TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya kalli Adam yana tunanin sake gwada sa’ar sa ko zai samu wani bayani a gurin Adam din. Yace “Adam, kana tunanin Ruqayyah is capable of sharri?” Sai yaji Adam ya danyi dariya yace “ohh dariya ma na baka?” Adam ya yi shiru yana kallon reflection din Hussain ta center mirror, yana yinsa yana nuna cewa he is serious. Adam yayi gyaran murya yace “sorry sir” Hussain ya kuma cewa “amana zan karbi maganar ka, nayi maka alkawarin ko Hassan bazan gaya wa ba balle wani. Ina so inji ne kawai for the mental health of my family” Adam ya saje yin shiru yana jujjuya maganar a ransa, sannan yace “ranar da na fara haduwa da Ruqayyah da Sumayya sharri Ruqayyah tayi niyyar yi min. Ta dauka bana jin hausa sai take shiryawa yar uwarta plan din yadda zasu damfare ni naira hamsin. Yar uwarta taki yarda kuma ta nuna mata rashin dacewar hakan. Bata ci nasara ba, wannan yasa har yau take jin haushina duk da cewa banyi mata laifin komai ba. Dan haka your answer is yes, Ruqayyah is capable of hada sharri” Hussain yayi shiru yana tunani sannan yace “kana ganin zata iya hada sharrin da zai raba aure? Ko ya raba yan uwa?” Adam ya girgiza kansa yace “ban sani ba sir, but ni sharrin data yi niyyar hada min irin wanda defending on my destiny zai iya sawa mutanen unguwarsu suyi min duka, ko kuma su kona min mota, ko kuma su hada dani da motar su kona, kowanne daga cikin wadannan zaibiya jawo rikicin tsakanin kabila wanda zai iya jawo asarar rayuka da dukiyoyin daruruwan mutane. So ina ganin haddasa husuma a tsakanin mutum biyu ba wani abu bane a gurin ta”.
Hussain ya koma ya zauna sosai yana kokarin digesting yadda zai bullowa maganar amma sai yaji ya kasa, Hassan yayi masa shield, sannan ga cikin da yake jikin Ruqayyah.
Sai yamma ya dawo gida, shima kuma ba wai dan ya gama abinda suke gabansa ba sai dan yana son yazo yaga halin da Fatima take ciki duk kuwa da cewa bayan kowacce awa yana kiranta, kuma daga muryar ta ya fahimci cewa ta daina kukan sai dai still akwai miki a ranta, mikin da dan uwansa ya dasa mata. A dining room din su ya sameta, ta cika masa shi da kayan abinci kamar yadda itama taci kwalliya kamar babu abinda ya faru. Ta tare shi tana zura hannunta cikin nasa. “Welcome Mi Amour. I made your favorite dises for you” kyawun fuskarta kadai ya saka shi yaji rabin damuwarsa ta tafi. Yayi murmushi yana kokarin kissing dinta, ta juya kanta gefe tana dariya “zaka bata min kyalliya ta tun kafin ka gama gani” ya juyo fuskar yana kare mata kallo sannan yace “na gama gani, can I kiss you now please?” Tayi dariya sannan ita tayi kissing dinsa da kanta, sai kuma ya hana ta janyewa sai da ya sake ta dan kansa sannan yace yana kallon ta idonsa cike da kaunarta “me yafi wannan dadi?” Tace “kiss din?” Yace “that included but ina nufin mutum ya dawo daga aiki ya tarar da kyakykyawar matar sa tayi masa kwalliya ta tare shi fuskarta da murmushi ga abinci ta jera masa, this is perfect, komai yayi dai dai my life is finally complete” ya bata fuska tace “complete? Tun yanzu? Tun kafin suzo?” Ya bude ido “ohhh kinga wannan kwalliyar taki ta saka ni na manta da babies dina ko? Wannan ko sunzo din in dai zaki cigaba da irin wannan kwalliyar to mantawa zan ke yi dasu” tace “hmmm really? Kai din kuwa? Duk ran da muka haihu a gidan nan ina jin ni kaina kaiyade min lokacin daukan jaririn zakayi” yace “kamar kin sani, dashi zan ke fita a mota, in bashi madara a office” suka yi dariya. Tace “to Baban baby, wanka ko abinci?” Yace “wanka ya kamata, but this food is so tempting har na kasa controlling appetite dina” ta sunkuyar ta dauko masa samosa guda daya a cikin wadanda ta jera da tayi arranging dinsu a shape din heart, a tsakiya kuma ta zuba tomato sauce din da tayi garnishing da vegetable. Ta saka masa a baki tace “kayi taste sai muje ayi wanka” ya cinye yace sai ta kara masa ta kara masa daya sannan ta jashi zuwa toilet yayi wanka, wanda rabi ita tayi masa dan cewa yake wai hannunsa baya kaiwa, anan aka karasa bata kwalliyar sannan suka fito suka shirya suka dawo gurin cin abinci, a nan kuma yayi ta hadama, komai sai yaci, ita dai tana tayi masa dariya tace idan tayi tumbi babu ruwanta.
Sai da suka gama cin abincin su, wanda akan cinyarsa taci nata, sannan yayi mata magana “Princess kiyi hakuri kinji? Akan maganar Hassan kiyi hakuri. Ba halin sa bane ba treating mutane that way ballantana ke da kike matata. Naso inyi masa magana dazu amma kuma raina ya baci sosai bana son in dora akan barnar ya shi ya riga yayi, na fi son in zanyi masa magana ya kasance maslaha ce zamuyi” ta gyada kai kanta a kasa tace “kar ka damu, dama na riga nasan baya sona tun kafin auren mu, amma bansan kiyayyar sa gare ni ta kai haka ba. Ka rabu dashi kawai, yace in rabu da matarsa ni kuma na barta har abada. Ba zance babu ni babu ita ba saboda matar dan uwanka ce ita sai dai bazan kuma nemanta ba sai dai in ita ce ta neme ni, bazan shiga gurin su ba but she is welcome to come here anytime. Shi kuma ka gaya masa kar ya kuma trying daga min hannu dan wata rana hannun sa zai iya gocewa ya same ni. Duk kanin mu kuma bama fatan haka ta kasance” Hussain ya girgiza kansa “I promise you Princess, hakan ba zata taba kasancewa ba kinji?” Ta danyi murmushi. Yace “zan je in ganshi in an jima. We will talk things out kinji?” Ta kuma gyada kai.
Hussain baya son ya shiga gidan Hassan suyi magana a can saboda bai son Ruqayyah ta shiga maganar su, ba kuma yaso taji mai zaice. Yasan kuma ko ya kira shi nashi part din ba zai zo ba dan haka ya tafi palon Aunty ya zauna, yasan duk dare yana shiga ya gaishe ta su danyi shawarwarin su. Dan haka ya kwanta akan kujera ya rufe idonsa yana jiransa. Ganin haka yasa aunty ta kora yammatan ta sama ita kuma ta zauna suna hirar dinner din da yake shiryawa ta family and friends na taya shi murnar bude sabon kamfanin sa, a lokacin yake gaya mata motocin da ya siya wa Fatima tare da Ruqayyah. Tayi murna kuma tayi masa godiya.
Sunanan a zaune Hassan ya shigo, ya kalli Hussain ya dauke kai ya gaishe da Aunty suka dan yi magana kadan sai ta tashi ta basu guri dan ta fahimci akwai dan tension a tsakanin su. Tunda basu saka ta a ciki ba kuma bata son ta saka kanta gwara ta barsu su warware kayan su. Tana tafiya Hussain yace “me Fatima tayi maka?” Hassan yace “wrong question, abinda ys kamata ka tambaya shine ‘me Fatima tayi wa Ruqayyah?” Hussain “as far as I know babu abinda tayi mata face kokarin taimaka mata” Hassan yace “okay haka ta gaya maka? Taimakon nata ne ya kai Ruqayyah asibiti? Ko baka san cewa she is now under bed rest ba? A saboda Fatima?” Hussain ya bata rai yace “ban gane ba, dukanta tace tayi ko me?” Hassan ya bashi labarin duk abinda Ruqayyah ta gaya masa, har da shawarar da tace Fatima ta bata na cewa ta zubar da ciki bata isa haihuwa ba.
Hussain ya bude baki yana mamaki. Ko a mafarki bai taba tsammanin Ruqayyah zata iya wannan mugun sharrin ba kamar yadda bai taba tsammanin Hassan zai yarda da wannan maganar ba. Tabbas da gaskiyar Adam da yace “he should be very worried” .
Yace “and you believe that bro?” Hassan ya daga kafada yace “what’s there not to believe? Kar ka manta Ruqayyah yarinya ce karama, only 18 years, bata san komai akan abinda duniya take ciki, I doubt it in tasan ma ana shan pills dan a zubar da ciki kamar yadda I so much don’t believe zata iya hada magana irin wannan ta fada” Hussain ya dafe kansa yace “and you believe Fatima zata iya yin abinda Ruqayyah tace tayi mata?” Hassan yace “sosai. Ta fita shekaru ta fita wayewa ta fita wayo da sanin duniya” Hussain ya gara zamansa yace “I dated Fatima for full four years kafin in aure ta, nasan 90 percent na halayen ta kuma nasan duk abinda ka fada na cewa tana da shekaru, wayewa, ilimi, wayo, dabara duk yes tana da su amma kuma hakan bai sa ta zama mai munanan halayya ba. Fatima tana da kirki fiye da yadda kake tunani, yes, tana da flows dinta kamar kowa amma ba zata taba cutar da mace mai ciki ba, ko a mafarki ba zata aikata haka ba. Duk da nasan ka sani, maybe wani abu ne yaje rufe maka idonka baka gani amma nasan kasan cewa age is just a number, halayyar mutum bata da alaka da shekarun sa ko background dinsa ko ilimin sa ko yanayin tarbiyyar da aka bashi, wadannan duk suna shaping halayyar mutum ne amma ainahin halayyar da ita ake haifar kowa. Shi yasa tagwaye suke tashi da mabanbantan halayya duk kuwa da cewa sun samu komai iri daya. Bance Ruqayyah bata da hali mai kyau ba amma ina tuna maka da cewa baka san ko da kashi daya cikin uku na halayyar ta ba saboda wata uku da sanin ta ka aure ta kuma ba…. “