TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali sati ya zagayo, babu wanda ya kuma neman wani a tsakanin Ruqayyah da Fatima, Hassan da Hussain kuma babu wanda ya kuma tayar da maganar sun maida hankalin su kan bikin bude kamfanin da yake gaban su, har ranar tazo kuma aka gabatar da bikin successfully komai ya tafi yadda aka shirya, sannan da daddare suka gabatar da dinner ga friends and families dinsu.

Da farko Hussain yayi niyyar samun gurin da za’a yi a can, amma sai Fatima ta bashi shawarar tunda dai dinner din ta mutum dari ce very close friends da kuma immediate family members why not a mayar da ita informal kawai ayi a gida? Akwai filin da swimming pool dinsu yake, katon guri ne zai dauki duk mutanen. Shawarar tayi masa dan haka aka kira masu decoration suka zo suka gyara gurin aka saka kujeru da tables aka shirya komai tun two days to day din. Abinci kuma tace tunda informal dinner za’a yi home cooked meals zai fi dacewa akan ayo order. Amma duk da haka sai da tayo hayar wasu chefs gida biyu sannan suka hadu har ita da kuma kannen ta biyu da suka zo ga kuma su Khadijah duk da suka shigo ga kuma yan aiki nata dana Aunty duk aka hadu a katon kitchen dinta ana tayi. A soya wancan a dafa wannan a yanka wancan. Nafisa ce ta fita zuwa part din Hassan ta gaya wa Ruqayyah cewa ana aikin abinci fa a gidan Hussain ko zata leka ayi da ita? Tana dariya tace “duk da dai nasan yadda kike ta laulayin nan ba wani taya mu aikin da zaki yi amma dai ai ayi hira a dan wataya ko?” Ruqayyah ta tabe baki tace “kin san bana son warin kitchen, kar in je in tayi muku amai in haramta muku abincin ku gwara inyi zamana kawai” sai Sumayya taji babu dadi dan haka ta dauko mayafin ta tabi Nafisa suka tafi. Suna zuwa Khadijah tace “bata taho ba ko? Dama ai nasan ba zuwa zata yi ba kawai dan kar in sagar muku da gwuiwa ne yasa banyi magana ba amma gashi nan kun tabbatar ai yanzu” ashe da rabon tata guiwar ce zata sace dan tana rufe baki sai ga Ruqayyah ta shigo. Nafisa tace “a’a, aman fa?” Tace “yaya zanyi? Abinda ya zama dole ai dole ne ayi shi. Wannan abu ai namu ne maganin a kwabe mu bare ma suka zo ballantana mu?” Sai duk suka yi shiru suna kallon kallo ban basu san waye bare a gurin ba.

A lokacin Sumayya ta koyi abubuwa da yawa ta fannin girki, musamman a gurin Fatima da kuma chefs din da aka gayyato sai ta fahimci cewa Ruqayyah sam bata da wayo kuma bata san ma me take so ba, da ta kwantar da kai da ta samu abubuwa da yawa daga gurin Fatima. Amma zafin ran ta da girman kanta ba zai barta ba.

Idan wani ya shigo gurin yaga yadda Ruqayyah ta kame tana bada order sai ka dauka itace matar gidan, sai ka lura sosai sannan zaka fahimci cewa kare ne da fatar kura dan kayan girkin da ake amfani dasu ma kansu ba sanin su tayi ba ballantana abinda za’a yi dasu. Sai wajen karfe biyar na yamma suka kammala komai, suka jera komai a gurin da za’a yi taron sannan kowa ya tafi da niyyar shiryawa kafin baki su fara zuwa. Ruqayyah tana komawa gida tayi wanka sai ta saka rigar zaman gida tayi sallah tayi kwanciyar ta tana chatting dinta a waya da sababbin kawayenta. Har Sumayya ta shirya ta fito ita kuwa tana kwance, tayi mata magana sai tace ta tafi kawai zasu taho tare da Hassan. Wannan yasa tayi tafiyar ta ta rabu da ita. A kofar shiga gurin ta ga Adam, and he took her breath away, all suit up kamar shine oga Hussain, ya tsaya yana kallon yadda tayi kyau itama cikin doguwar rigar lace dinkin bubu da akayi wa landing da red aka kuma yi mata ado da red flowers a gaban rigar, ta daura dankalin lace din sannan ta yafa red mayafi, fuskarta babu kwalliya sosai amma kyawun da tayi ba kadan bane ba. Ya mika mata hannu, smiling from ear to ear, ta makale kafada yayi dariya yace “a kwana a tashi dai” tace “Allah ya kaimu lokacin, but not now” sai ya dauka wayarsa yace “wannan kwalliyar sai nayi mata hoto dan in ajiye a gefen pillow na” tayi murmushi tana rufe fuskar ta da hannunta shi kuma yana yi mata hoto, sai daya gama tace “ban dauka zan ganka anan ba, tunda naji ance taron is for specific people” ya juya suka jera yana cewa “oga Hussain ne ya banj wadannan kayan yace in shirya in shigo tare dashi saboda in kula da manyan bakin sa, in tabbatar sun zama fully satisfied” tace “ohh kace taron ma yana hannunka gaba ki daya, to plate dina yana gurinka” yace “ke xe ta farko da zaki samu komai da kike bukata, ko oga Hussain ne sai dai ya jira ki gama tukunna” suka yi dariya a tare.

Ruqayyah tana kwance har Hassan ya shigo a gaggauce, ya kalle ta yace “what? Wai baki shirya ba? Ki yi sauri Please ki shirya zan shiga in shirya nima, saboda ina so duk wanda zai zo ya tarar dani a gurin” kafin ta bashi amsa har ya shige dakinsa. Ta koma tayi kwanciyar ta har ya gama shiryawa ya fito yana daura agogon hannu, sai kawai ya tsaya yana kallon ta, fuskar sa tana nuna bacin ransa. “Hassana wai baki tashi ba har yanzu?” Ta tashi zaune tana yamutsa fuska tace “ni fa ba zan je ba mijina, kayi tafiyar ka kawai” sai yana yin fuskarsa ya chanja daga bacin rai zuwa concern yace “ba kya jin dadine precious? Ko jikin ne?” Ya zauna a kusa da ita sai ta fara kakaro kuka, hawaye yana zuba tace “ni ba zanje a wulakanta ni a cikin mutane ba. Ranar nan na shiga gidan da niyyar mu dai-dai ta tsakanin mu tunda naga ka damu da abinda ya faru, naga yadda kake son dan uwanka shine naje dan muyi sulhu, amma matar nan sai ta rufe idonta ta ci min mutunci wai naje cin arziki” ta kara sautin kukanta “babu irin zagin da bata yi min ba wai kar ta sake ganin kafata a gidan ta, harda cewa wai a gidan su banfi darajar bayin su ba, ita tafi ƙarfin tayi harka dani…..” Ya daga mata hannu idanunsa sun kada sunyi ja. “Kinga dakata Hassana. Please not now. Kinga baki ne damu suna waje suna jiran mu ki tashi muje ki shirya mu fita” ta bishi da kallo tana sheshshekar kuka, bata ji dadin yadda yayi reacting ba, tace “yanzu kafi son inje a wulakanta ni a gaban jama’a? Kafi son a gaban kowa da kowa ta nuna wa duniya cewa ba mijina ne mai kudin ba mijinta ne?” Ya mike tsaye yace “she wouldn’t dare. Kuma ita bata isa ta hanaki shiga gidan Hussain ba saboda ba gidanta bane ba. Babu yadda zata yi ta rabaki da ni kamar yadda babu yadda zata yi ta raba ni da Hussain. Ki tashi muje in gani in zata yi wani abu akai. I want to see her try something in yaso ni kuma sai in koya mata hankali” a dolen ta ta tashi ta shirya, amma ita ba haka taso ba, so tayi ace ya hau sosai ya tafi gurin taron ya ciwa Fatima mutunci ita kuma ta rama, sai taga Hussain wa zai zaba a cikin su. Ta riga ta san amsar, wannan shi yasa take son ta hada rigima a tsakanin su.

Haka suka shiga cikin gurin taron hand in hand, suka tsaya a bakin kofar shiga gurin tare da Hussain da Fatima, duk wanda yazo zasu tarye shi su gaisa yayi musu murna sannan ya shiga ciki, a haka har bakin suka gama zuwa sannan ya kuma kama hannunta suka shiga ciki suka sake zagaya bakin sannan suka he suka zauna aka fara gabatar da taro. A lokacin ne yan gidan su Ruqayyah suka shigo gurin, ita kanta bata san Hassan ya gayyace su ba kuma bata nemi ya gaiyace sun ba saboda tana ganin kamar zasu ata mata show ne, kamar zata wulakanta a idon mutane irin wadannan in aka ga Baba da Inna Ade a matsayin iyayenta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button