TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta juya tana kallon side din gidan Hussain, ta nuna da hannu tace ” you mean……. Irin wancan zai gina mana……sai ka hana shi kasa ya gina irin wannan……..?” Yayi murmushi ganin irin tarin mamakin da yake kwance a fuskarta yace “eh mana. Har fushi yayi ya kaini kara gurin aunty” wasu hawayen takaici masu zafi suka zubo mata, wannan wanne irin rashin rabo ne da Hassan? Ya saka dan yatsa ya gogi hawayen yace “kuka? Kukan me kike yi kuma?” Sauran kukan ya kwace mata gaba daya, tace “kukan godiya nake yi ga Allah, wanda ya bani miji mai gudun duniya da hangen nesa kamar ka” ya zauna sosai yana kwanto da ita jikinsa yace “it is okay. Ki bar kuka, you have cried a lot a cikin kwanakin nan. Murna zamuyi muyi godiya ga Allah kinji” ta gyada kai tana tashi daga jikinsa. Ya mike yana mikar da ita itama. “Ki tashi muje to muyi sallah mu gode masa, in mun gode masa sai ya karo mana. Haka yace da kansa” ta mike tana goge idonta da bayan hannunta.

Sai da ya kai ta har dakin ta sannan ya fita, har yanzu bai debo kayansa daga tsohon dakin sa ba, yan kayan da zai bukata kawai ya dauko ya dawo gidan. Ya kai kayan dakinsa sannan ya koma dakinta ya tarar tana toilet har yanzu. Ya koma dakin sa ya shiga wanka shima.

Sai da ta yi kuka mai isarta a toilet sannan tayi wanka tayi alwala ta fito ta saka doguwar riga tayi sallar ishai da bata yi ba. Tana tashi yana shigowa da basket a hannunsa ya ajiye akan side table yace “kar dai har kinyi sallah kin barni” tace “sallar ishai nayi ai” yace “ohhh okay” sannan yazo ya shiga gabanta suka gabatar d sallar sunna da annabi ya umarci ma’aurata suyi. Bayan sun idar Hassan ya yi musu adduoin neman albarka a auren su, neman samun dacewa a duniya da kuma a lahira.

Suka shafa ya juyo yana kallonta ya dan hade rai yace “idonki, kamar ya kumbura, duk kukan ne?” Ta sunkuyar da kai tace “da rashin bacci ma, kasan in mutum yazo bakon guri baya iya yin bacci” yana murmushi yace “kar ki damu, yau zakiyi bacci har da munshari” ta mike tana jin wani iri a jikinta, sai yanzu take tunanin yama akayi ta yadda tayi aure yanzu ne? Ita yar karamar ta ina zata kai wannan mutumin? So take tayi tunanin ta yadda zata zille masa amma kwakwalwar ta ta toshe ta kasa aikin tunanin yadda zata yi dashi dan ita sam yau bakar rana take gani kar yazo ya kara wa ranar ta duhu dan bakikkirin take ganin sa.

Ta mike tana kokarin shiga closet taji hannunsa ya rufe kofar sannan ya murda key, ta juyo da sauri sai gata a kirjinsa, ya saka hannunsa a dayan side din ta yadda ta kasance a tsakiyar hannayensa. Ta fara yayyarfe hannu sauran kukan da bata karasa dazu ba yana dawowa. Yayi dariya yace “cry cry baby, tunda kin zama baby let me treat you as a baby” ba tare daya jira amsarta ba ya daga ta chalak kamar baby, ya zauna akan gado yana dora ta a cinyarsa, ya lura da yadda jikinta yake rawa kadan kadan, ta boye fuskarta a jikinsa. Yace “bafa wani abu zanyi miki ba, look at me, look at me precious” ta dan dago kai tana kallon serious face dinsa yace “nace ba wani abu zanyi miki ba, I just want to feed you that’s all. Na ga dazu baki ci abinci a gurin dinner ba, am sure da rana ma ba ci kika yi ba” tace “to ka sauke ni, zan ci da kaina” yace “to zan sauke ki, amma sai kin gaya min a fruits me kika fi so?” Tace “ni banason komai, ni bana shan fruits ma” ya dauko ayaba yana barewa yace “in dai kika cinye wannan to zan sauke ki kuma ba zan yi miki komai ba” ya fada yana kaiwa bakin ta, ta girgiza kai sai ya mayar nasa bakin yace “to shikenan, bara in cinye abata amma kuma duk abinda ya biyo baya ke kika siya da kudin ki” tayi saurin dawo da hannunsa baya tana saka ayabar a bakinta tana ci a hankali idonta a cikin nasa har ta gama cinyewa sannan tace “na cinye to” ya dauko cinyar kaza yace “saura wannan” tayi kamar zata yi kuka “ni ayaba kawai kace min ai” yace “ai ba rantsewa nayi ba”. A haka sai data ci kazar, shima kuma yaci. Tace “to na koshi, ka sake ni to” yana murmushi yace “ai ba rantse wa nayi ba” sannan ya juyo da fuskarta zuwa gare shi, ta rufe idonta, ya dora bakin sa akan nata.

A part din Hussain, a cikin Bedroom dinsa. Fatima tsaye a gaban mirror tana cire ear rings dinta. Hussain yana zaune a kujera yana amsa waya yana ta dariya, tana kallonsa ta mirror fuskarsa tana reflecting farin cikin da yake zuciyarsa. Tayi murmushi itama tana jin zuciyarta wasai. Bata da wani tension bata da pressure din komai sai farin ciki da annashuwar cikar burinta na zama matar Hussain. Rabin ranta. Ya ajiye wayar yana cewa “Time to switch off the phone, duk wanda bai kira ba yayi missing, duk kuma wanda bai zo ba shina yayi missing” ya karaso bayan Fatima ya tsaya yana tayata cire sarkar wuyanta yace “duk wanda bai ga kyalliyar Fatima ta yau ba yayi missing” tayi murmushi tana juyowa suna facing juna sannan ta mika masa hannunta yana cire mata awarwarayen ta tace “wanne mai missing din ne ya kira ka? Nasan duk wanda ya bar gidan nan yanzu ba zai kira ka ba” ya kamo yatsunta yana cire zobuna guda biyu da suke yatsun yana ajiye su a gefe yace “Sadiq ne, dan banza, bayan yaki zuwa bikin kuma shine zai kira ni yana min dadin baki” tayi murmushi tace “the prince of Abuja kenan. Shalelen Sarki Abdallah. Ina zai iya tahowa daga america ya bar his Arabian girlfriend?” Hussain yayi dariya yace “sai na gaya masa kina tsokanar sa” ta durkusa tana cire masa socks din kafarsa, sai ya kamota ya dago da ita yana kallon fuskarta yace “kinsan me yace min” ta girgiza kanta idonta a kasa, ya jawo ta zuwa jikin sa sannan ya kai bakinsa dai dai kunnen ta yace “yace wai insha strawberries before I kiss you, so that I will taste like a strawberry to you” ta danyi dariya tana sunne fuskarta a kirjinsa. Yace “kinsan amsar dana bashi?” Ta girgiza kanta ba tare data kalle shi ba, ya saka hannu ya dago fuskarta amma sai ta rufe idonta sai dai ta kasa daina murmushin da take yi, yace “nace masa ba zan sha din ba, cos when I kiss you, I want you to taste me, to taste Hussain not strawberry”.

Nasan ba yawa, ayi hakuri

Hassan ya danyi dariya yace “CEO na H and H? A ina kika samu wannan tatsuniyar?”

Wannan littafin na siyarwa ne, in kima so kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020Tun da ta shiga motar bata ce masa komai ba, hankalin ta yafi karkata ga halin data baro yaruwarta dan taga babu alamar Hassan zai bata kofar da zata kubuce masa. Ta lumshe idinta a ranta tana fatan Allah ya huci zuciyar Hassan ya rangwantawa Ruqayyah, duk da dai tasan ko da Ruqayyah ta samu kafar zamewa to kuwa tabbas Hassan zai diga mata alamar tambaya, wannan zai kawo doubt a rayuwar aurensu, zargi kuma zaizo ya shiga ciki, daga nan komai zai rushe. Dan zargi yana lalata aure komai karfin soyayyar da aka gina auren a kai.

Adam ya kalleta sannan yayi ajjiyar zuciya yace “ni bani na kar zomon ba, ratayar ma kuma ba’a bani ba amma an daura min laifi” ta juyo tana kallon sa tace “wato bayan magana da yaren hausa har karin magana ka iya ko?” Yace “ina cin A+ a hausa language sanda ina school” ta danyi murmushi ta sake yin shiru. Yace “what’s wrong? Ko har kin fara missing sister dinki ne?” Ta girgiza kanta da sauri, sai kuma taji hawaye ya taho mata. Tayi saurin gogewa kar ya gani amma da yake hankalinsa yana kanta ya gani din, yace “subhanallah. Kuka Sumayya?” Sai ya sauka gefen titi yayi packing duk kuwa da cewa babu motoci sosai akan titin. Ta sake goge idonta tana kokarin kirkiro murmushi tace “babu komai fa, mu tafi kawai, maybe kamar yadda ka fada ɗin ne, maybe missing Ruqayyah na fara tun yanzu” yace “is that right? Ni kuma a fuskarki banga haka ba, fuskar ki tafi kama da wadda take jin tsoron something will happen, ko kuma ma ya faru din” tana girgiza kanta tace “am just scared for Ruqayyah, ina tausaya mata rayuwar da zata yi a gidan Hassan” Adam yace “tausayi kuma? Ruqayyah fa oga Hassan ta aura, kin san kuwa kudin da mutanen nan suke dashi? She will never lack anything a rayuwarta” Sumayya tace “and that’s the problem Adam. Kudi sune problem din. Babu wanda ya san halin Ruqayyah Kamar ni a duniya kuma ni din babu wanda nake zama muyi hirar Ruqayyah dashi dan ita din tamkar wani barin jiki na ce da bazan iya butulcewa ba. Ruqayyah bata taba zama satisfied a rayuwarta, Ruqayyah bata taba murna da abinda ta samu, abinda bata samu ba shi take so. Na san kaddara ce ta hada Hassan da Ruqayyah amma aurensa da tayi, tayi ne saboda kudinsa, saboda tana tunanin kamfanin sa ne, yanzu da akayi auren ta fahimci na dan uwansa ne ina tsoro abinda zata aikata akan hakan” sai ta bashi labarin haduwar Hassan da Ruqayyah, dan brief soyayyar su, furtawar da Ruqayyah tayi da bakinta cewa Hussain yafi Hassan kyau, nuna wa da tayi tafi son gidan Hussain akan na Hassan, kin zama ta kalli kayan lefen gimbiya, da kuma abinda ya faru a gurin siyan baki. Bata san me yasa ta iya sakin bakinta tayi masa wannan zancen ba maybe dan abin yayi mata yawa a ranta ne, maybe kuma dan dadin ac da comfort din motar ne, maybe kuma it is something else.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button