TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Hassan yayi kokarin mikewa, ransa yana baci zuciyarsa tana baƙi, bai taba tsammanin yadda yake jin farin ciki a ransa lokaci daya zai iya komawa baƙin ciki ba. So yake ya kira security din gidan su zo su fitar musu da wadannan marasa kunyar yaran masu niyyar haddasa musu fitina a daren farkon auren su. Jabir ya sake rike shi fuskarsa da murmushi yace “to ke yanzu baiwar Allah da kike ta wannan jawabin akan lallai sai an baku mota in aka baku din me zakuyi da ita? Ku kusan goma sharing zaku ke yi?” Tana juya idonta tace “siyarwa zamuyi mana, mu raba kudin ko ma samu na kashewa zuwa wani lokaci” Jabir yace “shikenan, yanzu wata a cikin ku ta turo min account details dinta sai in tura muku kudin motar ku” Hassan yayi sauri zaiyi magana Jabir ya sake yi masa alamun yayi shiru da hannunsa. A take suka bashi kuma a take ya tura musu kudin. Yana shigar musu suka duba “ahhh wannan ai sai dai karamar mota zamu siya” yayi dariya yace “ku da ya kamata ku gode min na taimaka muku ba sai kunyi wahalar neman mai siyan mota ba? Kuma in kuka tashi siyarwa tayin wulakanci za’a yi muku ba lallai ne ma ku samu irin wannan kudin ba. Yanzu kuwa babu ruwanku da jira, kafin kuje gida ma zaku iya raba abin ku” da haka ya shawo kansu suka yadda, sannan suka dan saya fuskar Ruqayyah kadan yadda za’a gani. Jabir ya dan leka fuskar yace “to amarya, Allah ya sanya alkhairi, sai nazo cin ta tsotse” ya mike yana mikawa Hassan hannu “ango, Allah ya bamu alkhairi, na yi maka wannan yakin saura kai kuma kayi naka” ya fada da dariya a muryarsa amma Hassan bai mayar masa da dariyar ba kuma bashi da niyyar rama wasan da yayi masa. Minal tayi wa Jabir fari da ido tace “kuma tafiya zaka yi, ko dan ragin hanya babu?” Yace “rufa min asiri kar matata tayi min duka, sai dai ku fito a samo muku driver ya kai ku har gidajen ku, amma ni yanzu ma kira na take tayi nayi dare” ya fada yana duba wayarsa duk da babu wani missed call a kai.

Suka kwashi tarkacen su ba tare da wata kyakkyawar sallama ga Ruqayyah ba ballantana ga mijinta daya tasa ta a gaba yana kallon ta , fuska babu walwala. Suna fita gidan yayi tsit kamar an kawo sakon mutuwa. Sumayya ta cire hannun ta daga na Ruqayyah tana jinta totally out of place ta mike. “Tooo da haka haka, nima bara in kara gaba” Ruqayyah ta sake rike mata hannu “ba sai gobe zaki tafi ba? Dare fa yayi sosai” ta sake zare hannunta daga nata tace “ai ina da me kai ni, tun dazu ma yana waje yana jirana” ta fada tana kallon fuskar Hassan tana jiran ya bata amsa tunda yasan wanda take nufi amma sai taga ko kallonta bai yi ba. Ta shiga daki da sauri ta dauko jakarta ta fito sannan tace musu sai da safe ta sauka da sauri tun kafin bomb din ya tashi da ita, tana fita taga Adam a tsaye a jikin mota yana danna wayarsa, ya dago kai yana kallon ta yace “I thought you are never coming out” tace “kai dai tunda na fito shikenan” bata jira ya buɗe mata kofa ba ta bude baya ta saka jakarta sannan ta bude gaba ta zauna. Ya shiga ya kunna motar suka bar gurin, ta juya tana kallon gidan Hassan a ranta tana jin kamar wani ticking bomb ne a gidan wanda zai iya exploding any time. Ta san dama shi ramin karya kurarre ne amma bata san zai kure tun a ranar farko ba. But something yana gaya mata Ruqayyah will find a way out of this.

Sun jima a zaune, ita kanta a kasa, hannayenta a kan cinyarta, shi kuma yana facing dinta ya jingina bayan sa da jikin kujera. Studying dinta yake yi, amma sai ya kasa karantar fuskarta, so yake ya hango guilt ko kuma tsoro ko kunya amma bai ga komai ba sai dan guntun murmushi a fuskarta. Ta danyi gyaran murya yace “CEO? Really?” Ta dan dago fuskarta ta kalle shi sai ta mayar da kanta kasa tace “ceo? Menene ceo?” Ya bata fuska yana jin confusion yace “kawayen ki suka ce kince nine CEO na H and H” ta daga kafada tace “ba fa kawayena bane ba, ni kasan ba kawaye ne dani ba, da za’a yi bikin ne Sumayya da Minal suka gayyato su dan su tsaya a matsayin kawayena tunda bani da kawaye” yace “wacece Minal?” Tace “yar makotan muce a wancan gidan, wadda ta zauna anan” ta fada tana nuna inda Minal ta zauna. Ya sake cewa “amma suka ce kince musu nine CEO?” ta danyi dariya tace “ni fa na ce maka bansan abinda hakan yake nufi ba” yadda ta fadi maganar so innocently ya sa ya fara yarda da ita, to ita ina zata san wadannan business terms din? Yanzu fa ta gama secondary school kuma ga yanayin gidan su. A ina zata san me duniya take ciki? Yace “amma da suka fada me yasa baki karyata su ba a gabansu, duk da baki san term din ba sai ki musa ki ce ke baki fada ba, dan nan gaba kar su sake yi miki karya” ta dan sunkuyar da kanta tana dan rufe fuskarta kamar mai jin kunya tace “siyan baki na fa akeyi, in ana siyan baki fa ba’a magana” ya dafe kansa da hannu biyu yana jin kansa yana neman fara ciwo. Zuciyarsa da kwakwalwar sa suna yaki a tsakanin su, but son Ruqayyah yana rinjayar sense dinsa. Ya cire hannun sa daga kansa sannan ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna. Ya kamo hannun ta ya rike a nasa, ta sunkuyar da kai cikin jin kunya tana kokarin karbe hannunta amma yaki cikawa sai ta bar masa.

Yace “amma kunyi magana dasu akan aikina?” Ta daga kai tace “sun tambayeni aikin ka nace ban sani ba, amma sai na basu labarin daukan Baba aiki da kayi a H and H. Ina jin daga nan suka samu kalmar CEA din” yayi dariya yana girgiza kansa yace “CEO ake cewa. It means Chief Executive Officer, wanda shine matsayin da yafi Kowane matsayi girma a Company, shi yake da final say a duk decision making, wani ceo din kuma shine mamallakin Company, shine founder, shine kuma sole share holder” ta dago idanu tana kallonsa tace “and are you?” Ya girgiza kansa yace “noo, am not” taji dan sauran hope din da take dashi yana bin iska. Ta sunkuyar da kanta kasa, Ya sa hannu ya kuma dago da fuskar tata suna kallon juna yace “Hussain shine CEO kuma owner na H and H bani ba. Ni ko share ma bani da ita a cikin Companyn. Duk group of companies din nasa ne shi kadai. Ni maaikaci ne a karkashin sa nake aiki. Matsayina shine chief of staff, duk wani maaikaci na kamfanin a karkashi na yake, ni nake daukan su kuma Ni nake kula dasu. Nima Hussain albashi yake bani kamar yadda yake biyan sauran ma’aikata albashi. Gidajen nan guda biyu duk nasa ne, shi ya gina su, duk motar da kika gani a gidan nan da kuma gidan Aunty to Hussain ne ya siye ta, yana da passion for mota shi yasa yake chanjata kamar yadda yake chanja sutura. Duk abinda kika gani a gidan nan tun daga kan gadon da kika kwana akai zuwa chokalin da zamu ci abinci dashi Hussain ne ya siya” ta sunkuyar da kanta kasa tana fighting kukan da yake taho mata. Dama abinda ta aura kenan? Solobiyon miji wanda zai zauna kaninsa yayi masa komai? Shi me yake yi a lokacin da Hussain yake neman kudin? Ta rabu da Baba ta dawo hannun Hassan. Ita dai bata da Sa’a a rayuwa.

Ya sake dago kanta da hannunsa yana cewa “do you have a problem with that?” Ta girgiza kanta da sauri tace “babu matsala, kayansa ai kamar kayan ka ne. Kuma wata rana Allah zai hore mana namu mu tasar masa daga gida” yace “yes, da banyi niyyar zama anan ba, gida nayi niyyar in gina mana da kudin da nake ta tarawa. But ganin Baba ya fi mu bukatar gidan shi yasa na siya masa sauran kudin kuma nayi amfani dasu a biki, yanzu zan sake tara wasu kafin nan kafin mu tara zuri’a sai muyi ginin mu, shi yasa ban bari Hussain yayi mana gini irin nasa ba, saboda ba lallai bane mu gina irin nasa, kuma bana so in mun zo tashi muga kamar munci baya ne gwara muji cewa munci gaba. Kin fahimta?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button