TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana fita yaji mutane suna shigowa da sallama, ya sauka yana amsawa. Yan uwansu ne kaf dinsu da suka zo daga Gombe suka shigo, daga alama sallama zasuyi musu. Ya kara fadin murmushin sa yana karasa saukowa sannan ya gaida manyan ciki yaran kuma suka gaishe shi. Suka zazzauna shima ya zauna dattijan ciki suna tsokanar sa wai yana kyallin goshi. Ya shafa goshin nasa kamar mai son gogewa yana dariya, ya kasa daina dariya. Wata a ciki tace “ina amaryar to? A kira mana ita mana muyi sallama” ya shafa kai yace “tana sallah amma ban sani ba ko ta idar yanzu” Zulaihat data rako su ta mike tace “bara in dubo” ya bita da kallo kehar ta hau saman, a ransa yana tunanin irin dramar da za’ayi da Ruqayyah a gurin saukowa daga bene. Daga nan suka cigaba da hirar su shida yan uwansa, kawai sai jin muryar Ruqayyah yayi a bayansa, tana gaishe da mutanen gurin, suka amsa da amarya bata laifi ko ta kashe dan masu gida. Sai da ya waiga sannan ya lura cewa a tsaye tayi gaisuwar, yaji babu dadi a ransa amma sai ya bata uzuri da ciwon da jikinta yake yi, ai tayi ma kokari data iya saukowa daga stairs din. Yace “Zulaihat tashi ki kawo musu ruwa” nan take suka ce “a’a alhamdulillah, yi zamanki Zulaihat ba zamu iya sha ba” “ni cikina kamar zai fashe saboda koshi” “kayan gara muka samu a gidan Hussain, Fatima tayi ta loda mana wai sai munci, sai da kyar ta rabu damu kagan su can ma tray guda ta aika mana dashi gurin Amina wai ma ci a hanya in munji yunwa” Hassan yace “ta kyauta, kamar ta san ummah (kanwar kakarsu) dama da cikin zani, bata koshi” tace “ko ma cikin menene dani ci zanyi, dama zubi na daban tayi min kuma tace kar in bawa kowa in ajiye a firji in na koma gida” Ruqayyah tace “can kuka fara shiga kenan?’ Yadda tayi maganar yasa duk suka juyo suna kallonta tana tsaye a bayan kujerar da Hassan yake kai, Ummah tace “eh, can muka fara zuwa, shine a farko ai” kadan ya rage Ruqayyah bata bata amsa da cewa ai Hassan ne babba ba, sai kawai ta rabu da ita saboda Hassan yana gurin amma a zuciyarta tana tunanin ba suyi dai dai ba, ai Hassan ne babba dan haka gidan sa ya kamata su fara zuwa ba wai suje gidan Hussain sannan su zo suna basu labarin abinda suka ci a gidan ba, wannan gaskiya a ganinta rashin adalci ne da nuna bambanci.
Shirun da gurin yayi ne ya saka suka fara mikewa daya bayan daya “to mu zamu tafi, Allah ya sanya alkhairi, sai mun dawo suna kuma” suka fada cikin tsokana, Hassan yayi murmushi sannan ya bisu a baya zaiyi musu rakiya, Ruqayyah kuwa ko ci kanku bata ce musu ba ta juya ta komawarta sama.
Kwanaki suka wuce suka samar da sati biyu A cikin sati biyun nan kowane amarya da ango sun ci amarcin su son ransu. Hussain da gimbiya suna ta zuba lafiyayyiyar tsadaddiyar soyayyar su irin ta wayayyun ma’aurata. Duk yawon Hussain a wannan satin babu inda yaje in banda gidan Aunty. Amma fa shi nasa gidan kullum a cike yake da mutanen sa da mutanen gimbiya wadanda suke zuwa ganin gida da kuma cin arziki, duk kuma wanda yazo ɗin to sai yaci arzikin ya kuma bar arzikin a inda yake. Dan ita ma Fatima budadden hannu ne da ita babu yadda zaka shiga gidanta ka fito ba tare data baka wani abu ba, in ka hadu da Hussain shima ya kara maka. Kullum daga gidan aunty ake yin girkin safe rana da dare a kai gidan Hassan da kuma gidan Hussain, bayan yan aikin da Aunty ta basu kowa bibbiyu duk da cewa Fatimah ta taho da nata daga gida amma an kara mata, yammatan aunty kuwa tun da akayi auren gidan Fatima suke wuni su shiga duk inda suke so a gidan suyi duk abinda ransu yake so. In kika tarar dasu tare zaki dauka kannen ta ne. A bangaren Ruqayyah ma bakin suna dan leka mata, amma basa wani jimawa suke tafiya su koma gidan Hussain, abinda yake kara kona ran Ruqayyah kenan, ita gani take yi saboda kudin Hussain da tittle din Fatima ne yasa mutane suka fi zama a gurin su.
Tun da akayi auren bata taka kafarta part din Hussain ba, ba kuma ta jin zata shiga anytime soon dan bata jin tana da zuciyar da zata dauki abinda idonta zai gani, dan duk wanda ya shigo gidan ta indai ya shiga gidan Hussain sai ya bata labarin wani abin burgewa da ya gani a gidan. Bata kulasu sai dai kawai tayi musu fuskar shanu, wannan ne yake sawa su tashi su tafi dan kansu. And those comments are killing her inside. Ga nacin Hassan, shi ya kasa fahimtar ita ba wai son wannan abin take yi ba, tana dai bashi ne dan taga yadda yake tsananin son abin ita kuma top priority dinta shine ta kanannade komai nashi, yadda duk abinda take so zaiyi mata abinda bata so kuma ba zaiyi ba.
Ya na sakata ta shiga ta gaida Aunty kullum da yamma, a can suke haduwa da Fatima wasu lokutan. Ranar nan ma a kitchen ta tarar da ita da aunty da sauran yaran gidan wai tana koya musu wani tuwo da ake yi a gidan sarauta da ake kira da tuwon dalayi. A ranta tace “ji munafurci, sai kace ba bayi ne suke musu abincin a can ba” a lokacin ne Fatima take cewa da Aunty “aunty ni dai da zaki bi ta tawa da kin daina mana girkin nan haka, kiyi zamanki kiyi hutawarki” aunty tace “yanzun ma ai ina hutawa Fatima, babu fa abinda nake yi a gidan nan, ni ba aiki ba ni ba kasuwanci ba sai dai in saka TV a gaba inyi ta kallo” Fatima tace “duk da haka dai Aunty ki barshi, na gidan nan ma ku daina, in yaso su Nafisa suke zuwa can muna yi tare sai ake kawo muku kawai. Lokacin hutawarki ne yanzu. In kin gaji da zama guri daya sai a fitar dake ki zaga gari, in kin gaji da garin ma sai a kaiki wata kasar ki cigaba da hutawa. Ko Ruqayyah?” Ta juyo tana yiwa Ruqayyah wadda tun da ta shigo bata kulata ba murmushi, Ruqayyah tayi murmushi kawai, amma a ranta tana jin kamar ta rufe Fatima da duka, yanzu ita in aka daina kai mata abincin daga gidan nan ta ina zata fara dora abinci a gidan ta? Ita da bata iya irin wadannan girke girken ba.
Sai da suka gama tuwon suka jera a dining, wai yau duk a nan za’a hadu aci tuwon Fatima. Suka zauna a palo suna ta hira, anan taga Fatima ta kira Hassana suna magana a waya tana tsokanar ta wai tayi missing gashi nan za’a ci abinci gabadayan su banda ita, har tana cewa zata tura mata hotunan su. Yadda suke maganar ya nuna cewa sun saba sosai, sai Ruqayyah tayi realizing ita ko number din Hassana bata da ita kuma in banda rannan da suka gaisa a wayar Hassan basu taba waya ba tunda akayi bikin su. Wato dan ita yar talakawa ce kuma mijinta bashi da kudi shine suke wareta ko?
Suna nan zaune har Hassan da Hussain suka shigo, suma suka zauna aka cigaba da hira, Hassan yana ta kokarin ya saka Ruqayyah a cikin hirar amma sai dai tayi murmushi kawai ta sunkuyar da kanta, ita ba zata iya irin wannan rashin kunyar irin na Fatima ba.
Loma daya tayi wa tuwon taji ba zata iya ci ba, zuciyarta har ta fara tashi kamar zata yi amai, wani iri taji shi a bakinta. Amma sai taga su ci suke tayi suna santi, har da Hassan dinta dan abin kunya, wannan ai kunyata ta yakeyi. Sai da suka gama sannan Hussain yake cewa “aunty dama ina so in gaya miki monday muke so zamu tashi zuwa honeymoon” Hassan ya rankwashe shi sannan”yanzu auntyn kake gayawa zaka je honeymoon saboda baka da kunya?” Hussain yace “ouch, Fatima kina ganin sa zai nakasa miki miji ko? So yake ya hargitsa min ƙwaƙwalwa ta in kasa lissafi” Ruqayyah ta dauke kanta tana dan karamin tsaki, shi komai sai y nuna shi mai kudi ne, ko me y kawo zancen lissafi? Fatima Ta daga kafada tana masa alamar kunfi kusa, Aunty tace “Masha Allah, Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya. Ruqayyah kin shirya dai ko?” Zulaihat tace “ni na shirya Aunty, dani zaku tafi” Khadijah ta harare ta “ke kin fiya sakarci wallahi” Ruqayyah ta juya tana kallon Hassan, shima ita yake kallo, Hussain yace “ask him ooo Aunty, Mr Tsimilmila cewa yayi wai ba zasu je ba” Hassan yace “cewa nayi ba zamuje kasa biyar ba, me za’a je ayi a kasashe har biyar? Guda daya ko biyu in muka je sun ishe mu” Hussain ya kalli Aunty yace “kinji ba” Sannan ya juya gun Ruqayyah yace “convince your husband akan kuzo mu tafi tare, idan kika biye masa you are going to miss a lot.” Ruqayyah tana jin tunda akayi auren yau ne Hussain yayi addressing dinta directly.