TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana gama wa ya shirya ya fita sai Ruqayyah ta shirya itama tace Sumayya tazo ta raka ta gidan Hussain. Sumayya ta shirya ta bita dama tana ta so ta shiga gidan ta kashe kwarkwatar idonta. Ai kuwa tun daga bakin kofa ta fara kashe wa “wow. Ruqayyah haka gidan nan ya hadu dama?” Ruqayyah tayi tsaki, komai akayi da jaki sai yaci kara dama. Bata jira yan aikin gidan sunyi mata iso ba kawai ta kama hawan bene zuwa sama. Sai data je karshen benen kuma sannan ta rasa inda zata yi taga wadansu benayen daya yayi hagu daya yayi dama ga kuma kofofi nan ta ko ina. Dole ta nemo yarinya daya ta tambayeta inda matar gidan take, sai yarinyar ta bude mata wani guri tace su shiga bara ta kirawo ta. Suna shiga suka ga daki ne kawai da akayi masa ado da tsarin sarauta, in kana ciki zaka ke jinka kamar a gidan wani sarkin kake, anyi masa irin zanen jikin bangon nan na sarakuna sannan babu kujeru a ciki sai tintin da aka jejjera a ko ina ga lallausan carpet ga kuma lallausan kamshi. Suka zauna suna bin dakin da kallo Ruqayyah tana aiyanawa a ranta cewa ko gidan ya zama nata ba zata chanza tsarin wannan dakin ba.
Sun jima a zaune, sannan fatima ta shigo amma bata kofar da suka shigo ba, su bama su lura da kofa a gurin data shigo ba sai kawai ganin ta suka yi ta shigo din. Fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna a saman tintin daya ta harde kafafuwan wa irin na sarakuna sannan tace “sannun ku da zuwa, kuyi min uzuri na barku kuna jira, ina wasu aiyuka ne a lokacin da kuka shigo” Ruqayyah ta tabe baki, wai aiyuka, ko ita tunda tazo gidan hatta Bedroom dinta share mata ake yi, na Hassan kuwa bata san sanda ake gyara shi ba kuma bata san waye yake gyara shi ba kawai dai tana ganinsa a gyare. Sai ta kirkiro murmushi tace “babu komai wallahi, dama zuwa nayi in baki hakuri akan abinda ya faru jiya, dan nima kaina ba zan iya cewa mai ya faru ba wallahi. Dama tun da akayi bikin mu yana ta cewa baya son in ke shiga harkar ki waye da waye, to amma ban dauka zai dauki zafi irin haka ba. Na san baki ji dadin abinda yayi miki ba amma dan Allah ina bada hakuri on his behalf” Fatima ta bita da kallo tana studying dinta, ta saba da zama da mutane iri iri a gidan su tana kuma kyautatawa kowa zato har sai ya bata rawar sa da tsalle sannan sai tayi placing dinsa a inda ya dace, and right now ta yi placing Ruqayyah a dai dai inda ya dace da ita. Sai kuma tayi murmushi tace “it is okay, ya wuce. Zaman Hussain nake yi bana Hassan ba, duk wani abinda Hassan zaiyi tunani a kaina duk kuma wani abinda Hassan zai yarda dashi a kaina bazan damu ba saboda nasan Hussain ya sanni ya kuma san halina, yasan abinda zanyi da kuma abinda ba zanyi ba. Wannan shine abinda na damu dashi kuma na riga na samu, saura Hassan. Ba zance ba damu da abinda Hassan yake tunani a kaina ba saboda shi Hassan wani sashi ne mai girma na jikin Hussain kamar yadda Hussain yake sashe mai girma na jikina. Ba’a taba raba hanta da jini. Da sannu shima Hassan zai fahimci wacece ni kuma lamura zasu dai-dai ta a tsakanin mu. Kamar yadda na gaya wa Hussain, you are always welcome zaki iya shigowa gidan nan a duk sanda kika ga dama kuma kiyi abinda kike so ki ci arziki ki bar arziki a inda yake. Nima kuma duk sanda kike bukatar wani abu a gurina Please don’t hesitate to ask, tun daga kudi zuwa shawara zuwa a listening ear duk zan baki”. Ta mike tsaye tana duba kyakykyawan agogon hannun ta tace “lokacin shiga kitchen yayi, kuyi min afuwa” har ta kai bakin kofar data shigo sai ta juyo tace “Sumayya in kin je gida ki gaishe min da Inna da sauran yan uwa” Sumayya tayi mata murmushi tace “zasu ji. Insha Allah”.
Kafin Sumayya ta sauko daga dogon benen har Ruqayyah ta kai gida, bata taba jin ranta ya baci irin na yau ba. A palon ta Sumayya ta same ta tana ta safa da marwa, Sumayya tace “kiyi hankali fa, kin manta likita ya baki bedrest?” Ta jefa mata harara tare da tsaki a hade, tana jin kamar ta hada da ita da likitan da kuma Fatima ta babbaka musu wuta. Ta fara masifa “kutumar…ni matar nan zata zauna ta gaya wa maganganu har haka? Lallai ba ta san wacece Rukee ba tana kuma gab da sani wallahi. Wallahi sai tayi nadamar hada hanya dani” Sumayya ta saki baki “magana? Wacce magana ta gaya miki? Ni dai banji ba, kinje kin bata hakuri kuma tace ta yafe miki shine maganar? Ko kuma cewa da tayi mijin rabin jikinta ne shine maganar” Ruqayyah ta juyo kanta “baki ki ta ba? Baki ji ba wai har da wani cewa inje inci arziki in bar arziki a inda yake?” Sumayya tayi dariya tace “salon magana ne fa kawai. To in kika je gidan aka baki wani abu ba arziki aka baki ba? Kuma dole dai in kika fito kin bar sauran arziki a gidan. Ni banga abin tada jijiyoyin wuya a nan ba” Ruqayyah ta rike kugu tace “dama ai ke ba zaki gani ba, tunda ke din ba sosai idanuwan ki da kunnuwan ki suke miki amfani ba. Ki kuwa naji kuma na gani kuma sai na rama. Tana so ta nuna min wato ban isa in hada ta da mijin ta ba ko? To mu zuba mu gani. Ita ce a tsaye a gurin da nake bukatar tsayawa dan haka dole ko tana so ko bata so dole ta matsa ta bani guri” Sumayya tace “guri? Wanne gurin kike magana akai Ruqayyah? Ji nake ke da ita kowa mijinsa daban, dan haka gurin tsayuwar ku daban daban menene zaki yi a gurinta bayan kema ganaki gurin nan?” Ruqayyah ta bata rai, bata so tayi subutar baki ba a gaban Sumayya dan tasan ko bata tona mata asiri ba zata bita da nasiha ne, ta juya tana cewa “wannan kuma ba abinda ya shafe ki bane ba” ta wuce sama ta shige dakinta.
Sumayya ta zauna akan kujera tana tattauna maganganun Ruqayyah a zuciyarta. “Ya Salam! Me yarinyar nan take so ta zama ne mai kuma take shirin aikatawa? Ko ma menene akan Fatima ne, that nice Fatima. Ai gwara ka zalunci wanda ya ke azzalumi ne akan ka zalunci wanda ya ke kyautata maka.
Ta tashi ita ma ta tafi saman gurin Ruqayyah ta tarar da ita zaune a bakin gado har yanzu tana huci, ta zauna tace “ko ma menene kike shirin yi ina tuna miki da cewa ba dai dai bane ba, matar nan bata yi miki komai ba. In fact tare ma kika gansu ke ce outsider a cikin su. In baki gode taimakon su a gare ki ba kuwa ai bai kamata ki zamar musu kadangaren bakin tulu ba” Ruqayyah tace “taimako? Kina nufin taimako na suka yi da Hassan ya aure ni? Ni dana taimake shi na tseratar dashi daga mutuwa kuma fa?” Sumayya tayi murmushi tace “in kin manta Ruqayya bara in tuna miki, shi rai Allah ne yake hurawa mutum shi kuma shi yake cire shi a lokacin da ya ga dama. Da ace Allah yayi Hassan zai mutu a ranar da babu ta hanyar da zaki bi ki cece shi. Shin bakya tunanin cewa Allah ya hada ku a ranar ne a matsayin jarabawar ki? Dan yaga yadda zaki yi da haduwar taku? Think about this please” ta mike ta sauka kasa ta fara hada yan kayanta da tazo dasu. Ba zata iya cigaba da zama a gidan nan ba kar bakin cikin yar uwarta yayi mata illa amma kuma tana tsoron tafiya ta bar ta ita kadai tare da wannan muguwar zuciyar tata mai kissima mata abubuwa iri-iri. Sai ta ajiye jakar tata a kasa ta zauna a bakin ttare da yin tagumi tace “oh Allah. What should I do?”
Kamar amsar tambayar ta sai gashi Hassan ya dawo yana ce mata ya hadu da Baba a office ya kuma roke shi a kan ya bar ta ta dan yi musu kwana biyu saboda Ruqayyah bata jin dadi “duk da cewa da akwai masu aiki a gidan, amma nata ke bukatar wani a kusa da ita sosai yadda ko wani abun zai faru za’a yu saurin taimaka mata” sai Sumayya taji tausayin sa, shi duk ya damu Ruqayyah bata da lafiya bayan kuma karya take yi lafiyar ta kalau, shi duk ya damu da Ruqayyah bayan Ruqayyah bata damu dashi ba ko kadan, ita wani abin take hange na daban.