TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Bayan Hassan ya gama nunawa Ruqayyah guraren da zasu je sai ta sake komawa dakinsa zai mayar da system dinsa, a lokacin ne ta jiyo maganar mutane daga waje, ta daga labuke ta leka window ta hango Fatima dasu Nafisa a kofar gidan Hussain, sai taga su Nafisa sun juya sun koma Fatima kuma ta shiga. Ta tabe baki, wayo gimbiyar ba ma zata iya tahowa ita kadai ba sai an take mata baya, amma ita sanda zata taho ai babu wanda ya rako ta duk kuwa da cewa ta nuna bata jin dadin jikinta. Ta fara kokarin cire kayanta da niyyar yin wanka, so take yau tayi amfani da rashin lafiyar da take ji ta gudu daga gadon Hassan. Tana fitowa daga wankan Hassan ya dawo dakin, shima har yayi wankan sa ya saka na bacci, ya bibta da kallo tana shafa mai a jikinta. Ya karaso yana karbar robar man. “Menene aiki na a gidan nan idan har na barki kina shafa mai da kanki” ta dan bata fuska “shafa mai ai ba aiki bane ba, zan iya da kaina” yace “akwai guraren da hannun ki ba zai kai ba. Ki kawo in shafa miki ko ina da ina, in tabbatar ko ina ya samu” ta lura da irin kallon da yake yi mata sai ta dan rike cikin ta kadan tana yamutsa fuska. Yace “ya dai? Ko cikin ne?” Tace “dazu ma sai da nayi amai, kuma yanzu yunwa nake ji. Ni tunda aiki kake nema ma da abinda zanci ka samo min” ya dan shafa kansa kadan yana kallon kirjinta “kuma shafa man fa?” Ta tura baki, ni ina jin yunwa ina zan damu da wani shafa mai” yayi ajjiyar zuciya “shikenan, let me go and get you something”. Ta bishi da ido har ya fita, sannan tayi dan karamin tsaki. “Duk an bi an lugwuigwuicewa mutum jiki an bar ni da ciwon jiki”.
Key din mota Hassan ya dauka ya fita, bai ma san inda zai samu abinci ba, shi ba mutum ne da ya saba da cin abinci a waje ba dan haka bai san guraren cin abinci ba. Yana fita yarinyar Fatima tana kaiwa Ruqayyah abincin da ta aika mata dashi. Tata yarinyar ta karba sannan ta hau dashi sama saboda ta ga fitar Hassan, ta shiga dan madaidaicin dining area dinsu ta ajiye sannan taje tayi knocking a kofar Ruqayyah, sai data ji tayi magana sannan tace “sako ne gimbiya Fatima ta aiko miki dashi”. Sai da Ruqayyah ta gama shafe shafen ta sannan ta saka doguwar rigar bacci wadda ta tsaya a gwuiwar ta mai siririn hannu ta fito tana daure kanta da ribbon, a ranta tana mitar tunda tazo gidan kullum sai ta wanke kanta gashi har gashinta ya fara lalacewa. Ta bude warmer din abincin a take taji yawunta ya tsinke, ta saka spoon ta dandana sai ta ja kujera ta zauna ta fara ci, sai data kusa koshi sannan ta tuna ta tura Hassan neman abinci. Ta dauko wayarta ta kira shi “kina ta jira na ko? Yanzu na kira Jabir yayi min kwatancen wani guri” tace “ka bar shima, har na dan dafa wani abu ma naci” yace “ayyah. Sorry Precious. Jikin yayi sauki kenan” tace “babu laifi”
Sauran data rage yazo shima yaci “amma yayi dadi sosai, sharp sharp haka har kin gama? Kai amma yayi dadi sosai” tayi murmushi kawai. Ita bata taba ganin irin wannan abincin ba ma ballantana har ta iya. Sai kuma ya ajiye chokalin hannunsa yana kallonta, ta gane kallon dan haka ta mike zata gudu, ya jawo ta ta fado cinyarsa. Wannan dai wankan da bata son yi sai data yi shi.
Washegari yace mata ta shirya zasu je ayi mata passport. Ta roke shi kuma zata je ta yiwa yan gidan su sallama. Ta shirya sosai tayi kyanta, shima haka, sannan suka fito tare suna hirar su yana yi mata alkawarin zai koya mata mota in sun dawo. “Duk san da zaki fita ko ina office ne sai kiyi tafiyar ki kawai” a kofar gidan ne taga abin mamakin da ya saka ta tsaya ta kasa motsi. Adam ne a tsaye a jikin mota yaa goge ta, ya dan rissina ya gaishe da Hassan sannan ya mika masa key din motar. Sai kuma ya juyo yana kallon Ruqayyah yace “Madam barka da fitowa” ta nuna shi da hannu “kai! Me kake yi anan?” Hassan ya juyo yana kallon ta yace “kin san shi ne?” Bata amsa ba ta sake cewa “me yake yi a gidan nan?” Yace “Sumayya bata gaya miki ba? Let’s go, zan gaya miki a hanya” ta sake juyawa tana kallon Adam sai ya daga mata kafada sannan ya juya yayi tafiyar sa hannayensa a cikin aljihun wandon sa.
Ta bude motar ta shiga shima ya zagaya ya shiga. Yana zama tun kafin ya tayar da motar tace “me Adam yake yi a gidan nan?” Yace “wai dama kin san shi ne? Da naga Sumayya tana biye miki shi na dauka baki san shi ba bata son ki sani” ta kara bata fuska tace “Sumayya? Wai kana nufin kasan shi tare da Sumayya?” Yace “a tare ma na gansu. Daga baya ba dauke shi aiki, yanzu driver ne shi a gidan nan. Yadda na fahimta kamar saurayin ta ne” ta sake cewa “Sumayyan? Lallai wannan yarinyar ta wuce duk inda nake tunani wallahi. Wato ashe Adam ne suke waya dashi, shine wanda ta karbi number dinsa a hannun ka kuka ce min wai abokin ka ne” yayi dariya, “I noticed bata son ki sani, I tot zata gaya miki kafin bikin mu shi yasa ban gaya miki ba” tace “ba zata gaya min ba ai. Ta san bata da gaskiya” ya dan bata rai yace “menene problem din? Ni a ganina kamar bashi da problem except that he was a christian sai ya musulunta, iyayensa har yanzu Christians ne. But character wise bana jin yana da aibu” Ruqayyah ta rike baki, tubabbe? Yanzu Sumayya a kan tubabbe zata kare? Amma ganin Hassan yana nuna hakan ba komai bane ba sai bata yi comment akan hakan ba. Amma sai tace “no you are wrong, yana pretending ne amma bana gari bane ba. A inda na sanshi, a inda muka fara haduwa dashi a motar sa ne taxi ya dauko mu daga school ni da Sumayya, and ge tried to touch me, a gaban Sumayyan. Shi yasa nayi mamaki da har zata kula shi har suke soyayya” Hassan yayi shiru maganar tana taba zuciyarsa, wato abinda ya dauko ya kawo musu gidan su kenan? Yace “tabbas biri yayi kama da mutum. Ranar dana fara ganin shi a kofar gidan ku ya faya min gaisawa yake so kuyi, amma sai yace da Sumayya zasu gaisa dan yasan in ya miki magana maba zaki kula shi ba. Wato wannan shine dalili” tace “tabbas. Yasan ni ba zan kuka mai dabi’a irin tasa ba”. Kafin su je gidan Baba Hassan ya yanke hukuncin korar Adam. “Muna da yammata a gidan, he is a risk to them”.
Sai da suka je aka yiwa Ruqayyah passport aka gama sannan suka biya ta bakery suka yiwa su Inna siyayyar kayan kwalama, suka kuma siya musu fruits da drinks da yawa sannan ya kaita gida, bai shiga ba yace zaije unguwa shima sai ya dawo zai shiga, ta turo Zunnur ya kwashi kayan ya shigar musu dashi.
Ita kanta sai data gansu sannan ta san tayi missing dinsu. Suma suna ta murnar ganinta kamar wadanda suka yi shekara basu ganta ba. Ta basu labarin tafiyar da zasuyi da Hassan da Hussain da Fatima, nan take su Zunnur suka fara jera mata list na kayan da zata siyo musu tsaraba. Anan suka ci abincin rana tare a palo, sai taji ta kasa cin abincin sosai duk kuwa da cewa babu laifi da kyansa duk da babu kaji amma akwai kifi da ganye a ciki. Amma kifin ne ma taji yana tayar mata da zuciya.
Sai da suka shiga daki da Sumayya zasuyi sallah sannan ta tayar mata da zancen Adam “yanzu dama Sumayya ashe Adam ne kuke wayar nan dashi? Duk wannan murmushin da kike yi ashe Adam kike yiwa? Yanzu ki rasa wanda zaki yi soyayya dashi Sumayya duk mazan garin nan sai inyamuri? Ina samarin hausawa? Ina fulani? Ina bare bari ina shuwa ina duk sauran kabila masu mutunci amma duk basu yi miki ba sai inyamuri? Kema kanki kinsan Inna Ade da Baba ba zasu taba karbar wannan maganar ba” Sumayya da take tsaye da hijab a hannun ta tace “kin gama? To bara in tuna miki, ni ce nake sonsa ba ke ba, in auren nema ni zan aure shi ba ke ba, ina ruwanki?” Tace “da ruwana mana, ke fa yaruwa tace, shi kuma drivern miji na ne, ba kya ganin alakar tsakanin ku kamar disgrace ne a guri na. Dama can ana min kallon wulakanci ballantana kin kara zubar min da mutunci” Sumayya tace “okay shine problem dinki? To ni babu ruwa na da kasancewar sa drivern mijin ki wannan problem dinki ne” Ruqayyah tace “amma dai ai na tabbatar kina da problem da kasancewarsa tubabbe ko?” Sumayya ta juyo tana yi mata wani irin kallo, Ruqayyah tayi dariya “ohhh kar dai kice min duk murmushin da kuke yiwa juna bai gaya miki ko shi waye ba” Sumayya ta ajiye hijab din hannunta tace “don’t ever call him that again” Ruqayyah tace “in na sake kuma fa? Me zaki yi min?” Sumayya tace “zan tabbatar baki sake yiwa wani rashin kunya ba” Inna ta bude dakin ta tsaya tana kallon su “ohh ni Sa’adatu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu yaran nan kwanan ku nawa baku hadu ba, amma daga haduwarku har zaku yi fadan naku da kuka saba? Yanzu kuma me ya hada ku?” A tare suka ce “babu komai Inna”.Har suka gama abinda zasu yi suka dawo gida Hussain hankalin sa yana kan maganar Adam. Yaron yaki ya gaya masa gaskiyar abindaya faru maybe daya gaya masa da yasan abinda ya kamata yayi. Shi tun farko hankalin sa bai kwanta da Ruqayyah ba, sai dai kuma a yanzu matar dan uwansa ce dan haka bibiyarta da kuma saka ido a kanta ba zai yiwa dan uwan nasa dadi ba. Dole sai yabi a hankali, dole sai ya nemi dabara yadda zai bullowa lamarin ta lumana ba tare daya taba zuciyar dan uwan sa ba.