TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Hirar su suka kama yi, mostly labarin drama din da ake yi a gurin abokan su yake bata, yadda aka sako su a gaba ana ta tsokanar su shida Hussain akan aure, har zaunar dasu masu auren ciki sukayi wai suna koya musu yadda zasu yi wa matan su. Tun Ruqayyah tana dan basarwa har ta fara murmushi, daga baya sai gata tana kyalkyala dariya duk wani ciwon kanta ta bacin ranta ya tafi. Anan suka yi tasu dinner din, yayi waya aka aiko musu da abinci nan aka jera musu suka ci suka sha, yaji dadin zamansu a gurin sosai duk da yasan Hussain yana can ya kumbura in ya lura baya cikin gurin.

Suna komawa masaukin su Aunty ta kama hannun Ruqayyah “Ruqayyah ina kika je? Ina ta nemanki ni da nake so in ganki a kusa dani?” Ruqayyah ta danyi murmushi tace “uhmm dama……..” Sumayya tace “tare da yaya Hassan suka fita, nima bansan inda suka je ba” Aunty ta saki hannun Ruqayyah tana cewa ” wannan yaro, zai zo ya same ni ne, wato shine shi bai zauna ba ita ma kuma ya hana ta zama? Menene amfanin tahowa da ita da nayi kenan?” Tayi ta fadan ta ita kadai su dai su Ruqayyah suka fara shirin kwanciya bacci.

Karfe goma na safe aka daura auren auren Hussain Aminu Abdullahi da Gimbiya Fatima. Daurin auren daya samu halarta manya manyan kusoshin kasarnan dan Hussain duk wanda yake fada aji sai daya gayyace shi daurin aurensa, kuma yawancin su sunzo wadanda basu samu zuwa ba kuma sun turo representatives dinsu. An dauta auren ne a masallacin juma’a na kofar kudu, duk girman masallacin sai da mutane suka cika shi taf wadansu ma a haraba suka tsatstsaya, daga nan aka tafi reception, cikin gida kuma aka fara shirye shiryen daukan amarya zuwa kaduna inda acan kuma za’a daura auren Hassana da karfe biyu na rana. Dan haka ba tare da bata lokaci ba duk aka gama shiri, sannan aka dunguma gabaki daya har gaban mai martaba sarkin Kano, yau sai ga Sumayya da Ruqayyah a gaban sarki. Inda yayi wa Fatima doguwar nasiha akan aure, sannan kuma ya danka amanar ta a hannun yan uwan mijinta ya kuma yi musu addu’ar samun zaman lafiya da kuma zuriya mai albarka, daga nan sai aka bi aka rarrabawa duk matan da suke gurin littafin da maimartaba da kansa ya rubutawa Fatima na nasihohi akan zaman aure wanda yayi wa tittle da “Nasiha gareki yata Fatima” saboda ta ringa karantawa a duk lokacin da taji ta shiga duhu a game da zaman aurenta. Aka bawa duk matan gurin suma su ringa karantawa albarkacin Fatima.

Sai da aka daga Fatima za’a fita da ita sai ta saka kuka ta ruga gurin mahaifinta ta rungume shi, aka je da niyyar a dauko ta amma sai ya dakatar da mutanen ya mike da kansa ya kamata ya fita da ita ya saka ta a motar da zata kaita airport sannan ya shiga shima tare da kishiyar mamanta suka raka ta har gaban jirgi. Anan kowa ya kuma tabbatar da son da mai martaba sarki yake yiwa yarsa Fatima.

Ana sauka a Kaduna a ka cigaba da hidima, ana ƙoƙarin shiga da Fatima gidan ta kuma ana shirye shiryen daurin auren Hassana. Ruqayyah duk jinta take out of place, duk kuwa da cewa duk juyi sai Aunty ta kira sunan ta, sai ta lallaba ta ja Sumayya suka koma part dinta, Hassan ma ko duriyarsa bata ji ba bata sani ba mako ya dawo daga Kanon ko yana can, ta shiga daki kawai ta cire kwalliyar ta tayi wanka tayi kwanciyar ta, sama sama take jin guda da hayaniya daga gidan Hussain, ta san yanuwan amarya ne suke ta bidirin su a ciki, ta tashi ta jawo window ta rufe ta rufe curtain sannan ta kwanta, sai dai zafi take ji gashi dakin babu fanka ita kuma bata iya kunna ac ba, a haka tayi kwanciyar ta tana hada gumi.

Cikin ikon Allah sai ga yan gidan su nan sun zo, har da su Sulaiman da Zunnur da yan uwan inna Ade dana Baba, duk wadanda Inna ta bawa card din dinner sannan kuma ta turo su suje suyi wa Aunty Allah ya sanya alkhairi na daurin auren Hussain da Hassana. Yan uwan Hassan din da basu shigo ganin dakin amarya ba ranar da aka kawo ta suma duk suka shigo, wasu daga cikin yan uwan gimbiya suma suka leko, sai ya zamanto kamar wani bikin ake sakewa amma babu amarya, amaryar tana can ta kulle kanta a daki tana baccin wahala. Sai laasar ta tashi, shima gwoggo Habibah ce ta aiko Sumayya akan lallai ta tashe ta tayi wanka ta shirya ta fito. Dole ta tashi ta shirya din sannan ta nemi doguwar riga a cikin kayan lefenta ta saka tunda dinkunan nata sun kare sai wanda ta ware saboda dinner din yau. Ta kalli kanta a mudubi taga cewa tayi kyau sai dai idanunta da suka fada ciki suka yi baki. Ta danyi tsaki tana kara shafa hoda akan idon sannan ta fita.

Yadda taga gidan ya bata mamaki, ga abinciccika nan an kawo kala kala kowa yana serving kansa, ga kuma yan aiki nan an ajiye yadda daga an bata guri zasu gyara dan haka duk da yawan mutanen gidan fes fes yake yana kamshi. Ta gaggaishe da wadanda ya kamata ta gaisar su kuma wadanda ya kamata su gaishe ta suka gaishe ta.

Ana cikin haka sai ga jama’a nan suna ta shigowa, wai an kawo gimbiya gurinta za’a bata amanar ta a matsayin ta na yayar miji. A ranta tace “iyayi iya reto, wai matar da ta kusan haifa ta ita za’a bani amanar ta” aka zaunar da gimbiya a kasa, itama Ruqayyah aka zaunar da ita a kusa da gimbiyar sannan Aunty da sauran manyan iyaye suka zauna akan kujeru. Akayi ta jero musu nasiha akan su rike junansu amana. Aunty tace “to Ruqayyah da Fatima, ga amanar Hassan da Hussaini na na baku. Na san cewa kun sani marayu ne basu da uwa basu da uba dan haka basu da wanda yafi junan su kusanci da kansu. Dan Allah ku zamo sanadiyyar sake karfafa musu zumuncin su kar ku zamo sanadiyyar rushewar sa. Na san cewa Hassan da Hussain basa minti talatin a zaune tare ba tare da sunyi rigima ba amma hakan baya nufin cewa basa kaunar junan su dan ni ban taba ganin yan uwan da suke kaunar junan su ba kamar su. Dan Allah ku zamanto sanadiyyar karfafa wannan kauna a tsakanin su kar ku zama sanadiyyar haddasa gaba kiyayyar junan su a zukatan su”. Daga nan sauran iyaye kowa ya kara da tasa. Duk sai da jikin kowa yayi sanyi a gurin harda Ruqayyah

Da zasu fita Aunty tace da Ruqayyah “in anyi magrib mai kwalliya zata zo tayi miki, sai ki fito da duk kayan da zaki bukata ki ajiye su a kusa sannan ki yi Sallah da wuri kar ta zo tana jira tunda ita zata yiwa Hassana ma. Fatima ta taho da nata” Ruqayyah ta gyada kai amma sai taji zuciyarta ta tabu, dan me aunty zata ce mata Fatima ta taho da nata? Ko tana tuna mata ne cewa ita bata taho da tata ba?

Bata yi wanka ba tunda tayi dazu, dakunan kasa aka budewa yan uwanta suka yi ta shirin su a ciki, bata tuna da kawayenta ba sai data ji hayaniyar su sun shigo sannan suka hau sama gurinta. Suna ta hayaniyar su kuma mostly zancen basu akan waye mai gidan kusa dana Ruqayyah ne, ita Ruqayyah sai taji suna kara mata pressure ne , tayi nadamar ina ma bata yi hayar su ba? Kadan daga cikin su ta sani suma kuma Minal ce kawai wadda ta sani sosai, duk sauran hada ta akayi dasu. Anan suka shirya, tare da hargitsa wa Ruqayyah kayan kwalliyar ta, wasu suka debi rabon su a ciki. A karshe ma sai da Sumayya ta faki idonsu ta kwashe kayan ta saka a closet ta rufe sannan aka samu lafiya. Shima suka yi ta mata mita. Ruqayyah kuwa sai shiga toilet tayi ta rufe kanta saboda hayaniyar su tayi mata yawa. Sai da aka ce ga mai makeup din tazo sannan ta wanke jikinta tayi alwala ta fito. Sai data yi sallah sannan ta zauna suka fara kwalliyar, yarinyar ta kware sosai a aikinta dan haka nan da nan ta mayar da Ruqayyah zuwa irin matan da take ganin hotunan su a Instagram. Ta taimak mata ta sak kayanta, making some adjustments here and there, yadda rigar ta zauna sosai, sannan ta saka mata duk accessories din da suka dace, wanda taga baiyi ba kuma tace a chanja wani, har ta gama shirya ta tsaf yadda Ruqayyah tasan ko a Instagram din ne ma sai an duba kafin a samu amaryar da tayi kyawun ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button