TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari da sassafe jirgi ya tashi da tagwayen maza tare da amaren su zuwa yawon cin amarcin su inda zasu fara ta Amalfi Coast, Italy. Kannen su gaba daya sunzo rakiyar su har Hassana da bata gidan, suna gab da tashi sai ga Adam ya kawo Sumayya, Sulaiman da Zunnur, suma sun zo yiwa yar uwarsu sallama. Kallo daya Ruqayyah tayi masa ta dauke kanta ta je gurin yan uwanta. Sai da jirginsu ya tashi sannan ya rakiyar tasu kowa ya kama gabansa.
Wannan littafin na siyarwa ne, duk wadda take so tayi mini magana through WhatsApp 08067081020Pregnant
The titles are back. Just because I love you alot.
Not edited please.
A cikin wata guda da suka yi a honeymoon dinsu, abubuwa da dama sun faru, na farko dai a wannan lokacin ne idanun Ruqayyah suka bude, a wannan tafiyar ne tasan kiyasin how much Hussain is really worth. Kudin data kiyasta kuma ba kadan bane ba, ta lura da duk inda suka je da mutanen da suka hadu dasu da kuma irin girman da mutanen suke bashi. Sunansa yaje inda ita bata taba zato ba. Irin hotels din da suke zama kadai ko a cikin mutanen kasashen ba kowa ne yake zama a irin wadannan gurin ba. Irin guraren da zata iya kira da aljannar duniya dan ita in tana lissafin aljanna a ranta irin haka take hasko wa. Duk kuma kalar dakin da Hussain ya kama musu shida Fatima to irinsa yake kamawa Hassan da Ruqayyah, daga nan kuma kowa zai shiga harkokin sa babu wanda zai takurawa wani sai dare sannan zasu hadu suyi dinner tare suyi maganganun su shikenan kuma kowa sai ya kama gabansa. Amma duk da haka Fatima sai da tayi kokarin ganin ta cika alkawarin ta, kullum takan ware wasu lokuta a cikin lokutan mijinta ta zauna da Ruqayyah. Kullum da akwai darasin da suke yi, tun daga kan kwalliya, dresssing, passion trend, tafiya, zama, magana da kuma harkar kula da miji musamman a gado. Da farko Ruqayyah taki bata hadin kai, tana ganin kamar wata hanya ce ta dauko dan ta kaskantar da ita amma daga baya bayan tayi waya da Minal sai ta fahimci wannan hanya ce da zata shiga gari itama. Tasan Fatima karshe ce a abubuwa da dama, dan haka in ta kiya daga gare ta kuma ta yi koyi da ita to kuwa tabbas in vata zama kamarta ba to kuwa zata zama a kusa da ita. Dan haka ta zage dantse ta bude kunnuwanta da kwakwalwar ta take koyon duk abinda Fatima take koya mata sannan tana lura da ita ta a kwaikwayon yadda take duk wani abinta. Amma ko sau daya bata taba gayawa Hassan abinda suke yi tare da Fatima in suka kebe ba. Daya tambayeta sai tace “hira ce kawai muke yi. Kullum labarin gidan sarauta da sarakuna kamar bansan xewa daga can take ba, ni na gaji wallahi. Bana so dai in daina zuwa kar taga kamar wani abu ne” shima kuma Hassan bai hana ta ba, saboda a lokacin ne yake samun personal time dinsa ya dan gudanar da wasu ayyukan office din ko kuma suyi maganar aiki shi da Hussain, musamman maganar da ta shafi bikin bude kamfanin da za’a yi da zarar sun koma Nigeria.
Amma duk wannan abin Ruqayyah tana lura kuma tana sane da Hussain, ta lura baya kula ta amma idanuwansa yana kan ta, kamar wanda yake studying dinta, kamar wanda yake so ya kama ta da wani laifi. Sai dai ko da wasa bata taba barinshi ya kama ta da laifin ba, in tana gabansa tana jin kamar dalibi marar gaskiyar da yake gaban principal. Wannan yasa bata enjoying dinner din da suke yi tare duk kuwa da cewa abinci ne irin wadanda bata taba tunanin akwai abinci irin su a duniya ba.
Bayan sunyi sati daya a Amalfi coast, Italy, sai suka tafi Austin, Texas daga nan sai Islands din Maldives sannan Bali a Indonesiya Anan ne Fatima tayi suggesting aje a duba lafiyar Ruqayyah, dama tun zuwansu take lura da ita musamman wayan kwadayin da taga tana dashi, da farko ta dauka saboda bata saba wadannan ciye ciyen ba amma sai daga baya ta lura da cewa yafi karfin haka. Bata taba zama bata cin wani abu, jikinta ya murje sosai tayi kiba da fari, sannan kirjinta sun kara girma kamar ana hura musu aska. Girman kirjin ya saka Fatima tace akai ta asibiti. “Ruqayyah ki shirya gobe muje asibiti a duba ki” Ruqayyah ta bude ido kwakwalwar ta tana zama alert, wannan matar me take nufi? Kar dai wani salon yaudarar zata fito dashi. Tace “asibiti kuma? Dama an taba kai mai lafiya asibiti? Ni na dauka marar lafiya ne yake zuwa asibiti?” Fatima tayi murmushi tace “Ruqayyah, wani tunani nake yi a kanki amma ban tabbatar ba. Gani nake anya ba karuwa zamu samu a gurin ki ba?” Ruqayyah ta bata fuska. “Ban gane karuwa ba? Wacce irin karuwa kuma?” Fatima tayi dariya tana tabbatar wa yarintar Ruqayyah ta wuce duk inda take tunani tace “ina zargin kina da ciki Ruqayyah, amma ni ba likita bace ba dan haka ban tabbatar ba. Shi yasa nake so muje asibiti a tabbatar min da cewa na kusa zama aunty” ta karasa maganar excitedly. Ruqayyah taji gabanta ya fadi, tsoro ya kama ta, ta bude ido “ciki kuma? Ciki fa kike magana?” Ta shafa shafaffiyar marar ta, babu wani alamun ciki, tace “wai kina nufi ciki da za’a haifi baby? Ni Ruqayyah ce nayi ciki?” Fatima ta sake dariya tace “kina magana kamar wani abin gudu. Ciki agun matar aure ai abin so ne abin ayi celebrating ne. Kin san wani abu? Tun da muka baro Nigeria Mi Amour ba shi da magana sai ta so yake mu koma Nigeria da guzurin ciki, ta sake dariya tana tafa hannu ita kadai ta cigaba “ashe dai zamu koma da guzurin cikin amma ba’a jikin Fatima ba” Ruqayyah tana zaune still hannun ta akan cikin ta tana lissafin tunda aka yi bikin ta bata yi period ba, hawaye ya zubo mata tana jin kamar duniya ta ruguzo akanta. Anya bai yi sauri ba, anya rayuwar ta bata sauri da yawa?
Fatima ta bude ido ” kuka kuma? Ke da zamuyi murna kuma sai kiyi kuka? Kinga tashi zakiyi mu saci jiki mu tafi asibiti a tabbatar mana kinga shikenan sai mu shirya wa twins din mu surprise muyi musu albishir” ta mike tana juyi, “nasan zasu yi murna sosai nima kuma ina murna sosai”
Ruqayyah ta bita da kallo, ita bata ga abin murna anan ba. Shikenan yanzu haihuwa zata yi daga nan shikenan ta zama inna sai kuma ta tsufa? Tana kallon sauran mutane suna cin duniyar su da tsinke ita kuma tana faman renon yara? Anya kuwa hakan abu ne da zai yiwu? Maybe shi yasa Fatima take murna saboda taga hanyar da zata cigaba da taka ta.
Amma dai sai ta bi ta suka je asibitin, aka duba kuma aka tabbatar musu da ciki dan wata daya a jikin Ruqayyah, aka kuma tabbatar musu da abinda yake cikin yana cikin koshin lafiya. Fatima sai murna, Ruqayyah kuwa jikin ta yayi sanyi tana ta tambayar kanta dalilin da yasa tayi aure yanzu, ga Sumayya can a gida sanda suka yi waya tana gaya mata Baba ya siyo mata application form na jami’a. Sai kuma tayi tunanin rayuwar da take ciki yanzu, da bata yi auren ba da ko a mafarki imagination dinta ba zai zo nan gurin ba.
Fatima ce ta shirya yadda zasuyi surprising guys din, ta rubuta musu notes ta hada baki da chefs din inda zasu ci abincin dare tace kowa ayi attaching a desert dinsa. Suka je suka zauna suna cin abinci kamar kullum suna hirar su a hankali, wadda yawancin ta Hussain ne yake tsokanar Hassan ko kuma ya tsokani Fatima, barely Ruqayyah. Babu abinda ya chanja sai mood din Ruqayyah sam bata jin dadi ta rasa ta yadda zata karbi chanjin da yake tunkaro ta. Hassan ya tambaye ta “are you okay?” Time without number. Amsar da take bashi shine gyada kai, tare da kirkirar murmushi. Sai da dinner tazo karshe an kawo musu desert sannan suka ga takardun da aka yi attaching a jikin wani dan tsinke akayi musu shape din umbrella, a saman ta kowa an rubuta “read me” Hussain ya dago kai yana kallon Fatima, yana gani yasan aikin ta ne ya bude ido “menene a ciki?” Tayi dariya. “Ka karanta mana” ya girgiza kai “kin san bana son surprises ko? Dan Allah ki gaya min, abinda nake tunani ne? Kar in saka raina fa” ta gane me yake tunani, dan da safe ma sai da yayi mata maganar baby yana lissafin sunan da zasu saka idan sun samu. Tayi murmushi tana jin babu dadi a ranta, but hakan bai sa taji murnar da taje taya Hassan da Ruqayyah ta ragu daga ranta ba, tace “it is that, but not exactly that” ya sosa kansa, shi bai gane me take nufi ba, sai da yayi bismillah sannan ya cire takardar ya karanta. “Congratulations. You are going to be an uncle” sai kuma aka yi drawing baby yana chanyara kuka. Ya yar da takardar yana zaro ido baki bude yana kallon Hassan da har yanzu ya saka takardar sa a gaba yana kallo. “Wow, wow” Fatima tayi saurin rufe masa baki “kar ka gaya masa karka gaya masa Please” Hassan ya kalle ta sannan ya kalli Ruqayyah data sunkuyar da kanta kasa hannunta a saman marar ta, ya juya ya kalli Hussain da Fatima take zaune akan cinyarsa suna kallonsa suna dariya. Ya kuma kallon Ruqayyah yace “she is pregnant, isn’t she?” Shi duk ya dauka fatiman ce mai cikin saboda mood din Ruqayyah daya gani sai ya dauka kamar sha’awa take yi.