TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Hassan ya daga masa hannu, “nasan cewa baka son Ruqayya, tunda ka fada min haka tun farko amma kar kayi kokarin tura laifi kanta saboda kana son ka kare matarka. Idan baka manta ba in tuna maka, Ruqayyah saved my life. Ta saka rayuwarta a danger saboda tana son ta kubutar da rayuwar wanda bata taba gani ba a lokacin daga danger. She could have lost her life a ranar nan saboda ni. Wannan kadai shi ya nuna min kyawun halayyar ta. Babu wanda zai aikata abinda ta aikata sai mutumin da bashi da son kansa, mutum wanda duniya bata gabansa, mutum mai kyakykyawar zuciya wanda ba zai iya harming wani ba, mutum…. ” Hussain ya daga masa hannu yace “kasan wani abu bro? Tun ranar da Allah ya dawo min da kai gida ranar daka bani labarin taimakon da Ruqayyah tayi maka da kuma hanyar da tabi gurin taimaka maka din, tun a lokacin naji bata kwanta min arai ba amma ban taba sanin dalilin da yasa hakan ba sai yanzu da kake wannan maganar. Yes she helped you and I am very grateful for that. Amma inda matsalar take shine hanyar da tabi wajen taimaka maka din. In reality, idan yarinya karama kamarta wadda bata san komai na duniya ba mai bla bla bla ta shiga toilet taga mutum cikin jini yana neman taimako abinda ya kamata tayi shine taje ta taso mahaifanta ta nuna musu shi su taimaka masa, but Ruqayyah sai ta kama katanga ta haura ta fita. Taje ta yaudari manyan matured top criminals har ta dalilin ta police suka kama su. Ta haka musu rami suka rufta ciki. If her brain can work out that plan a cikin mintuna kadan Allah ne kadai yasan abinda brain dinta take shirya mata a yanzu. In dai zata iya yaudarar criminals kamar wadannan in minutes ka gaya min dalilin da zai sa ba zata iya yaudarar ka ba. Ka gaya min idan har sun fada ramin data gina a cikin mintuna kai me yasa ba zaka iya fadawa ramin da take kwana take wuni tana gina maka ba?”
Hassan ya mike “ya ishe ka, ya ishe ka. My God, matata fa kake magana akai. Uwar yaya na” Hussain ya mike yace “wannan shine abinda yake rufe maka ido, ina fatan kuma ba zai makantar da kai nan gaba ba” Hassan yayi hanyar fita da sauri, Hussain yace “hey bro” ya juyo yana kallon sa bai ce komai ba, Hussain yace “Please in ka hadu da Mr Careful ka gaya masa ina bukatar taimakon sa. Cos you are no longer him”.
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kina so kiyi min magana ta WhatsApp 08067081020My Better Half
A palo Hassan ya tarar da Ruqayyah da Sumayya suna ta hira suna dariya, suka yi masa sannu da zuwa ya amsa musu sama sama ya wuce dakinsa, Ruqayyah tabi bayansa da kallo sannan ta tabe baki tace “mutum yayi ta kumbura shi kadai kamar ana saka masa yeast? Ni wannan ban san wanne irin mutum Allah ya hada ni dashi ba” Sumayya tace “ko ma dai menene dai mijinki ne shi, kuma mijinki ya dawo gida kamata yayi ki tashi ki bishi in yaso ko ma menene yake damunsa sai kiji daga can” Ruqayyah tace “ke ni fa ba zan iya da wannan fushin nasa ba, sai inje inyi ta faman lallashinsa kamar wani jariri bayan ni ba dani yayi fadan sa ba?” Ta koma ta kwanta tace “shi da dan uwansa ne, babu ruwana ni ai ance babu kyau shiga tsakanin yan uwa. Suje su kare kalau” Sumayya ta zauna tana nazarinta tace “ya akayi kika san shida dan uwansa ne? Anya kuwa kina da gaskiya Rukayya? An ya bake kika hada su ba?” Ruqayyah ta ajiye wayar hannun ta tace “ke fa kullum kamar ba nice yar uwarki ba ba kya kyautata min zato wallahi. Ni bani na hada su ba, ni ba dashi naso in hada su ba Allah ne kawai ya kawo Hussain din ya shiga maganar”.
Sumayya tayi shiru tana nazarin ta sannan tace “gaya min gaskiya Ruqayyah, menene gaskiyar abinda ya faru dazu?” Ruqayyah ta kalle ta, tunda suke bata taba boye mata kaifi idan tayi duk kuwa da tasan cewa zata yi mata fada amma yanzu anya zata gaya mata plans dinta, na farko tasan ba zata goyi bayanta ba kamar kullum, na biyu kuma yanzu bata yarda da amanar ta ba musamman saboda wannan inyamurin drivern da take ta faman yashe wa baki a waya. She can’t risk her telling him.
Ta girgiza kanta “in na gaya miki gaskiya ma babu abinda zaki yi akai” Sumayya tace “dazu babu abinda ya same ki kika saka Hassan ya kai ki asibiti ko?” Ruqayyah ta juya idonta tace “idan na yi miki bayani ma ba zaki
gane ba, Please just let me be okay? Ni da wadannan tambayoyin naki ma gwara inje in rarrashi jariri na” ta mike da sauri ta tafi dakin Hassan. Sumayya tace “ki bi a hankali fa, ko kin manta doctor yace ki ke bi a hankali?” Ruqayyah ta juyo ta harare ta ta shige, Sumayya ta sauke ajjiyar zuciya a hankali tace “what are you up to sister?”
Hassan yana shiga dakinsa kofar valcony ya bude ya shiga, ya ja kujera ya zauna ya harde hannayensa a kirjinsa yana ta lissafin maganganun Hussain a ransa, amma kuma ya kasa fitar da ma’anar maganar, ya kasa tsayawa a guri daya yayi tunanin. Idan kwakwalwar sa ta jashi nan sai kuma zuciyarsa ta jashi can. A haka yaji shigowar Ruqayyah dakinsa. Ta tsaya tana kallon kofar valcony din tasan yana can amma ita har ga Allah bata son zuwa can din saboda bata son ganin gidan Hussain. Ita in tana cikin gidan mantawa take yi da gidan Hussain saboda babu ta inda take hango shi sai ta valcony din nan kuma in taga gidan ji take yi ya tsaya mata a ranta har hana ta numfashi mai kyau yake yi dan haka bata son ma ganin sa, at least not now, sai ranar da ganin gidan zai faranta mata ba wai bakanta mata ba. Sai ranar da zata kira gidan da nata.
Ta shiga tana lura da yadda bai dago kai ya kalle ta ba. Sai ta jawo kujerar da take facing dinsa wadda kuma ta juya wa gidan Hussain baya ta zauna tana kallon fuskarsa tana lura da irin tension din da take hangowa a can. Tace “Allah dai yasa lafiya kake mijina. Naga kamar baka jin dadi” ya dan kalle ta kadan yana tuno maganganun Hussain a kanta yace “lafiya ta kalau Precious, ki je kuyi hirar ku, in kina jin bacci kije kiyi kwanciyar ki ni anan zan kwana yau” ta marairaice fuska “haba dan Allah, bayan kasan bani da lafiya, bayan kasan bazan iya kwanciya babu kai ba shine zaka ce anan zaka kwana?” Ya dora hannunsa akan nata yace “kiyi hakuri Precious. Ina so zan danyi tunani ne shi yasa bana son yawan magana kinji” ta bishi da kallo a ranta tana dariyar yadda yake mata magana kamar wata karamar yarinya, sai ta gyara zamanta “ni ba zan tafi ba, nayi alkawarin ba zan ke yi maka magana ba amma nafi son in zauna a kusa da kai, kaji? Please? Nafi son kayi ta kallona kana tunanin” yaso yayi mata murmushi amma sai ya kasa, ransa yayi baccin da ba zai iya murmushi ba, ya gyara kujerar sa yadda zai ke kallon gefe sannan yayi shiru, yana ta so ya hada kyakykyawar innocent fuskar Ruqayyah da maganganun Hussain amma ya kasa, sam ba suyi kama da juna ba musamman in aka yi la’akari da gidan da Ruqayyah ta fito. Gidan malamai ne gidan tarbiyya ne.
Da safe Sumayya ce ta hada musu breakfast din soyayyen dankali da wainar kwai sai tea. Amma sai taki zama a dining din ta debi nata ta tafi daki tana ci a can. Hassan da Ruqayyah kuma suka zauna suna cin nasu anan. Suna cikin ci ya dago kai unexpected yace mata “Fatima ta musa duk abinda kika ce tayi miki, tace da Hussain sharri kika yi mata” ya tsaya yana nazarin expression din fuskarta, ga mamakin sa sai ya ga babu wani shock ko wani tsoro mai nuna rashin gaskiya kawai blank ne. Yace “me zaki ce akan hakan?” Sai yaga tayi murmushi sannan tace “wai kana expecting zata karbi laifinta ne? Dama ai cewa zata yi bata yi ba, duk hanyar da zata bi ta tsara mijinta ya yarda da ita ta kuma nuna masa nice marar gaskiya dole sai ta bita. Amma ni ina ruwana in ma mijinta bai yarda da ni ba? Ni dai tunda nawa mijin ya yarda dani ai shikenan ko?” Ta karasa tana kamo hannunsa ta rike tare da langwabe kai, yayi mata murmushi, exactly, tabbas duk abinda Hussain ya fada Fatima ce ta tsara masa, zata iya tsara masa komai dan ta kare kanta. To ma banda abin Hussain ribar me Ruqayyah zata samu idan ta yi wa Fatima sharri? It is not as if miji daya suke aure ballantana ace kishiyoyin juna ne. Sai kuma wani bari na zuciyarsa ya tambaye shi “to menene ribar da Fatima zata samu idan ta zubar da cikin Ruqayyah?”