TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba’a fito da Fatima ba sai da suka je suka yi sallar laasar, dole Ruqayyah ta wanke kwalliyar ta tunda zata yi alwala amma duk da haka sai Nafisa ta dan gyara mata fuskar dai dai gwargwado kuma ta mayar mata da head dinta. Sannan suka koma suka zazzauna side daya dangin ango daya side din kuma dangin amarya, akayi ta rabon snacks da drinks daga can gefe kuma ga masu kidan kwarya nan suna yi . Sannan sai ga amarya nan an fito da ita lullube da alkyabba fara tas mai adon golden, ko tafin kafarta ba’a gani, aka zaunar da ita akan kujerar da aka tanada musamman domin ta sannan kawayenta suka zagaye ta duk sun sha ankon lace kalar zaren da akayi dinkin alkyabbar ta dashi. Kasanta kuma bayinta ne a jere duk sunyi ankon riga da zani na atamfa mai hoto da sunan ta a jiki. Hannayensu rike da shantu suna kida da cinyoyinsu sannan suna rera waka, a cikin wakar taji an ambaci sunan gimbiya Fatima, sannan ne ta fahimci wakar ma musamman saboda ita aka shirya ta.

Nan take guri ya tashi da sowa da tafi, wasu kananan yammata suka fito suma a jere hannayensu rike da mahutai wadanda side dinsu daya tambarin masarautar daya side din kuma hoton gimbiya fatima, suka jeru suna rawa gwanin ban sha’awa. Mutum biyu ne aka nema daga dangin ango suka je suka bude fuskar gimbiya sannan suka feshe ta da turare, duk da haka sai ya zamanto rabin fuskar ne kawai a bude idanuwan ta da goshinta still suna rufe, amma duk da haka zaka iya hango tsantsar kyawunta ta bakinta da yake dauke da murmushi da kuma dogon hancinta da yake tsaye chas. Ruqayyah tayi tsaki a ranta. “Ashe ma na fita hasken fata” ta fada a hankali tana hararar iska. Sai dai ita kanta tasan koda tafi Fatima haske to kuwa kulawar da fatar fatiman ta samu ba zai bar hasken Ruqayyah ya haska ba.

Daga nan sai taga an fara shigowa da kaya ana jere wa a tsakiyar gurin wai kayan gara ne, amma abin mamakin shine ba wai kayan abinci bane ba kamar yadda tasan ana yin gara aa wannan kayan suttura ne kawai, akwati akwati, jaka jaka. A al’adar gidan sarauta duk wadda aka yiwa aure a gidan sarauta idan wani gidan sarautar aka kaita to kuwa hatta bayin gidan sai an yi musu suttura kuma an basu kudi albarkacin ta, idan kuma ba gidan sarauta bane ba to kuwa za’a binciko duk dangin angon na nesa dana kusa sai kowa ya samu rabonsa albarkacin gimbiya, yan uwansa shakikai kuwa da iyayensa da gwoggonninsa nasu na musamman ne, sai an yi musu kamar wani karamin lefe. Haka akayi ta kiran sunan tun daga iyayen Hussain dangin uwa da dangin uba har zuwa kan dangin dangarere, wasu ma basa gurin, wasu ma ko kadunan basu je ba ballantana kano amma an kira sunan su kuma an basu rabon su, kowa aka bashi kaya kuma sai an hada da kudi, maza da mata.

A cikin rabon sai taga na Hassan, sunanshi na biyu daga Aunty sai shi, akwatin sa guda mai cike da dangin shaddoji masu tsada, da yar karamar jaka ita kuma takalma ne a ciki da huluna da turaruka na maza. Tunda babu maza a ciki dan haka ita aka ce taje ta karbo masa, ta taka kaje har gaban gimbiya, ita bakin cikinta kenan wai sai anje gaban gimbiya, ta tsaya a gefen gimbiya akayi musu hoto sai mai hoton ya yi mata magana da cewasai ta sunkuya saboda ita gimbiyar a zaune take, ita kuma Ruqayyah a ganin ta in da sunkuya kamar gimbiyar ta sunkuyawa amma ganin mutane suna kallo dole ta sunkuya din tana kirkirar murmushin karya aka sake daukan wani. A lokacin da zata bar gurin ne taji gimbiyar ta riko hannunta tayi mata alamar data sunkuyo, bakin ciki ya toshewa Ruqayyah makogwaro, amma dole ta sunkuya sannan ne suka hada ido, da murmushi a fuskar gimbiya fatima, ga wani fitinannen kamshi yana tashi daga jikinta tace “ban san dake aka zo ba ai, da tun dazu na aika an kawo min ke gurina, ke bakuwa tace ai bata mutan gida ba” Ruqayyah tayi yake “yeah right” sannan ta zare hannun ta ta bar gurin, ko ta kan kayan bata bi ba. Ita sunkuyawar da tayi wa gimbiya shi yafi komai kona mata rai. Tana dawowa ta fara sansana kanta dan taji ko tana irin kamshin da gimbiya fatima take yi?

Abin takaici sai gashi tana zama an sake kiran sunanta again, wannan karon kuma nata kayan taje aka bata, exactly zubin da akayi wa Hassan irin sa akayi mata kawai dai nasa na maza nata na mata. Wannan karon da akace taje suyi hoto cewa tayi ai tayi, tayi tafiyar ta.

Sai da aka kwashe kayan gara sannan su kuma dangin ango suka shigo da lefe, tun Ruqayyah tana lissafa akwatunan har taji kanta ya fara ciwo ta kwanta a jikin kujera ta rufe idonta, bata son ma ganin kayan ciki tunda ance kazantar da baka gani ba tsafta ce. Sumayya ta kama hannayenta, ta juyo ta kalle ta sai tayi mata murmushin kwarin guiwa, sai taji har Sumayyan ma haushi take bata. Gabaki daya mutanen gurin haushi suke bata, ranta zafi yake yi, zuciyarta ciwo take yi. Ta mike da sauri tana daukan jakarta. Aunty ta riko hannun ta “ina zakije Ruqayyah?” Ruqayyah ta langwabe kai “Aunty kaina yake ciwo wallahi, zuwa zanyi in dan kwanta kafin a gama” Aunty tayi murmushi “Akwai ciwon kai kam, nima kaina ciwon yakeyi, amma zaki iya gane hanya kuwa” Ruqayyah tayi shiru, ita wadannan sorayen da suka wuce ina zata iya gane su? Aunty ta waiga ta kira wata a cikin wadanda ta lura bayin gidan ne tace “dan Allah raka su inda aka sauke mu”.

Suna zuwa can Ruqayyah ko ta kan Sumayya bata bi ba tayi kwanciyar ta, taji karar wayarta ta dauko ta taga ten missed calls daga Hassan, hayaniya ce ta hana ta ji. Tayi tsaki ta mayar da wayar cikin jakarta sayi kwanciyar ta.

Sumayya ta bita da kallo sannan ta tabe baki tace “kin dorawa kanki aiki. Babban aiki ma kuwa” a kara gyara fuskarta Sannan ta juya ta koma gurin taron. Ita ba zata iya zama tayi tagumi ba bayan ga shagali can ana yi.

Wannan littafin na siyarwa ne, idan kina so kiyi min magana ta WhatsApp ta wannan number 08067081020Sai magrib aka tashi daga taron, daga nan duk aka dawo masauki aka yi Sallah masu son yin wanka suka yi sannan aka fara shirin tafiya dinner, sai a lokacin Ruqayyah ta tashi tayi sallah sannan itama ta shiga tayi wanka, suka zo suka fara shiryawa, kayan ta data zubo a jakar Sumayya ta dauko, daya daga cikin kayan da aunty ta siya mata ne na fitar biki, tayi kwalliyar ta tsaf ta shirya duk da cewa bata cika make up da yawa ba amma tayi kyau sosai. Sumayya ma tayi wanka ta chanja kaya, suka yi sallar isha i sannan suka fita suka tafi inda sauran mutane suke, ana ta yin make up da daurin dankwali, Aunty ta tambayi Ruqayyah ko tanaso ayi mata amma tace a’a, sai daurin dankwalin ta kawai aka gyara mata. Zuwa karfe takwas aka ce su fito za’a tafi. Sai a lokacin ta dauko wayarta ta kira Hassan, har ya gaji da kira ya hakura. Ring daya ya dauka. “Har na dauka ko an sace min amaryata” ta danyi dariya, “sace wa kuma sai kace kai” yace “ohh abin harda tsokana? To zan rama ne nima zan zo in sace ki kinga munyi one one” tace “ai ni bani na sace ka ba” yace “yeah, ke kika dawo dani gida, and I am never going to forget that” tace “me too”. Yace “nayi ta kiranki ne dazu dan in gaya miki mun karaso muma, an kaimu masauki tare dasu Hussain and I was lonely nace bari in kira matata tayi min hira” tace “muna gurin taron can, and the place was so noisy shi yasa banji ka ba, sai yanzu dana dauko wayar sannan na gani. Sorry” yace “it is okay dear. Gamu nan muna shirya wa yanzu zamu tafi dinner” tace “muma haka” yace “okay, I will see you there angel”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button