TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bai yi mamakin maganganun Sumayya ba saboda shi dama yasan Ruqayyah bata da kirki, but bai san how deep rashin kirkin nata ya kai ba sai yau. Ya fahimci yaudarar Hassan take yi, ya fahimci kuma she is a danger to that nice lovely family. Amma kuma babu abinda zai iya yi akai, shi dai ba zai tafi gurin Hassan yace masa “matarka yaudarar ka take yi ba” in yayi haka yasan bayan aikinsa da zai rasa maybe har a cell sai ya kwana. Sannan babu wani problem din da hakan zaiyi solving dan Hassan din ba yarda zaiyi ba.

Ya juyo yana kallonta yace “now, what do you propose we do?” Tace “ban sani ba nima. Ni dai nasan sanda Ruqayyah tana gida ina yin iyakacin kokari na wajen ganin duk sanda zata yi ba dai dai ba na hanata. Ko da kuwa zata yi fushi dani. Amma yanzu bama tare babu kuma wanda zai ke bata shawara acan inda take, duk abinda yazo mata zuciyarta shi zata yi, wannan shine tsorona” yace “still you can do something” ya juyo sosai yana kallonta yace “na fahimci cewa ta yarda dake tana gaya miki dukkan sirrinta, to kiyi kokari ki yi keeping that relationship a tsakanin ku, ki ringa bibiyar ta kina jin abinda take ciki ta yadda zaki san plans dinta, ke kuma sai kiyi kokarin ganin kin dakatar da ita ko kuma in abin yafi karfinki ki gayawa wanda zai iya dakatar da ita. Kin fahimce ni?” Ta gyada kai. Yayi murmushi yace “and you stop worrying about her, yes ku twins ne kina son sister dinki and all that but still you have to put yourself first, rayiwarku daban daban kar ki zama so caught up a ta ta rayuwar ki manta da taki rayuwar, musamman yanzu da ba kwa tare, find something to enjoy, someone to love, someone like me” ya karashe maganar ta sigar wasa yana nuna kansa, tayi murmushi tana hararar sa, yace “ha! Finally tayi murmushi, you have no idea yadda murmushi yake yi miki kyau. Please don’t ever let something stop you from smiling” ya mayar da motar kan titi suka cigaba da tafiya a hankali, har yanzu da murmushi a fuskarta tace “enough about Rukee, tell me about you. Who is Adam?” Yayi ajjiyar zuciya, yes ya gaya mata secrect dinsa amma har yanzu baya son yin maganar fast dinsa, not now, sai yayi kokarin chanja maganar yace “Adam is going back to school this session” ta bude baki cikin mamaki tace “really?” Proudly Yace “yes ma” tayi dariya “amma naji dadi wallahi na taya ka da murna kuma. But wait…wai har ka tara kudin” ya girgiza kai yace “nooo. Oga Hussain ya tambaye ni abinda yasa ban koma school ba sai nayi mishi bayanin plans dina and he said da zarar am fara siyar da form inje in siyo zai biya komai” Sumayya tace “Masha Allah. Allah ya biya shi da alkhairi” yace “ameen. Yana da kirki sosai, ni dai zan iya cewa ban taba haduwa da mutum mai kirkin sa ba, kowa kuma a gidan haka yake fada, daga haduwa ta dashi zuwa yanzu ba zan iya lissafa alkhairan da yayi min ba, kuma ba wai kyautar ce mafi muhimmanci ba, a’a yadda yake treating mutane shine abin so” Sumayya tayi murmushi tana tuno fuskar Hussain, bata tunanin ta taba ganin sa babu murmushi a fuskar sa.

Adam yace “yanzu sai inje in siyo mana tare ko?” Ta bude ido “noo. Kar ma ka fara” yace “why not?” Tace “baba ba zai yarda ba, in dai har ina karkashin sa ba zai bari wani ya dauki nauyi na ba” Adam yace “okay, sai mu dauke ki daga karkashin nasa ai, ki dawo karkashina” ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta, a hankali kamar mai magana da kansa yace “ban ma san ta yadda hakan zai kasance ba but ina son ya kasance din, ya ilahi see me through” ta dago kai tana kallonsa yace “I want to marry you amma ban san ta inda zan fara ba” suka hada ido briefly, tayi saurin sunkuyar da nata idon kasa dan bata da amsar da zata bashi.

Sai da yayi packing sannan ta dago kai tana kallon kofar gidan nasu, tayi ajjiyar zuciya tace “nagode sosai Adam. Sai da safe” yace “kar kiyi saurin yi min sallama, go and knock ina nan ina jiran ki. Know that in Baba ya dake ki I will feel it here” ya nuna kirjinsa, ta kalli kofar gidan sannan ta kalli agogon motar, 12:32. Ta ja numfashin tsoro tana bude ido sannan ta fita da sauri taje ta fara knocking kirjinta yana bugawa. Ba’a jima ba aka bude mata. Allah ya taimake ta yan uwan su da suka je dinner duk suna nan dan haka ba’a yi bacci ba ana ta hira ana mayar da magana. Ta juyo tana kallon cikin motar da Adam yake zaune suka hada ido sai yayi kissing hannun sa yayi mata blowing, ta dauke kanta tana blushing, hoping wanda ya bude mata kofa bai gani ba. Sai da ta shiga ta rufe kofa sannan ya juya motar ya bar layin, sai a lokacin ya lura cewa bata dauki jakar kayan sawar ta ba.

Sumayya ta samu ta shige cikin mutane, amma bata buyar wa Inna Ade ba dan sai data yi mata magana “Sumayya ke kuwa me yasa kika taho da daren nan haka? Ba suna da dakuna a gidan ba ba sai kiyi kwanciyarki ba in yaso da safe sai ki taho?” Sumayya tace “Inna kawai ji nayi ina son in taho gida, shine suka saka driver dinsu ya kawo ni har gida” Inna tace “nan gaba kar ki sake tahowa da irin wannan daren, gwara ki kira wayar baban ku ki gaya masa dare yayi zaki kwana, karkarinta yayi miki fadan me yasa kika bari dare yayi miki amma ba zaice ki taho da daren ba” Sumayya tace “insha Allah Inna” sai kuma ta fara tambayarta yadda ta baro Ruqayyah “bata kukan ko? Ranar nan ance min kuka tayi tayi” Sumayya taji wani abu ya taba ranta, Allah sarki uwa, ita bata san Ruqayyah duk ba wannan ne a gabanta ba, tace “ta daina kukan Inna”.

Ruqayyah kam ta gaya wa yan garinsu a hannun Hassan, dan sam bai daga mata kafa ba duk kukan da take masa, a take ta yanke a ranta cewa shi din azzalumi ne bayan kasancewar sa solobiyo, ba wai nadamar aure kadai tayi ba, sai data yi nadamar taimakon sa dan bata san wannan shine sakamakon ta ba. Shi kuwa oga Hassan bakinsa har kunne dan exactly abinda yake so shi ya samu a gurin Ruqayyah wannan ya saka yaji duk sauran gurbin da bata gama cikewa a zuciyarsa ba yanzu ta cika shi taf. Sai yazo kuma ya fara aikin rarrashi, shine rarrashi shine gyaran gado shine jinya. Yawan kukan da tayi ya saka mata ciwon kai da zazzabi, da kyar ya samu ya lallabata ta sha paracetamol sannan ta kwanta ya lullube ta. Amma kuma sai ta saka masa rigimar cewa ba zai kwanta a kan gadon ba dan kar ya kuma tabata haka yana ji yana ganin lafiyayyen gado da lafiyayyar shimfida ga kuma matarsa a kai amma dolensa ya saka pillow a kasa a gaban gadon ya kwanta ya rufe idonsa saboda ya lura idonta yana kansa, sai daya tabbatar tayi bacci sannan ya hau kan gadon ya jawo ta jikinsa ya lullube su yana ajiyar zuciya. Me yafi aure dadi? Da murmushi a fuskarsa bacci ya dauke shi.

Da safe ma bata chanja zani ba, zaman jinyar ya cigaba dayi. Anan akan gado taci abincin safe da na rana, sallah kawai take tashi tayi itama sai ya fita tukunna wai dan kar yaga yadda take tafiya yayi mata ɗariya. “Ba zanyi dariya ba fa” ya fada yana kokarin gimtse dariyar, ta saka kuka “wallahi gashi nan dariyar zaka yi, gashi nan na gani bakinka yana abin dariya” dariyar ta kubuce masa yayi, tace “ba ga shi nan kana dariyar ba” ya rufe bakin yace “na daina, bara in fita in baki guri” ya fita yana cigaba da dariyar yarintarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button