TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai da suka yi musu sallama suka tafi sannan cikin sassanyar muryarta tace “welcome, Mi Amour” bai amsa ba, tace “kayi kyau sosai” ya cire hularsa ya shafa gashin kansa sannan ya mayar da hular yace “kyau, in kina guri Fatima har ana iya ambatar wata kalma wai ita kyau?” Ta wuce shi tana bade shi da kamshinta ta zauna a edge din 3 sitter, ya zagayo shima ya zauna a dayan edge din sannan ta gaishe shi ya amsa ba tare da ya dauke idonsa daga kanta ba. Tace “to ka gama kallon nawa in tashi in zuba maka abinci?” Ya sake shafa kai yana murmushi, ba ya gajiya da kallonta, in dai tana guri to idonsa baya ganin komai sai fuskarta, duk sauran abubuwan da suke gurin suna yi masa duhu ne.

Ta tashi ta jawo table gabansa sannan ta dauko dan madaidaicin bowl ta bude wani food warmer ta zubo masa farfesun naman ragon da tayi masa ta ajiye akan table din sannan tace “kaci wannan da duminsa zaka ji dadinsa” sai kuma ta bude wani ta zuba masa wainar shinkafa ta ajiye kusa da naman sannan ta jawo wani madaidaicin tray da akayi wrapping da foil paper ta bude wani lafiyayyen potato pritata da yaji naman kaji da vegetables ta ajiye masa shima tare da jera masa knife da fork sannan da dauko mug tace “tea ko coffee?” Ya saki baki yana kallonta yace “duk wannan wai a ciki na zan saka su?” Ta langwabe kai tace “eh mana, in dai ba so kake duk wahalar dana tashi nasha a kitchen tun assuba ta tashi a abanza ba” ya ce “wai Fatima kina nufin ke kika yi wannan girkin da kanki” tace “to wa zan bawa tayi wa mijina abinci? Tea ko coffee?” ya jawo bowl din naman ya debi romon yayi tasting sannan yace “coffee please” ta hada masa tazo ta durkusa ta mika masa sannan ta koma gurin ta ta zauna tana kallonsa yana cin naman kamar zai hada har da hannunsa, ya juyo suka hada ido sai suka yi dariya a tare, yace “lallai sai nayi wa Hassan takeaway din naman nan, kin san shi kure ne” tayi murmushi tace “kace masa ya sha kurumin sa, duk sanda na shigo gidan sai yaci nama har ya ture” ya ajiye bowl din yana kallonta a ransa yana jin tamkar ya jawo watanni hudun da suke gabansu yace “Fatima, wallahi kinyi a rayuwa”

Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only

Sai na jiku….???????? TAGWAYE ????????

By

Maman Maama

Free Episode

Episode Five : Adam

A bakin kofar makarantar jeka ka dawo ta gwamnati ta yammata, tagwayen ne a tsaye suna jiran abin hawa.

“Kinga Sumayya, na gaya miki fa babu me napep din da zai dauke mu tun daga nan zuwa gida a naira hamsin, ai ba baban mu ne ya saya masa ba” Sumayya tace “kai Rukee, shekarar mu nawa muna tafiya gida daga nan a naira hamsin ɗin? Kullum ba goyo muke yi mu basu hamsin ɗin ba?” Ruqayyah ta fara tafiya tana barin bakin gate din tana cewa “a da kenan. Yanzu ƙatin ƙatin da mu zamu yi goyo? Ni wallahi na gaji ba zan iya da wannan abin kunyar ba, yanzu ni ina labor prefect kawai sai yara su ganni ina goyo a napep? Ke kina ganin hakan dai dai ne?” Sumayya tana bin ta a baya tace “to labor prefect, sai ki gaya mana yaya zamu yi? Hamsin din ce zata haifi wata hamsin ɗin ko kuma mune zamuyi aman wata hamsin ɗin” Ruqayyah ta ja hannuta suka yi sauri suka shige gaban wata taxi data tsaya a gaban makarantar da niyyar daukan dalibai. Wasu daliban duk suka shiga baya.

Sai da mai motar ya tayar ya fara tafiya sannan sumayya ta rada wa Ruqayyah “kudin mu fa ba zai kai ba, gwara mu gaya masa tun kafin muyi nisa in yaso ya karo wasu mu zauna tare, ko a cinyoyin mu mu dora su” Ruqayyah ta ture ta tana gyara zamanta tace “sai dai a dora miki a cinyarki ba dai a tawa cinyar ba. Bari kiji in gaya miki, hamsin din ma ni bani da niyyar bayarwa ajiye wa zanyi gobe in an bamu kudin motar sai mu hada da shi dan ya ishe mu” Sumayya tace “to shi wannan ta yaya zamu sallame shi?” Ruqayyah ta kalli driver din ta gefen ido sannan ta tabe baki tace da Sumayya “look at him, ba bahaushe bane ba. Dan haka duk baya jin abinda muke cewa. Muna zuwa gida sai mu nuna masa kamar mun yar da kudin a hanya bamu ganshi ba, sai mu bashi hakuri”

Sumayya ta leka ta bayan Ruqayyah ta kalli driver din. Saurayi ne daga ganin sa bai dade da gama secondary ba, that’s in yayi secondary din, kana ganin sa kasan ba bahaushe bane ba amma Sumayya ba zata iya tantance wanne yaren bane ba. Kuma a fuskarsa babu alamar cewa yana jin abinda suke cewa. Fari ne tas kuma jikinsa fes yake babu alamar wahalar duniya a tattare dashi dan haka daga gani kasan asarar naira dari ba zata dame shi sosai ba amma kuma a ranta tasan naira darin nan still hakkin sa ce, ta tuna da jerin waazin da Inna Ade take yi musu kullum akan cin haram, cin zali, daukan alhakin mutane, ballantana wannan bayan cin haram din ma kuma akwai karya, gaskiya zunubin yayi mata yawa.

Ta dawo da dubanta kan Ruqayyah tace “Rukee babu kyau fa, kinsan babu kyau” ta harare ta “to shehiya malama Sumayya. Sai ki zaba, ko dai ki karyata ni ki tona min asiri ni yaruwarki kuma har abada ba zan manta ba ko kuma ki yi shiru kici zalin inyamurin da ba kara ganin sa zaki yi ba a rayuwarki. Ai ina sane muka shigo motarsa, sai dana kalle shi sosai na zabe shi sannan muka shigo” Sumayya tace “to yanzu in ma mun gaya masa haka, what if yaki yarda yace sai mun biya shi kudinsa? Idan ya fara yi mana hayaniya fa a unguwa ya zamuyi dashi?” Ruqayyah tayi murmushi tace “da zarar naga ya fara kokarin daga murya zan zunduma ihu ince ya rike ni yana tattaba ni” ta kare maganar da murmushin mugunta a fuskarta.

Sumayya ta sunkuyar da kanta kasa tana kallon hannayen su da suke cikin na juna ita da Ruqayyah. Tasan Ruqayyah kusan fiye da Inna Ade data haife su, tasan kuma zata iya aikata abinda tace ɗin, but it is not right, in ta biye mata ita ma ta zama irinta kenan kuma kamar ta kara encouraging dinta kenan. A hankali ta zare hannunta daga cikin na Ruqayyah ta juya tana kallon titi.

Luckily sai da duk aka sauke sauran passengers din sannan aka zo bakin layin su Rukee. Suka nuna masa inda zai tsaya ya tsaya sannan ya juyo sosai yana kallonsu yace “your money please, 100 for the both of you”

Ruqayyah tayi pretending as if tana nemo kudi a jikinta, sai kuma ta hau duba jakarta tana da bincike, in ka kalli fuskarta zaka iya rantsewa da Allah cewa da gaske neman kudin take yi, sannan ta dago kai tana kallonsa da budaddun idanunta da suke nuna alamar tsoro tace “I can’t find it. I can’t find the money.” Ta sake shashshafa aljihunta sannan tace “I swear I put it inside my pocket. I must have lost it at school” ta langwabe kai “we are sorry sir. Please dash us the money”.

Sai ya dauke kansa gefe yace “check again. Maybe you hid it somewhere” sumayya ta juyo tana kallonta tace “Rukee ki bashi hamsin din, sai mu roke shi yayi hakuri in yaki yin hakurin sai inje gida in karbo masa a gurin Inna Ade” Ruqayyah ta harare ta tace “chafdi, wallahi ba za’a bashi din ba, so kike Inna Ade ta saka mu a gaba da nasiha”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button