TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya danyi gyaran murya kadan sai ta juyo da sauri tana kallonsa, sai kuma tayi masa murmushi tayi amsa alamar ya taho da hannunta. Ya zo ya tsaya a gefenta yana kara bin jikinta da kallo, fuskarta ta nuna alamun jin kunyarsa, yace “what are you doing?” Tace “getting in shape for the honeymoon” yayi dariya, “wa ya gaya miki ana fafe gora ranar tafiya?” Ta bata rai “to ni bana son in munje kaga turawan da suka fini shape mai kyau” ya dora hannunsa akan plat cikin ta yace “ni ban taba ganin baturiyar da take da shape daya kai naki ba Fatima, in kuwa akwai to babu wadda nata ya wuce naki” ta harare shi tace “in akwai kuma fa” yayi dariya yace “bazan kalla ba, kona kalla ma ba zan gani ba” tayi masa murmushi tana slowing down har ta tsaya sannan ta kashe machine din, ya jawo towel a gefe yana goge mata jiki yace “daga gurin Aunty nake, Hassan fushi yake yi dani” ta juyo tana kallon sa tace “akan me?” Sai ya bata labarin abinda ya sani a game da Adam. Sai kawai yaga tayi dariya, ya bata rai “au dariya kike yi min ma ko?” Tace “ba kai kadai nake wa dariya ba, ku biyun nake yiwa dariya da har kuka biye wa Ruqayya. Ruqayyah fa? Ruqayyah ai yarinya ce, sa’ar Zulaihat ce fa aka ce. Yarinta ce take damunta bawani abu ba kuma shima kansa Adam din da kuke magana a kansa yaron ne shina. Ni kasan abinda bake tunanin ya hada su? Irin abin yaran nan ne ko shi yace yana sonta tayi turning dinsa down sai ya koma kan kanwarta ko kuma ita tace tana sonsa shi kuma yace kanwar yake so. Shine suke holding grudges. Amma hakan bai kai ta saka a kore shi ba. Abinda Ruqayyah take bukata yanzu shine guidance, tana bukatar wanda zai koya mata abubuwan da suka danganci zama da miji zama da mutane da sauransu. Wannan zai taimaka mata wajen girma. Shi yasa na sage akan muyi tafiyar nan tare saboda mu samu damar bonding ni da ita, I have so many things to teach her” ya bata rai yace “wato da ita za kiyi bonding ba dani ba ko?” Ta zagaye hannayenta a wuyansa tace “kai ai kaine ginshikin komai, kowa kaga na kula albarkacin ka yake ci” yayi murmushi yana kallon cikin idonta yace “you know I love you right?” Tayi murmushi “and I love you too”.

Tun ranar da Baba ya bawa Sumayya damar ta gaya wa Adam yake zuwa gidan daukan karatu ta kira shi a waya da niyyar sanar masa, sai dai abinda ya gaya mata akan ganinsa da Ruqayyah tayi da kuma abinda yake tunanin zata aikata ya saka taji jikinta yayi sanyi ta kasa gane a wanne bari na zuciyarta zata saka maganar, tasan kuma tsaf Ruqayyah zata iya sakawa a kori Adam daga aiki vabu abinda yayi mata zafi da future dinsa da hakan zaiyi destroying ko kuma tunanin inda zaije, in dai har birinta zai cika ita bata tunanin kowa. Washegari kuwa sai gashi ya kira ta yana gaya mata cewa an kore shi din, amma kuma an sake daukan sa wani aikin. Ya bata labarin yadda suka yi da Hassan da kuma yadda sukayi da Hussain, sai ta taya shi murna sosai musamman daya gaya mata Hussain ya sake bashi sabuwar offer of employment wadda albashin daya rubuta masa ya fi na wanda Hassan ya rubuta masa. Sai dai kuma a wani bangare na zuciyarta tana jin rashin dadin sabanin ra’ayin da aka samu a tsakanin tagwayen. Tasan irin shakuwar dake tsakanin tagwaye tunda ita ma sune, sai tayi addu’ar Allah ya tsayar haka. Daga nan kuma sai ta shigar masa da maganar Baba “albishirinka” yace “goro, Baba yace ya bani ke?” Tayi dariya “haka nan kawai sai Baba ya baka ni ba tare da ka tambaya ba? Sai kace wata riga?” yayi ajjiyar zuciya yace “haka ne, to meye albishir din?” Tace ” nayi wa Baba maganar karatunka, ya amince kake zuwa gidan nan shi da kansa zai koya maka karatun Alkur’ani da duk littattafan addini” yace “WOW my Sweet Sumayya lallai wannan babban albishir ne kika yi min. Nagode Nagode” tace “nima na gode da ka amince cewa zaka ke zuwa ɗin” yace “kinga duk abinda ban gane ba sai in kira ki kizo ki kara min bayani ko?” Tace “no. Babu ruwana. Baba yayi fadan cewa nayi saurayi ban sanar a gida ba. Ruqayyah ce ta gaya masa abinda yake tsakanin mu” yace “to menene a tsakanin mu ɗin” tayi shiru, yace “ki fada min mana inji. So nake ki fada da bakin ki” tace “nima bansan sunan abin ba” yace “in gaya miki?” Tace “ina jin ka” yace “it is called Love. Ni dai abinda nake feeling a raina kenan, ina ji a zuciya ta cewa ke na ke so, da ke nake so inyi tafiya cikin rayuwar duniya har zuwa karshenta. Dake kuma nake so in tashi a can muyi rayuwa wadda bata da karshe a aljanna” tace “ameen, Allah ya amsa” yace “to ke kuma fa? Fada min menene a zuciyarki” ta danyi murmushi tana nuna jin kunya duk da ba tare suke ba tace “nima haka” yace “ke ma me?” Tace “duk abinda kace, nima irinsa” yayi dariya yana jin yana kara sonta a ransa yace “ki fito ki bude baki kiyi magana, in ba haka ba ba zan fahimta ba” tace “to zan gaya maka wata rana” yace “wacce rana kenan?” Tace “nima ban sani ba” yace “to shikenan, zanzo gobe sai ki gaya min a kunnuwa na inji” tace “hold it. Baba yace in ya kara gani na tare da kai sai ya zane ni” ya bude ido zuciyarsa tana bugawa yace “what? Saboda me?” Ta danyi dariya tace “yace sai ka nemi izninsa tukunna. Sai ya yarda ka ke ganina sannan zaka cigaba da gani na” ya yi ajjiyar zuciya yace “yau zan tashi da dare inyi sallah in nemi Allah ya dora ni akan sa. Kar ki damu, in na samu yadda nake so a gurinsa I will show you love the Igbo way”.

Kamar yadda Adam ya fada, ranar sai da yayi sallar dare saboda samun courage da kuma neman nasarar fuskantar Baba. Ya nemi iznin Hussain, wanda yake ta shirye shiryen washegari zasu tashi zuwa honeymoon dinsu sannan ya tafi. Ya fada wa Sumayya ta sanar wa Baba da zuwansa da haka shima Baban bai fita ba ya zauna ya jira shi. Da yaje ya aika aka fadi cewa yazo, Zunnur ya fito yace ya shigo, yana ganin sa ya fahimci kanin su Sumayya ne, dakin su ya kai shi sannan ya gaishe shi ya amsa yana tambayarsa sunansa. Sannan Zunnur ya koma cikin gida ya gaya wa Baba zuwan sa. Baba ya fito ya same shi a dakin.

Adam ya mike tsaye saboda jin shigowar Baba, kansa a kasa, sai da Baban ya zauna sannan shima ya zauna a kasa, Baba ya miko mada hannu amma sai ya ki bashi nasa hannun sannan ya durkusa ya gaishe shi. Duk wannan yayi practicing tun safe, zamansa da hausawa ya saka ya koyi dabiun su da abinda yake dai dai da abinda yake akasin haka a gurin su.

Baba yace “Husaina tace min kana so kayi karatu tare damu hakane?” Adam yace “haka ne Baba. Ina son yin karatu saboda ni… Saboda ni….” Baba yace “ta gaya min ko kai waye. Shi yasa nace kazo kayi karatun, zamu baka baka ilimi dai dai iyakacin abinda Allah ya bamu. Naji tace kana aiki, nima ina yi, dan haka zamu tsayar da lokaci wanda zamuke yin karatun” Adam yace “Nagode Baba, nagode sosai”

Baba ya cigaba da kallon shi, yana nazarin sa yayin da shi kuma Adam din yake ta lissafin ta yadda zai shigo da maganar Sumayya. Yana kuma jin idon Baba akan sa kamar Baba yana jiran ya fadi wata magana. Sai yace “kuma Baba, dama Sumayya tace in gaya maka…..” Baba yace ” Sumayya ce tace ka gaya min ko kuma kai ne kake so ka gaya min?” Adam yayi saurin gyara wa. “Nine, ba Sumayya bace nine nake so in tambayeka dama in ka amince….. In ka yarda….. Ina so….dama Sumayya……” Baba yace “kana so zaka nemi auren Sumayya” Adam yace “eh Baba. Haka nake so in ce” Baba yace “me yasa kake neman auren Sumayya?” Adam bai yi in ina anan ba, yasan amsar direct ya fada “saboda ina son ta Baba” Baba yace “saboda me yasa kake sonta” anan sai Adam yayi murmushi, yasan wannan amsar itama. “Saboda kyawun halayyar ta Baba” ya tuno ranar daya fara haduwa da yan biyun a mota, yadda Ruqayyah tayi niyyar damfarar sa Naira hamsin har kuma tana yiwa Sumayyan warning akan kar ta tona mata asiri, tana so su had kansu suyi masa karya idan kuma yaki yarda suyi masa ihu su yi masa sharri, duk akan naira hamsin, amma Sumayya ta zabe shi, inyamurin direban taxi akan twin sister dinta. Ya sake maimaita wa “saboda kyawun halinta Baba” Baba yayi murmushi yace “kayi gaskiya, Sumayya tana da hali mai kyau, kuma ina son ya cigaba da zama a haka. Bana son ka zama dalilin chnazawar ta dai dai da kwayar zarra ne. Allah yayi muku albarka”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button