunty ta kira ni tace kina ta kuka wai ko zan zo in rarrashe ki. Me ya faru? Waye ya taba min ke inzo in nuna masa matsayin sa?” Ruqayyah tayi shiru, a ranta tace “kamar gaske” yace “Please kiyi min magana mana inji dadi, in baki magana ba yanzu zan ajiye duk abinda nake yi in taho” a hankali tace “kana ina?” Yayi murmushi yace “gidan yafi karfin mu, baki sunyi yawa shine muka kama hotel mu da friends din mu. Kin gansu ma duk suna ta tsokana ta wai na kasa rufe baki saboda an kawo min amarya ta” bata ce komai ba saboda bata jin zata iya gaya masa magana mai dadi, dan haka shirun yafi. Yace “ba zaki gaya min abinda ya saka ki kuka ba? Ko sai nazo na gani da idona? Inji kuma da kunne na?”
Ta gyara kwanciyar ta tan jin cewa bata son ganinsa kwata kwata, at least not today, tace “na dauka a can zakuyi zamanku? Tunda nan din akwai mutane da zasu kwana saboda tafiyar da za’ayi kano gobe ko?” Ta shafa kansa yana runtse idonsa yace “yeah, right. Haka ne. But what about siyan baki and other traditional stuff?” Tace “it can wait ai……jibi in akayi dinner din kowa kaga zai watse ai, sai ku zo kuyi ta siyan bakin ku” yace “hakane……but ni kuma fa? Shikenan ba zanga matata ba? Ni fa yanzu ba gwauro bane ba fa” tace “ko? You will see me tomorrow ai in ka shigo da wuri kafin mu tafi” yace “ni ba wannan ganin nake nufi ba ai…..” Tayi shiru, yace “ko abinda kike wa kuka kenan dazu?” Tace “good night” yayi ajjiyar zuciya yace “to ya zanyi da raina, ba haka dai aka so ba” tace “kanin miji ya fi miji kyau ba”.