TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Suna dawowa gida ya wuce part din Aunty ya gaishe ta, a can ya tarar da Hassan shima ya shiga gaisheta, Hassan ya dauke kansa yayi kamar bai ga shigowar Hussain ba shi kuma sai ya kama tsokanar sa wai yaga alamar har wani tumbi ya fara ajiyewa saboda jin dadin amarci. “Me Ruqayyah take baka ne? Zan ke aiko da kwano na nima ana sammin ko na kara kumari da kwarjini” Hassan ya kalle shi kawai ya dauke kai, Aunty tace “an kuma kenan, me ya hada ku?” Hussain yace “aunty driver na ya kora, ni kuma nace na mayar dashi bakin aikinsa shine yake fushi” Aunty tace “akan driver kuma? Hassan me yayi maka da zafi haka da har zaka yi fushi da dan uwanka?” Hassan ya mike yana daukan wayarsa yace “ya wuce aunty, laifi na ne dama, drivern sa ne shi yake biyan sa albashi, motar sa ce gidan sa ne, I should have know my place, yanzu kuma na sani dan haka zanyi minding business dina” aunty ta rike baki tana salati yayin da Hassan din ya juya ya bar gidan. Tabbas yan biyun nata suna fada, amma mostly fadan nasu yafi yi mata kama da wasa dan akan silly silly things suke yin fadan,but na yau is different. Na yau ba wasa bane ba.
Ta juya tana kallon Hussain tace “ka sallami drivern Hussain” ya girgiza kansa “Aunty ba zan iya ba. Kuma akwai dalilin da yasa ba zan iya din ba” ya dago yana murmushi yana kallonta. “Ki rabu dashi, yadda ya hau shi kadai haka zai sauko shi kadai”
Daga gidan aunty hassan gidan sa ya zarce, a palo ya tarar da Ruqayyah a kwance a kujera da packet din chewing gum a gaban ta tana kuma cin wani, tayi masa murmushi amma sai ya wuce ta ba tare daya mayar mata ba, ta bi bayansa da harara sannan ta cigaba da wayarta. “Wallahi ina gaya muki Rukee sai kin waye, in ba haka ba kina ji kina gani za’a mayar dake tsumman goge kashi” tace “to Minal me zanyi? Kin ga fa su Fatima ce tasu, sam basa ma shigo bangare na sai gurinta, saboda zata dauko abin duniya ta basu ni kuma bani dashi” Minal tace “nema zakiyi kema ai, in baki dashi ai mijinki yan dashi shine zai baki ai. Ki san me yafi so ki ringa yi masa, ki kwantar da kanki sosai kar ki sake ki nuna masa wannan zafin ran naki, ba dai shine babba ba? In dai kin kama babban yayansu ai kin kama su gabaki dayan su babu wanda zai isa yayi miki musu. Kuma suma ki shiga cikin su, ki nuna musu soyayya kamar ruwa, ai da haka ake jan ra’ayin mutane, ke yanzu ko yar kissar nan ma ashe baki iya ba? Ai nuna musu zaki yi duniya babu yasu. Ki kafa gwamnatin ki sosai sannan ki fara diban rabonki. Dakin samu kin tara ki sayi gida, in kin kuma tarawa ki kuma siyan wani. A haka in rabuwa ma tazo Allah ya kiyaye kin ga kin samu madafa, tunda dai ba wani sonsa kike yi ba nasan auren ba wani guri zaije ba” Ruqayyah ta bata rai tace “wannan ai mugun fata ne, kuma ni yaushe nace miki bana sonsa?” Minal tace “ko kima sonsa ma na tabbatar kinfi son kudinsa a kansa, ko ba haka bane ba?” Ruqayyah ta jiya ido tace “to waye bayan san kudi? Annabi ma da kansa yace mu nemi tsari da talauci dan talauci musiba ne. Duk wanda yace baya son kudi to munafiki ne” suka yi dariya tare. Minal tace “yanzu yana ina?” Ruqayyah tace “yana dakinsa ina jin. Yanzu muna wayar nan ya shigo ya haye sama, kin san fushi yake yi akan maganar drivern nan” Minal tace “amma lallai Ruqayyah sai na kai ki ina jin gurin Aunty Hafsa ta wanke min ke, yanzu mijin naki yana fushi shine kika barshi ya tafi daki shi kadai? Mijin ma kuma mai kudi irin wannan? Ai ko da baki yi laifi ba zuwa zakiyi ki ba shi hakuri. Ki lallaba kayanki in ma yaga laifin ki ya dawo yana ganin laifin wanda ya fadi laifin ki”.
Da haka suka yi sallama Ruqayyah ta tashi ta hau saman itama, sai data fara shiga dakinta ta shafa turare saboda jin ta take yi kamar tana dan tashi kadan duk kuwa da cewa tayi wanka ta kuma saka turaruka iri iri, amma ta na jin kamar kalar turaren da ta saka ne bata so. Ta shiga dakinsa ta tarar ya fito daga wanka yana shafa mai, ta bi kirar jikinsa da kallo sannan ta danyi masa murmushi “yanzu ni shikenan sai mijina yazo ya wuce ni ko kula ni ba zaiyi ba, kawai sai yake fushi dani duk da bansan laifin da nayi masa ba?” Bai ce komai ba ya fara shafa man sa, ta zo gabansa ta tsaya tana shagwabe fuska kamar zata yi kuka. Ya zauna a bakin gado sai ta bishi ta zauna akan cinyarsa tana leka fuskarsa. “To ni ka kalle ni mana? Ni ka gaya min laifin da nayi maka” ta fada tana kakalo kuka. Ya dakata da abinda yake yi yana kallon ta sai ya fara tunanin laifin menene tayi masa wai? Menene laifinta a cikin maganar? Ai kamar ma ita akayi wa laifi ko?
Sai ya kara hade fuska yace “shine kuma bayan kinga nayi fushi kika rabu dani ko?” Ta matso hawayenta “to ni ai bansan me zanyi maka ba, ka taho daga dakina ka dawo nan bayan tunda nazo a dakina muke kwana, ka saka ni na kasa bacci ina ta jin tsoro cikin dare” ta kara matse kwalla “kuma dazu ma da nayi maka murmushi baka rama min ba” ta turo baki.
Ya bi bakin da kallo yana jin murmushi yana forming a fuskarsa, yarinya ce Ruqayyah in ma laifin tayi kamata yayi ya gaya mata abinda tayi din ballantana shi yanzu ya fahimci babu laifin da tayi in banda fadar laifin Hussain. Wannan ne laifinta. Kamata yayi ya gaya mata cewa baya so a fadi laifin Hussain ba wai yayi fushi da ita ba.
Ya zagaye hannayensa a kugunta yana dora goshinsa akan nata, idonsa cikin idonta da yake cike da kwalla “am sorry Precious ki daina kuka kinji. Nine ko?” Ya kama kunnensa daya da hannu daya ya ja yace “wannan Hassan din baya jin magana tunda ya sa matarsa kuka” ta dan yi dariya kadan sai ya goge mata hawayenta yace “baki yi min laifin komai ba kinji? Raina ne kawai ya baci. Kema kiyi hakuri akan maganar drivern nan kinji? A hankali zanyi wa Hussain baya ni yadda zan gamsu da dalili na na korar sa” ta kwantar da kanta a wuyansa tana jin dadin kamshin shower gel din da yayi amfani da shi tace “ni na bar maganar ma ai, ina fata ne kawai kar Hussain ya gane when it is too late. Damuwa ta kawai ita ce kai mijina, ina tsoron kar drivern nan ya raina ka” Hassan ya danyi dariya yace “it is never going to happen kinji. Kar ki damu akan hakan” ya dagi fuskarta yana kallo yace “mutane suna tsokana ta wai ina kyallin angonci, they should come and see yadda fuskarki take haske kamar wata zahra” ta kwace fuskarta tana sake mayar da kanta cikin wuyansa, yace “daga ni to Madam in tashi in shirya” ta makale kafada “naki din. Kamshin ka dadi” ya kyalkyale da dariya yana komawa da baya yana kwanciya akan gadon, ta bi jikin sa ta kwanta itama, ya rufe ta da hannayensa yana sauke ajjiyar zuciya.
Hussain daga gurin Aunty shima nasa part din ya tafi. Part din gimbiya ya zarce ya shiga har cikin Bedroom dinta amma bata nan, sai ya dauki waya ya kira ta, ta masa tace masa tana gym, ya fita ya tafi can. A can ya same ta ta kunna slow music kan treadmill tana tafiya da dan sauri kadan, bata ji shigowar saba, shi kuma yayi amfani da damar gurin tsayawa yana kare mata kallo a cikin gym wears dinta yana lura da jikinta yake motsawa tare da kowanne motsin ta, gashin ta data tubke guri daya yana kwance akan kafadarta guda daya, bakin ta yana motsawa a hankali tana bin wakar da take tashi a gurin.