TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ruqayyah ta dago kai tana kallon sa tace “not her. Me! I am pregnant” Farin cikin data gani a idonsa bata taba tunanin zai yi irin haka ba. Ya mike yana jawo ta jikin sa yana jin kamar duk duniya babu wanda ya kai shi Sa’a dan a yanzu yana ganin he is the happiest person in the world. Sai kuma ya rasa wa zai rungume yaji dadi, Hussain ko Ruqayyah a karshe sai ya jawo su duk su biyun, Hussain a damansa Ruqayyah a hagunsa.

Celebrating sosai suka yi, ita ta rasa wadanne irin mutane ne su, ita ta dauka yan gayu masu kudi basa son haihuwa ballantana ace daga yin aure an samu ciki, amma ga wadannan su murna suke yi kamar babu gobe. Ita dai har yanzu bata ji murna a ranta ba. But mintuna kadan bayan sanar da maganar cikin Hussain yayi mata kyautar mota, exactly irin motar da yayi wa Fatima order, yanzu sai dai ya kara order a kawo biyu instead of daya. Sai a lokacin tayi tata murnar, tana ji kamar babu wanda ya kaita farin ciki a duniya. Wannan motar will be her first but wata rana ita ce zata yi kyautar mota irin wannan.

Daga nan kuma sai laulayi, wani na gaskiya wani kuma na karya. Duk kuma sai hankali ya dawo kanta, Hussain da bai cika kulata ba sai gashi har daki yake zuwa ya dubata. Ko da idonta ta kalli abu kuwa sai Hassan ya kawo mata shi. In ya kaso kuma sai tace bashi take so ba wani take so daban. Fatima kuma tayi ta shiga yanar gizo tana nemo hanyoyin kula da mai ciki, kiwon lafiyar ta da sauran su. Sai lessons dinsu ya koma akan renon ciki.

Daga Bali sai suka taho Egypt, ba wai dan yana cikin lissafin su ba sai dan Ruqayyah ta nuna tana son zuwa, nan ma satin su daya sannan suka karaso Nigeria bakunansu cike da labarin wannan babban daddadan al’amari daya tunkaro su.

Wannan kenan……….

A bangaren Adam tun da ya samu go ahead din zuwa karatu gurin Baba, gashi kuma wanda yake yiwa aiki yayi tafiya, sai ya kasance kusan kullum yana gidan su Sumayya, wasu ranakun ma har kwana yake yi. Sun karbe shi sosai, dan tun da ya bar gida bai taba jin homy feeling ba sai a gidan su Sumayya. Ba wai Baba ne kadai malamin sa ba, kusan kowa a gidan in ka ɗauke inna ade to duk malaman sa ne duk wanda ya gani available sai ya kura shi ya koya masa wani abu. Karatu yake yi sosai, kuma irin karatun nan with understanding dan duk abinda aka koya masa sai yayi tambaya akai, shi yasa Zunnur ya kan gudu yace “kai yaya tambaya ce da kai, nema kake ka kure ni” in yayi masa tambayar da ya kasa amsawa kuma sai ya tafi yaje ya tambayo Inna Ade sannan yazo ya bashi amsa. Sai da suka fara koyar dashi sannan suka fahimci cewa abinda ya riga ya sani a game da addini ko wani wanda aka haifa a cikin addinin bai san har haka ba. Babban abin da yake burge su dashi shine his willingness to learn, da zuciyarsa yake karatun ba wai kamar ace an tilasta wa mutum ba. Shi shine yake so, kamar yadda shine ya zabi addinin islama ba tare da wani ya tilasta masa ba.

Ana fara sayar da form din jami’a yaje ya siyo mudu shida Sumayya. Ya kawo mata da niyyar su cike a tare yaje yayi mudu submitting amma sai taki tace sai ta kai wa Baba kuma ta nemi izninsa kafin ta cike. Washegarin ranar ta samu Baba yana breakfast ta gaishe shi sannan ta ajiye masa takardar tace “Baba dama mun taba maganar karatu da Adam, to shine yaje zai siyo form dinsa sai ya siyo tare da ni. Jiya ya kawo min gashi” Baba ya dauka yana jujjuya takardun a hannunsa duk da baisan me aka rubuta a jiki ba yace “to Masha Allah, ya kyauta sosai. Nawa ne kudin?” Ta sunkuyar da kai tace “ban sani ba Baba, bai gaya min ba” yace “kyauta ya baki?” Tace “eh” yace “ki tambaye shi dai ki ji, babu abinda zai gagara insha Allah. Ku biyu ma nayi niyyar biya muku karatu, yanzu kuma cikin ikon Allah Hassana nauyin ta ya sauka daga kaina, ke kadai ce yanzu sai kuma kannen ki idan Allah ya kaimu nasu lokacin. Dama gida na da muka taso shi na siyar nayi wa Hassana gara, sauran kudin kuma na ajiye da niyyar zan yi amfani dasu gurin harkar karatunki” Sumayya tana ta murmushi har ya gama maganar tayi godiya sannan tace zata tambayi Adam kudin form din, duk da tasan ko ta tambaya ma ba fada zaiyi ba, watakila ma suyi fada akan hakan.

Baba ya kuma cewa “yanzu shi wannan din da aka siya shikenan an shiga makarantar kenan?” Tayi dariya tace “a’a baba, wannan in an siya za’a cike sai a mayar, kamar an fada wa masu makarantar cewa ana son shiga makarantar kenan, su kuma zadu duba suka wanda ya dace sai su kira mu suyi mana jarabawa irin wadda akayi muku sanda za’a dauke ku aiki, to sai mutum yaci sannan za’a ce ya je ya biya kufin makaranta, in ya biya shine ya zama dalibi kenan” Baba ya jinjina kai yace “ashe abin babba ne, babu komai, zamu hada su da Allah babu abinda zai gagareshi”

Daga nan ta dauka taje ta cike, Adam yana zuwa ta bashi shi kuma ya hada da nasa yaje ya kai musu. Suna waya da Ruqayyah kowa yana jin halin da kowa yake ciki, kusan kullum dai maganar ta bata wuce complain akan Fatima, tayi mata kaza tayi mata kaza, abubuwan da ita Sumayya take gani kamar kyautata wa ne amma yadda Ruqayyah take juya maganar sai du zama kamar wulakanta wa. Kullum kumain tayi mata complain din sai ta bata shawara. Shawara mai kyau amma ko ba’a gaya mata ba tasan shiga take ta wannan kunnen tana fita ta wancan, sai dai ita ba zata gaji ba, ba zata taba daina bata shawara ba.

Ranar nan kawai sai ga wayar Ruqayyah tana kuka tana gaya mata wai ciki ne da ita, ita bata ga abin kuka a cikin wannan labarin mai dadi ba, amma yar uwar tata kuka take yi tana ganin ba lokacin daya kamata tayi ciki bane ba. Sai Sumayya ta samu kanta da tambayar kanta wai menene ubangiji zai bawa Ruqayyah wanda zata gode masa? Sai taji tana jin tsoron sanin amsar.

Ranar da su Ruqayyah zasu dawo suma su Sumayya sunje taryen su, ta kuma ji dadin yadda taga yar uwarta sosai da sosai. Ba ita kadai ba, duk wanda yaje gurin sai da yayi mamakin irin chanjawar da Ruqayyah tayi, masu hankalin cikinsu a take suka fahimci yanayin da Ruqayyah take ciki kuma duk sunyi murna musamman Aunty saboda wannan shine jika na farko da za’a haifar mata. A gida jen su ma an gama duk shirye shiryen taryen su, an shirya musu abinciccika iri iri musamman traditional food saboda an san sunyi missing din su. Amma Ruqayyah tana fara ci ta tashi, an ya kuwa zata iya cigaba da cin irin wadannan kalar abincin? Bata jima a part din Aunty ba tayi musu sallama tace zata je ta kwanta saboda bata jin dadin jikinta. Sumayya wadda ta biyo ta gidan ta da niyyar suyi kwana biyu tare suyi hirar yaushe gamo ta tashi itama tayi musu sallama, duk da cewa abincin bai ishe ta ba. Bayan sunje part dinta sun zauna tace “WOW Rukee kima ganin kanki a madubi kuwa? I mean kinga girman da kika yi kuwa?” Ruqayyah ta juya idonta tace “haka kullum mijina yake cewa, shi cewa yayi ma anya kuwa in kika ganni zaki gane ni?” Sumayya tayi dariya tace “shima wasa yake yi. Ni kuma ba girma kika yi ba ko ma me kika yi babu abinda zai saka in kasa gane ki” Ruqayyah ta tabe baki tace “Allah yasa to..yadda na fara cikin nan da wuri kar inne in tsofe da wuri ke kuma kina yammatancin ki ninkuma yayi na ya wuce” Sumayya tayi dariya tace “yayin ki ya wuce a gurin wa? Ba dai a gurin mu mu yan uwanki ba ba kuma a gurin mijin ki ba. Dan yadda naga yana ta rawar kafa a kanki nasan cikin nan ne ya kara masa sonki haka, in dan ta tashi ne nasan duk shekara sai kun haihu” Ruqayyah ta zaro ido “ba dai dani Ruqayyan zai haiho ba ko? Dan ni in nayi wannan gaskiya zan jima ban kuma yin wani ba” Sumayya tace “lallai baki da wayo. Ai masu son kama mazan su musamman maza masu son yaya to da yayan suke kama su, ki haifar masa yaya da yawa Ruqayyah yadda babu yadda zaiyi dake” Ruqayyah tayi shiru tana kallon yar uwarta, akwai wani abu a cikin maganar ta da yayi calling attention dinta amma ta kasa gane menene, har suka rabu kowa ya tafi gurin kwanciyar sa bata fahimci menene abin ba, ta hada ruwan wanka ta shiga tana yi, a lokacin ne maganar ta fado mata. “Da yaya ake kama gida” a sanin ta babu wani jika a gidan nan, sai wanda yake cikinta, dan da yake cikinta kuma dan Hassan ne dan haka nephew din Hussain ne. Yanzu idan ta hayayyafa da yawa kuma ta samu maza a cikin yayanta, and if something bad is to happen to Hussain, then H and H zai zama na Hassan and if something bad is to happen to Hassan then H and H zai zama nata ita da yayanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button