TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Sumayya ta fito da ita palon sama ta zaunar da ita sannan itama ta tafi ta fara nata shiryawar. Itama irin ankon kawayen Ruqayyah ne ta saka sai dai nata dark pink nasu light pink. Ita kuma amarya peach. Sai a lokacin Ruqayyah ta kira Hassan. “Ka manta dani” ta fada da muryar shagwaba, yace “kin taba ganin inda mutum ya mance da rabin jikinsa a wani waje? Tace “gashi kuwa, tun safe fa baka ko bi ta kaina ba” yace “sake dubawa dai, ki lissfa missed calls nawa na ajiye miki a wayar ki” tace “ni ban gani ba” yace “kun shirya? Cos Gamu nan fitowa yanzu” tace “mun gama ai, ku kadai muke jira”
Abun ya matukar kayatar yadda angwaye Hassan da Hussain suka shigo su kadai a mota daya, Hussain da kansa ne yake driving Hassan yana gaba, suka fara zuwa kofar gidan Hassan Ruqayyah ta fito a bisa rakiyar kawayenta ta shiga sannan suka karasa kofar gidan Hussain Fatima ta fito itama ta shiga ita kadai, suka rufe mota suka ja suka yi tafiyar su. Sai bayan sun fita sannan aka fara rububin shiga motoci ana bin su a baya. Suna zuwa gurin taron suka yi packing a bakin kofar shiga gurin sannan suka yi zaman su a mota.
Tun da Fatima ta shigo take ta yabon kyawun da Ruqayyah tayi, wannan yasa Ruqayyah ta kara kumbura tana ta faman fasa kai duk kuwa da cewa tun da Fatima ta shigo motar taji ta raina kanta, hatta kamshin da take yi na daban ne yanayin kwalliyar ta ma haka. Fatima irin cikakkun matan nan ne masu cikar kirji da hips, wannan yasa kayan jikinta suka yi mata matukar kyau suka fitar da kyakykyawan fasalinta duk da cewa ba kama mata jiki suka yi ba, ga kuma dogon trail din da aka dinka a jikin rigar kamar yanayin dinkin alkyabba daya taso tun daga kafadar ta ya rufe mata kurjinta sannan ya sauka har kasa yana jan kasa yana binta a baya, sai ya zamanto kamar yayi serving a matsayin mayafi kenan. Angwayen kuma anko suka yi, komai nasu iri daya ne hatta agogon hannayensu, sai a lokacin Ruqayyah ta kara tabbatar da kamannin su. Hira suke tayi, Hussain yana ta tsokanar kowa har Fatima bai bari ba ita ma kuma sai ta rama, yace wai kowa a cikin su ya kure adaka dan ace sunyi kyau shi kuma yasan duk ya fi su kyau, har da posing yake yi wai matso kyan sa yake yi, wai sai lallai sunce duk yafi su yin kyau. Ita Ruqayyah yadda taga Fatima tana magana da dariya sai abin ya bata mamaki, sai taga kamar ba wannan gimbiyar da bayi suke kwanciya a gabanta bace ba. Ita ta dauka ai da kyar take magana saboda mulki. Sunyi ta hotunan su a cikin motar, itama Ruqayyah ta dan ware tayi magana da taji Hussain ya saka ta a gaba wai in bata magana zata haifi kurma. Suna ganin mutane suna ta shiga hall din, sai da aka tabbatar kowa ya gama shiga sannan aka zo kiran su, a lokacin itama Hassana da angonta Saeed sun karaso. Sannan sai suka jera suka shiga. Kawayen sune suka fara shiga a layi, kawayen Ruqayyah a farko, sai na Fatima sannan na Hassana, kowanne sunyi anko. Daga sai masu gayya masu aiki, Hassan rike da hannun Ruqayyah a gaba, Hussain da Fatima a tsakiya, Hassana da Saeed a baya. Sai kuma abokan angwaye suka take musu baya. Abin gwanin burgewa.
Komai ya tafi bisa tsari, anci an sha an bar abinci, anyi programs masu kayatarwa yawancin su na barkwanci, sannan Aunty ta gabatar da jawabin godiya ga duk wanda ya samu halartar bikin. Daga nan kuma sai akayi ta daukan group pictures. Anyi kida nayi rawa, amma sai amaren duk kamar sun hada baki suka ƙi yin rawar. Angwaye kan sun cashe abinsu, abin mamaki sai ga Hassan ya biye wa Hussain suna ta rawa, ai kuwa nan take guri ya dauki ihu da tafi aka fito akayi ta musu ruwan kudi, kudi dai kam kamar ba’a talauci a Nigeria. Daga nan sai suka yanka cake akayi addu’a aka tashi.
Daga gurin taro aka wuce da Hassana gidan mijinta, wannan yasa duk yan gidan basu dawo gida ba can suka wuce, amaren ne kawai da kawayensu suka dawo. Kamar yadda aka dauke su haka aka dawo dasu, aka fara sauke Ruqayyah sannan aka karasa da Fatima.
A gajiye Ruqayyah ta shiga gida. Gidan ba kowa tunda su suka fara fita amma tas tas dashi yan aikin da aka kawo mata sun gyara mata shi kamar ba’a yi taro ba. Ta wuce sama ta cire tarkacen kayan jikinta dama duk sun bi sun ishe ta sannan ta kwanta akan gado yana mayar da ajjiyar zuciya. Ta lumshe idonta tana tunanin event din, gaskiya ya kayatar da ita, tayi ta kokarin ta gano fault a ciki amma ta kasa, sai dai kawai tasan kawayen Fatima sunfi nata haduwa, ta kuma san mutanen gurin sunfi bada karfin su ga Hussain da Fatima akan ita da Hassan.
Tana nan kwance ta jiyo hayaniyar kawayenta suna shigowa. Kamar yadda suka sabarwa kansu direct bedroom dinta suka zarce suna ta hayaniya. “Ni ban gane ba Ruqayyah, naji a gurin kamar ana cewa kanin mijinki ne mai kamfanin ba mijin ki ba, menene gaskiya wai?” Wata tace “ni kuma ji nayi ance nasu ne su biyu wai Hassan and Hussain shine h and h din” Sumayya data fara rage kayan jikinta itama tace “to ku menene naku a ciki? Me zaku karu dashi in kun san waye?” Minal da take kwance rashe rashe akan gado tace “dan musan yadda zamu yi pricing kudin siyan baki mana? Ai iya kudin ka iya shagalin ka ne abin” ita dai Ruqayyah baya ce musu komai ba, sai kuma suka koma hirar wai waye yafi haduwa a tsakanin angwayen, kowa tana fadar gwaninta tana kuma fadar dalilin ta. Can suka ji tsayuwar mota sai suka garzaya taga suna leken motocin da suka tsaya a gaban gidan Hussain. Wata tace “wai Allah! Wannan gida! Gaskiya Ruqayyah da sake, in dai har kamfanin nan nasu ne su biyu to ki tubure ki ce sai dai ku zauna tare a can gidan, ai zai ishe ku” wata kuma tace “ni ta mijin nake bata gidan ba, gayen ya hadu karshen haduwa gashi ya iya daukan wanka”
Ruqayyah ta mike ta shiga toilet ta rufe kanta kamar dazu, bata so su kara mata bakin ciki, ta samu zuciyarta ta dan kwanta su kuma suna so su kara taso mata da ita. Sumayya ta cire kayan ta ta saka simple ones sannan ta hada duk kayan da tazo dasu a jakarta, ana gam siyan baki itama zata tafi gida, sun riga sunyi magana da Adam yana jiranta a waje zai je ya kaita.
Suna nan zaune har Hassan yazo, suna jiran suga ya zo da motoci kanar yadda Hussain yazo dashi sai gashi daga shi sai Jabir. A palon sama suka zauna sannan Hassan ya kira wayar Sumayya yace mata gasu sunzo. A dole suka fito da Ruqayyah daga toilet suka kara gyara ta sannan suka lullube ta da mayafi suka fita da ita, sai taji a ranta cewa bata son mayafin ta irin alkyabbar gimbiya take so. Suka zaunar da ita a gefe sannan suka zagaye ta suna gaisawa dasu Hassan. Minal tace “ina sauran abokan?” Jabir yace “gani!” Tace “gaskiya kayi mana kadan kai kadai, ai munfi son da yawa yadda zamuyi ciniki sosai” yayi dariya yace “ciniki kuma sai kace wani kayan gabas?” Tace “ina jin dai ba ka kalli amaryar nan sosai ba, ai ta wuce kayan gabas ma ita” yace “wannan kuma sai dai a tambayi ango, ni ina ni ina kallon matar mutane?” Hassan ya dan leka kasan mayafin Ruqayyah yace “kinyi gaskiya, ta wuce kayan gabas, ta wuce kaya baki dayansu. Ni a gurina ta wuce komai fa. She is soo PRECIOUS to me” duk suka kwashe da shewa daya ta miko wa Hassan hannu tace “to kawo, tunda dai ka yaba sai ka biya” ya koma ya kwanta a jikin kujera yace “wanne biya zanyi kuma? Bayan na riga na biya sadaki ai na gama komai” tace “sadaki wannan nata ne, wannan kuma mu zaka sallama” Jabir ya zaro kudi daga aljihun sa wanda dama ta riga ya tanada saboda su ya ajiye a kan cinyar ta kusa dashi yace “duk tsadar ku dai wannan ya ishe ku” Minal ta dauka tana kimasta adadin kudin tace “wannan din, haba dai, kar ku bada mu mana, a matsayin sa na the whole CEO of H and H ai mota muka saka ran zai sallame mu da ita”.Duk kawayen suka yi shiru suna kallonsa kamar yadda shima yake kallon su daya bayan daya, sannan suka juya suka kalli Ruqayyah, shima ya juya ya kalleta duk da fuskarta tana rufe da mayafi. A hankali Ruqayyah ta saka hannu ta kamo hannun Sumayya ta rike a cikin nata, kamar me neman karin courage daga gareta. Minal ta sake cewa “wai kana nufin ba kaine CEO ba?” Hassan yace “ke waye ya gaya miki nine?” Jabir ya dafa kafadar Hassan yana kallon Minal yace “to ke menene naki a ciki? In shine in ma bashi bane ba ina ruwanki? Ku dai ba kudin siyan baki kuke so ba kuma gashi an baku?” Wata a kawayen tace “to ai matar tasa ce ta gaya mana shine CEO, wannan yasa muka fitar da kudi masu yawa muka yi kwalliya da sauran abubuwa dan kar azo aji kunya, kuma dan muna saka ran zamu fanshe kudin mu a jikin ku, yanzu kuma gashinan daga dukkan alamu ashe yaudarar mu tayi bashi bane ba ko kuma shine yake boye mana dan kar ya bamu abinda muke nema. Mu kuma ba za mu bar gidan nan ba sai an bamu mota”