TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta tura kujerar ta baya tana mikewa, abinda yasa Hassan shima mikewar yana tambayarta lafiya? Aunty ma tace “lafiya Ruqayyah? Ko abincin kirki baki ci ba” Tace “bana jin dadi ne sosai, wannan tuwon kamar bai karbi cikina ba. Zan dan koma gida, Aunty sai da safe” Aunty tace “ki je ki kwanta to, Allah ya baki lafiya, zan aiko miki da wani abu ki ci ko tuwon ne ba kya so”.
Hassan bai zauna ba ya bita da sauri a baya, amma saboda saurin da take yi da kyar ya kamota har ta kai kofar karamin gate din da ke tsakanin part din su dana aunty. Ya ruko hannunta “Hassana” ta juyo, tun daga idanuwan ta yasan ranta a bace yake yace “lafiya wai? Menene yake damun ki?” Ta juyo gaba daya tana rike kugu, tace “me akayi min? Okay yanzu na gane inda problem din yake” ta karbe hannunta tana kara sauri. Baya son ya ja hankalin ma’aikatan gidan zuwa kansu, dan haka sai ya rabu da ita ya koma cikin gida ya karasa cin abincin sa duk da hankalin sa yana kanta. Yana gamawa ya tashi ya tafi gida. A daki ya tarar da ita tana kwance da waya a hannunta. Ya zauna a kusa da kafafuwanta yana mammatsa mata su yace “ya jikin naki? Hope kinji dadi yanzu” ta ajiye wayar tana tashi zaune tace “naji dadi, dama tuwon ne naji ya tsaya min a kirji ya ki karasa wa” yace “akan maganar tafiya honeymoon ne? In kina so sai muje, bana son mu biyewa Hussain ne ” Ta girgiza kai tace “I don’t care about honeymoon, in baka so muje ba zamu je ba, duk abinda kake so shi zamuyi. What i care about is you mijina. Raina ya baci ne saboda naga ana neman a gaya maka magana a cikin mutane” ya dan bata rai yace “magana kuma? Wacce irin magana kike magana akai Precious?” Ta bude ido Tace “wai baka ji abinda Hussain ya gaya maka bane ba? Mr Tsimilmila fa yace maka, it is insulting ni a ganina” sai taga yayi murmushi sannan yayi dariya yace “my dear precious wife. Ba magana Hussain ya gaya min ba kinji? Wasa yake min, tun muna yara, tun primary school yake gaya min haka, mr Tsimilmila ko mr Careful duk haka yake ce min in yana so ya zolaye ni” ta daga kafada “okay, maybe dan ni macece shi yasa naji raina ya baci akan hakan, kasan mu mata muna da daukan karamin abu mu mayar dashi Babba. Dan haka ko da ace yana gaya maka haka a tsakanin ku bai kamata ya gaya maka a gaban mu ba, musamman a gaban matarsa, wannan ai sai ta zo ta raina ka tana yi maka wani kallo da daban, ni kuma ba zan iya tolerating wannan ba in tayi min na kyaleta bazan kyaleta ba in ta taba min mijina” Hassan yace “hold it! Fatima tana yi miki wani abu ne?” Ruqayyah ta koma ta kwanta sannan tace “bana son in fiya complain ne shi yasa ban taba gaya maka ba. But dama ya kake tunanin yar sarki zata yi treating yar mai gadin kamfani? Kamfanin ma kuma na mijinta. But ni ban damu ba …….” Ya kamo ta ya tayar da ita zaune, idanunsa suna nuna bacin ransa yace ” yar sarki da yar mai gadi, dukkan ku matsayin ku daya a gidan nan, duk kan ku zaman aure kuke yi a gidan nan. Daga yanzu duk ranar da ta kara miki ko da kallon banza ne ki gaya min ni kuma zan nuna mata cewa she is no longer in her father’s palace”
Wannan littafi na siyarwa ne, in kina so ki yi min magana ta WhatsApp through this number 08067081020Da fatan munsha ruwa lafiya, Allah ya karbi ibadun mu ameen.
Not edited
Ruqayyah tace “uhm uhm, ni bance kayi mata magana ba, kar taga kamar na hada ta da kai, ka barni da ita kawai ni ce dai dai yin ta va kai ba” sai kuma tayi murmushi tana ratayo hannunta a wuyansa “sorry mijina, na bata maka mood dinka” ya danyi mata murmushi yana shafa gefen fuskarta, kullum kyau take kara yi masa yace “kar ki kula ta kema kinji, ki fita daga harkarta kawai bana son wani abu ya hada ku saboda Hussain. Kinji? Promise me ba zaki kulata ba, one day zaiyi realizing abinda ya auro cos na gaya masa tun dadewa. I warn him about her” tayi ajjiyar zuciya tace “shikenan, duk abinda kace shi zanyi”.
Ya mike ya fita sai gashi da system dinsa ya dawo, ya zauna akan kujera tare da kiranta “Precious zo ki gani, kinga guraren da Hussain yake son muje. In kina so sai mu bi su mu tafi tare” ta taso ta zauna a gefen sa tana kwanto da kanta jikinsa, ta karanta sunayen guraren, ita ko sunan ma vata taba ji ba kuma bata san wadanne kasashe bane ba. But koma ina ne tunda har jirgi za’a shiga a bar kasar nan ai kuwa va za’a barta a baya ba. Amma sai ta boye excitement dinta tace “ba naji kace ba zamu je ba?” Yace “in kina so sai muje” tace “ina ganin muje din kawai, kar Hussain yaji babu dadi, kaga har ya kai kararka gurin Aunty” yace “ai ya riga yasan saboda menene. Ni bani da lifestyle irin nasa” sai kuma yayi murmushi yana kallon dan karamin bakinta yace “but since we are talking about a honeymoon tare da ke, I think I can make an exception” lips dinta suka bude tana murmushi, yayi murmushin shima yana kallon fuskarta, duk wata damuwarsa tana wucewa tare da murmushin ta. “I am going to enjoy this” ya fada yana jan fuskarta zuwa gare shi.
A gurin Aunty Fatima tayi hirar darenta, Hussain yai ta zungurin ta akan su tashi su tafi tana share shi. Sai ya mike yana kirkirar hamma “na gaji sosai yau din nan. Aunty sai da safe zan tafi in kwanta” Aunty tace “Allah ya bamu alkhairi” ya kalli Fatima yace “sai da safe” ta dauke kanta tana kokarin rike dariya. Yana fita Aunty tace mata “tashi ki bi mijin ki, dan ba ta ido ce dashi ba zai iya sake dawowa ya sake yi mana wata sallamar” Dole Fatima ta mike Khadijah da Nafisa suka raka ta har kofar part dinta.
Tana shiga ta amsa gaisuwar bayinta su biyar da suke da dakuna a karamin palonta na kasa, inda anan din ne dai kuma yan aiki da Aunty ta bata suke. Sai data dan yi hira dasu kadan sannan ta wuce kitchen. Yarinyar ta da taje da hakkin kula da kitchen ta bita a baya da sauri, suna shiga ta tambaye su abincin da suka dafa, ta gaya mata sai ta yamutsa fuska tana girgiza kai sannan ta bude freezer ta saka yarinyar ta dauko kaza, tace “ina irin pepper soup din nan da muke yi a gida mai dankali?” Yarinyar ymta gyada kai da sauri tace “shi za’a yi miki? Yanzu kuwa zanyi miki” Fatima tace “shi zakiyi, amma bani zaki yi wa ba in kin gama ki zuba a mazubi mai kyau ki je ki kaiwa Ruqayyah kice gashi in ji ni” da sauri ta amsa da “to ranki ya dade, an gama” daga nan Fatima batakuma tsayawa ba sai turakar mijinta.
A dakinsa ta same shi daga shi sai towel yana ta zagaye da waya a hannu. Ya juyo yana kallomta sai ya yar da wayar ya rike kugu, ta jingina da jikin kofar tana murmushi yace “da baki taho ba ko, da zuwa zanyi in dauko ki aka tun daga gaban Aunty har nan” ya fada yana nuna kan gadon sa. Ta bata rai tana kallonsa tace “na yi fushi, shine kayi wankan ka ka rabu dani ko?” Ya tako zuwa gabanta yace “waya gaya miki nayi wanka? Ni na isa? Ta yaya zan wanke baya na?” Ta dan taba gashin kansa tana dubawa ko da ruwa a jiki, yayi dariya yace “banyi ba fa na gaya miki” tace “da kayi wanka ka barni ko, da yau ba zanyi wanka ba haka zan kwanta” ta fada cikin shagwaba. Ya jawo ta zuwa jikinsa, hannunsa a bayanta yana zuge zif din rigarta yace “na gaya miki ai, ba zan sake wanka ni kadai ba” ta fara dariya kuma sai ta dauke wuta saboda hannun sa da taji a cikin rigarta.