TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan littafin na siyarwa ne, duk mai so tayi min magana ta hanyar WhatsApp ta wannan
Mr Careful
Hussain ya bi Hassan da Ruqayyah da kallo fuskarsa dauke da mixed emotions na shock da kuma tambayoyi kala-kala, har suka wuce shi suka fita suka bar kofa a bude, ya juya ya rufe kofar sannan ta juyo yana kallon fatima da take tsaye tana sheshshekar kuka. Tunda yake da ita tunda ya santa sama da shekaru hudu bai taba gani ko jinta tana kuka ba, bai san gaskiyar me ya faru a gurin ba amma sai yaji zuciyarsa tafi karkata gurin Fatima, yaji kukan ta har cikin ransa. Da sassarfa ya karasa inda take ta jawo ta jikinsa ya zagaye ta da hannayensa yana jin kukan ta yana karuwa. Bai lalllashe ta ba sai ya barta tayi kukan ta sosai ta gama. Tunda take a zata iya tuna ranar da aka yi mata tsawa ba, in ma an taba yi mata gaskiya bata sami ba ballantana hara akai ga daga mata hannu kuma akan laifin da bata san ta aikata ba. Ita da soyayya aka raine ta, im ma tayi laifi ana yi mata fada ne ta sigar lallashi da kuma nasiha, wani lokacin ma ba zata fahimci fada ake yi mata ba sai anyi mentioning laifin da tayi. Duka kuwa is totally out of the question, amma ita yau Hassan yake daga wa hannu, ta dauka marin ta zaiyi duk da cewa bata san me tayi ba, ya kuma kirawo ta da munafuka amma bata sam munafuncin me tayi masa ba, and above all yayi violating privacy dinta ya ganta a yana yin da in ba mijinta ba babu namijin da ya taba ganin ta haka a duniya, ko babanta, ko brothers din ta babu wanda yake shiga Bedroom dinta ballantana yaga tsiraicinta. Idan a waje ne kuwa ko gashin kanta babu wanda zai ce ya taba gani saboda yadda take adanawa da tattalin jikinta. Amma yau Hassan, yayan mijinta…….
Ta sani cewa tun kafin ta auri Hussain ta san cewa Hassan baya sonta, but ta dauka ya fara saukowa tunda taga suna Magana yanzu sosai har suyi wasa da dariya, menene ya chanja lokaci daya? Ta tuna abinda yace mata “stay away from my wife” to me tayi wa wife din tasa? Ita dai tasan babu abinda tayi wa Ruqayyah sai alkhairi, babu wani abinda yaje zuciyarta a game da Ruqayyah sai alkhairi. Me yayi zafi haka shi ba wuta ba?
Hussain ya fara jijjigata kamar baby yana cewa “shshsh, ya isa haka. Kar kiyi ciwon kai kuma Princess. Ya Isa haka” ta dago jajayen idanunta tana kallon sa tace “babu abinda nayi masa, wallahi babu abinda nayi masa” yayi kissing idanuwanta da goshinta yace “I know, I know. Zan same shi kinji? Zai gaya min dalilin da yasa yayi abinda yayi idan kuma bashi da dalili zan dauki mataki akansa. Ki daina kuka dan Allah” ta dan ture shi daga jikinta tana cewa “ka ga fa a yadda ya shigo ya ganni, in gurin matarsa yazo ba zai tsaya a pao ya aiko a kira ta ba? Ko kuma yayi mata waya ta fita? Ko kuma daya shigo ya ganni a haka ai sai ya koma ko? Sannan kuma ya ce min munafuka, munafuncin me nayi masa? Me nayi masa?” Ta sake saka kuka. Ya ji ransa ya kara baci, bai san me zai ce mata ya lallashe ta ba, bai san wanne kalami zaiyi amfani dasu wajen nuna mata bacin da ransa yayi akan abinda twin brother din nasa yayi ba. Sai kawai ya jawo ta ya hade bakin su guri daya, wannan ya tsayar da kukan da take yi sannan a hankali tayi relaxing jikinta ya saki. Ya sauke ta yabi ta siraran stairs din da zasu kai ka har kofar bedroom dinsa, ya kaita ya kwantar da ita a kan gado ya lullube ta sannan ya sauka da sauri, zuciyarsa tana kuna cike da kishin matarsa.
Part din Hassan ya dosa da sauri, ya bude kofa kuma sai ya tsaya yana kallon hoton Hassan din da yake rataye a gurin, his twin brother, ya kuma tuna da maganar Annabi Muhammad SAW da yayi hani da yanke hukunci a yayin da mutum yake cikin fushi. Sai kawai ya saki kofar ya koma da baya. Dama fita zaiyi ya shiga da niyyar ya sanar da Fatima cewa zai fita, bai ma san suna tare da Ruqayyah ba balle ya saka ran ganin Hassan. Dan haka motarsa ya dosa ya tarar Adam har ya tayar da ita ya shiga suka fita.
Hassan yana dauka Ruqayyah mota ya kaita, tana ta dan kuka kadan kadan hannunta akan marar ta ya zagaya ya kunna motar suka fita daga gidan “Allah sarki baby na, wallahi ina sonka kar ka tafi dan Allah” ya dan kara gudun motar yana jin ransa yana kara baci, in wani abi ya samu babyn sa ba yar sarkin kano ba ko yar sarkin macca ce Fatima sai jikinta ya gaya mata. Ta samu yarinya yar karama tana neman ta cuceta saboda bakin hali irin nata. Saboda tana mata bakin cikin ita ta samu ciki ita bata samu ba. Dama tun farko sai data gaya wa Hussain ya kuma ja masa kunne akan auren yarinyar nan saboda ta riga ta saba da samun duk abinda take nema and now she can’t stand ganin Ruqayyah da ciki ita babu. Tun kafin auren yayi nisa har ta fara nuna hali.
Suna zuwa asibiti aka karbi Ruqayyah aka shiga da ita, Hassan yana rike da hannun ta doctor ya gama duba ta yayi mata tambayoyi akan abinda take ji sai tace marar ta ce take mata ciwo, ya tambaye ta wanne irin ciwo sai tace “bazan iya yi maka bayani ba, ciwo dai sosai kamar zan mutu” doctor yayi murmushi yace “kar ki zama raguwa mana, in lokacin haihuwar yazo kuma ya za’a yi kenan? Kuma ba zaki mutu ba kinji?” Ya saka ta kwanta yayi mata scanning yana duba lafiyar cikin yace da Hassan “Babu wani problem da na gani gaskiya, duk babies din lafiya kalau suke mahaifar ma haka” Hassan yace “babies?” Doctor yace “eh fa, double gestation na gani. But zaku iya dawo wa after two weeks ku sake confirming, but am sure” Hassan ya bude baki cikin murna, yana jin duk fushin sa yana tafiya. Blessing often blessing. Allah ya na sonshi sosai babu abinda zaiyi masa sai godiya dan shi kam duk burikan sa na duniya suna ta cika.
Doctor din ya tambayi abinda yasa Ruqayyah ciwon marar sai Hassan yayi masa bayani kamar yadda Ruqayyah ta gaya masa, likitan duk ya gama dube dubensa bai ga problem ba amma sai yace su koma gida on bed rest, ta daina yin zirga zirga sosai ko daukan abi mai nauyi ko makamancin haka, amma zata iya yin normal tafiya just dai kar ta gajiyar da jikin ta sosai. Daga nan ya rubuta mata pain reliever da prenatal vitamins ya sallame su. Har suka dawo gida still tana kwance tana dan complain dama sama, har dakinta Hassan ya kaita ya kirawo Sumayya da sai a lokacin ta tashi daga bacci ya gaya mata abinda ya faru sannan ya fita da kansa ya siyo mata drugs din.
Hussain suna mota tare da Adam, abinda ya faru a gida yana ta yi masa yawo akai and even without bincike kawai zuciyarsa Ruqayyah take pointing at. Ita ce a tsakiya, duk abinda ya faru ta sani dan tana tare da Hassan kuma tana tare da Fatima. Ya tuno maganar da yaji Hassan ya fada wa Fatima “stay away from my wife” ya juya kansa, tabbas koma menene Ruqayyah is at the bottom of it. Yasan Hassan baya son Fatima amma bai kai har hakan ba, dan shi ya dauka ma wannan maganar ta wuce, to ko dai Ruqayyah tace da Hassan Fatima tayi mata wani abu ne? Gabansa ya fadi tunawa da yayi da cikin jikin Ruqayyah. Yes, that must be it. Cikin nan shi ya saka Hassan reacting the way he did. But me tace an yi mata? Dan shi har cikin zuciyarsa yasan Fatima ba zata yi harming pregnant woman intentionally ba, sai dai in a rashin sani. To ko sharri tayi mata?