TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Tayi murmushi tana kashe wayar. Sai yanzu taji dadin zuwansa garin, ita sam bata son zuwa gurin dinner din nan dan bata ga abinda zata je ta gani a can ba. Sai yanzu kuma take kara gode wa Allah da Sumayya tayi dabarar sallamar kawayenta da sun biyo ta kano ai da ansha abin kunya. A cikin palace din za’a yi dinner amma sai da aka dauke su a motoci aka kaisu gurin saboda girman palace din, kamar wata duniya suka je.
Suna shiga suka tarar da gurin already da mutane, taji ana zancen harda governor da matarsa ne zasu je gurin. Yanayin tsarin gurin kadai ya isa yasa mutum kamar Ruqayyah ciwon kai. Sumayya sai kalle kalle take tana daukan hotunan yadda akayi arranging tables din gurin da kuma kujerun amarya da ango, ta dauki hoton high table, wannan lallai sai ta nuna wa Inna Ade dasu Sulaiman, wannan lallai sai ta nuna wa Adam.
Ruqayyah ta ja Sumayya zuwa can extreme end din hall din suka zauna, Sumayya tace “nan ai ba gani zamu ke yi ba, Please ki tashi mu koma gaba” Ruqayyah tace “ke da kika zo gani kenan, ni kuma zuwa nayi a ganni and I really don’t want to be looked at, dan haka nan zanyi zamana. Ke ma kuma sai ki zaba, gurina kika zo ko gurin bikin gimbiya? The choice is yours” Sumayya tayi ajjiyar zuciya ta zauna tana ta daga kai, sai daga baya ta lura a gefen su ma akwai katon screen da kake iya hango can gaba kamar a gabanka akeyi, just like kana kallon TV. Shikenan Sumayya ta gyara zaman ta da niyyar shan kallo tana yi tana recording as much as she can. Basu jima da zama ba guri ya cika, sai ga Hassan yana kiran Ruqayyah, “kuna ina ne? Ga guri an tanadar mana” ta yamutsa fuska “mun samu guri mun zauna ma, kuyi zamanku kawai” yace “noo, ni ba zan iya zama ni kadai babu ke ba, common ki na ina inzo in taho dake inda nake” ta kwantar da murya “ni ba zan iya zama a can ba, dan Allah ka bar ni inyi zamana anan” yayi ajjiyar zuciya, he thought as much, yaso a rabu da yarinyar nan tayi zamanta a gida aunty tace lallai sai an taho da ita, ita bata saba da irin wadannan abubuwan ba dan haka dole zata jita a takure. Yace “kina ina? Ni sai inzo inda kike” ta gaya masa. Mintuna kadan sai gashi nan yazo, yaci kwalliya kamar babu gobe dan ita kanta tasan yayi kyau. Tayi masa murmushi shima ya mayar mata yana jan kujerar kusa da ita ya zauna. Sumayya ta gaishe shi yace “su Sumayya an samu abinda ake so ko? Biki dai ayi ta hidima dai” tayi dariya tace “eh mana, biki ai lokaci daya ake yinsa daga an gama shikenan” yace “Allah ya kaimu baki bikin to, mu sha shagali har mu gode Allah” ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Yace da Ruqayyah “muna shigowa ai Hussain ya kira ni wai gimbiyar sa tana ta nemanki, tana so wai ko zaki shiga cikin friends dinta and I said no, baki san su ba ba zaki ita zama a cikin su ba” Ruqayyah bata ce komai ba sai kira ya shigo wayarsa ya dauka yayi magana sannan ya mike “excuse me ladies, zan je zamu shigo da Hussain. Reserve my seat please dan anan zan zauna”
Bayan fitarsa da kadan sai akayi sanarwar amarya da ango zasu shigo, kowa ya mike tsaye kamar wani president ne zai shigo, suka shigo suna taku dai dai abokan ango da kawayen amarya suna take musu baya, camera tana daukan su ta kowanne angle ana turo hotunan a manyan screens din da suke a gurin saboda wadanda ba zasu iya gano wa ba. Mai video yana dauka tun daga kan takalman gimbiya har zuwa kan sarka da dan kunnen ta, haka shima Hussain aka dauko shi, ba kuma wai shigarsu ko kuma kyawun surar sune abin burgewa ba, a’a, soyayyar junan su da take kwance akan fuskokin su. Kowa ya gansu ya san a cikin farin ciki suke. Ruqayyah ta kifa kanta a jikin table din gabanta tana rufe idonta kamar mai bacci, wannan abin shine abinda tayi ta mafarki zata samu a bikinta tun lokacin data hadu da Hassan. Mutane irin wadannan, governor, ita da mijinta su shigo kowa yana kallon su cike da sha’awa, amma ita nata mijin ma cewa yayi ba zai je kowanne event dinta ba, in dai bai je ba kuwa mutanen sa ba zasu je ba, shi yasa bata yi komai ba saboda baya ga amfanin yin ba tunda so take yayi introducing dinta ga mutanensa a matsayin matarsa ita kuma tayi a matsayin mijinta kuma ceo of h and h group of companies. Now she is just a guess a bikin ceo na H and H group of companies. Jama’ar amarya da ango suna wucewa ta mike ba tare da tace komai ba ta bar cikin hall din ta fita waje, a can gefe taga wata doguwar veranda da kujeru a ciki sai ta tafi can ta ja kujera daya ta zauna sannan ta zubawa bishiyoyin gurin ido tana kallon su tana lissafo rayuwar da take gabanta.
Bakin ciki dai kam tasan zata sha shi har sai ta godewa Allah. Abu daya ne zai saka ba zata fasa auren Hassan ba shine saboda tasan in ta rabu dashi ko a mafarki ba zata samu mijin da ya kai ko da rabin sa bane ba, ceo or not ceo tasan cewa Hassan ba sa’an aurenta bane ba kaddara ce kawai ta hada ta da shi har kuma ta kulla aure a tsakanin su, ta kuma san cewa yana son ta da gasken gaske, dan haka zata yi amfani son da yake yi mata gurin samun cikar burinta. Burinta na auren ceo, bata san yadda hakan zai faru ba bata san ta inda zata fara ba amma tasan abinda take so kenan, abinda ta hango wa kanta kenan. Wannan gidan, wannan valcony din na can sama shi take so. Title din matar ceo na H and H shi take so.
Su Hassan suna kai su Hussain gurin zamansu sai ya juyo ya dawo inda ya bar Ruqayyah, amma sai ya tarar bata nan sai Sumayya da bata ma san Ruqayyah ta tashi ba, ya zauna ya kira yawarta ta dauka ta gaya masa inda take, so take ya taso ya bar gurin bikin ya taho gurinta. Ai kuwa ko minti goma ba’a yi ba sai gashi a gabanta yana mata murmushi. “Shine kika gudu ko?” Tace “kida yayi kara da yawa, kaina kuma ciwo yake yi min” ya zauna a kusa da ita yana murmushi yace “wannan ciwon kai, ki gaya min yaya zanyi dashi ne” ta dafa kan tace “gajiya ce kawai, da ace ba’a taho dani ba kaga da yanzu ina can ina hutawa ta” ya gyada kai yana dada jin rashin dacewar tahowa da ita da Aunty ta dage sai anyi, sannan yace “kawo kan inyi miki addu’a” ta makale kafada yayi dariya “adduar ce ba kya so? Kin san dai adduar miji ga matarsa tana da saurin karbuwa inayi miki zaki ga kin warke” ita dai taki yadda, ta san wayon ya tabata ne babu wata addu’a da zai yi mata, wai ita zaiyi wa wayo bayan itama tana da wayon ta. Shi kuma yayi ta mata dariya, yasan abinda take gudu kuma abin yana kara masa sonta a zuciyarsa, yana kara nuna masa cewa she is pure, baya jin ta taba rike hannu da wani balagaggen namiji, dan haka tashi ce shi kadai babu wanda ya gutsira ya rage masa.
Ya saka hannu a aljihu ya zaro kudi, sababbin 200 notes bandir biyu ya ajiye a tsakiyar su, sannan yayi folding hannunsa yana kallonta yace “ga kudi nan, ban sani ba ko kina so ki shiga cikin gurin biki kiyi liƙi” ta kalli kudin sannan ya kalle shi, tana lura da yadda idanuwansa suke studying dinta tace “liƙi kuma? Dole ne sai anyi likin?” Ya girgiza kansa yace “ba dole bane ba, ra’ayi ne, ban sani ba ko kina da ra’ayin yi?” Ta dan yi murmushi tace “kai me yasa ba zaka je kayi musu likin ba” yace “ni bana yi” tace “saboda me?” Yace “saboda banga abinda hakan zai amfane ni dashi ba, a duniya da kuma a lahira. Banga amfanin in dauki kudin da zan iya yin wani abu dasu mai muhimmanci a duniya, ko kuma inyi sadakar su in samu ladan a lahira, sannan in ringa watsi dasu mutane suna rawa akai ba. I don’t see the logic in that” ta harde hannayenta itama irin yadda yayi tace “kuma ni shine kake bani inje inyi?” Yayi murmushi bai ce komai ba, ta dauki kudin ta jujjuya su a hannun ta mentally tana calculating adadinsu, ba laifi, shima fa yana da kudin, ta mayar dasu ta ajiye tace “har na lissafo irin amfanin da za’a yi da wadannan kudin, ba zan zubar dasu a kasa ba” ya jima yana kallon ta, fuskarsa da sassanyan murmushi sannan yace “take it” tace “bazan yi likin ba fa” yace “na sani, ki saka su a jakarki ko zaku fita shopping dasu Nafisa, nasan babu abinda suke kauna irin shopping, maybe zaki ga abinda kike bukata kema” ta girgiza kai sai ya saka hannu ya dauki jakarta ya bude ya zuba mata kudin a ciki sannan ya rufe ya mika mata. Ta karba a hankali tace “Nagode” zuciyarta fal farin ciki, tabbas ta samo bakin zaren sa.