TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana ganin su ta fara sunne sunne wai kar su ganta ai kuwa Hassan ya kama hannunta har gaban su ya hada su sannan ya koma gurin sauran bakin sa. Yana ta zuba ido yaga Fatima ko wani wanda ya danganci Fatima yazo yayi wa Ruqayyah ko wanda ya danganci Ruqayyah wulakanci amma bai gani ba, sai ma yaga Fatima ta nuna wa Hussain su Baba sannan sun tafi takanas sunje sun gaishe su.

Taron ya kayatar sosai dan ko dinner din bikin su bata yi wannan haduwar ba musanman saboda wannan din babu mutane sosai kamar wancan. Sumayya tana ganin du Inna ta bar gefen Adam da da suke tare ta taho gurinsu tana nuna jin dadin ta, a ganin ta honouring dinsu Hassan yayi daya gayyace su zuwa inda sai wane da wane ne a gurin. Ita ta kai su gurin Aunty suka gaisa sannan ta samar musu gurin zama yayin da Adam ya tabbatar sun sami komai da suke bukata. Yayin da Ruqayyah tayi excusing kanta ta koma side din Hassan, ta gaya masa cewa bata son ta barshi shi kadai shi yasa ta dawo “naga kowa yaci kwalliya, har da yammata, bana son idon mijina yayi yawo nafi son ya tsaya a kaina ni kadai” yayi mata murmushi “ke ma kin sani ai ba sai na gaya miki ba, idanun Hassan will always be on Hassana”.

Komai ya faru a gurin sai Ruqayyah tayi wa Hassan complain cewa anyi wani abu ba dai dai ba. Ko tace mutane sunfi kula Hussain a kansa, ko tace wata tayi mata kallon banza dan ba Fatima bace ba ko kuma tace wani ya tafi bai yi masa sallama ba amma yayi wa Hussain. Hassan Allah Allah yake yi a tashi saboda zuciyarsa gaba ki daya ta dawo makwogwaron sa. Ana fara tafiya bayan ya tabbatar personal abokan sa sun tafi kuma su Baba sun tafi sai ya jata suka koma gida. Suna shiga gidan tayi tsaki tace “ni duk raina a bace yake wallahi, ni ban ga dalilin ma da yasa za’a yi taron nan a gidan Hussain ba bayan kuma kaine babba, ko da yake dole ayi acan dan a nuna wa mutane babban gida” ya kama hannun ta bai ce mata komai ba suka hau sama. Suka wuce dakinsa tana cewa “dakina zan je in dan huta kadan naji wannan zirga-zirga ta sa mara ta ta fara ciwo” yayi murmushi yace “wani abu nake so in nuna miki a dakina” suna shiga ya wuce da ita valcony dinsa ya tsayar da ita ya tsaya a bayan ta yana nuna mata Hussain a tsaye a kofar gidan sa suna sallama da wasu baki daya rako yace “kin ga wancan mutumin?” Ta dauke kanta tace “wai Hussain kake nuna min? Na gane shi mana, ko dan show up dinsa da san a sani ai dole in gane shi ko a ina na hango shi” ya runtse ido ya bude ya sake juya mata fuskarta side din Hussain yace “ki kalle shi sosai” tayi kokarin dauke kanta amma ya rike fuskar a guri daya ya hana ta juyawa yace “ina so ki kalle shi sosai ki gane shi sosai. Sunansa Hussain Aminu Abdullahi, and he is my better half, kaf duniyar nan babu wani mutum ko wani abu da nake so sama dashi. In nace kowa ina nufin kowa, har wannan” ya fada yana dora hannun sa akan marar ta. “Har wadannan zan iya giving dinsu up for him. For a smile on his face. So I want you to listen to me carefully. Daga yau, bana son ki sake fada min wata magana marar dadi a kansa. Bana so, bana son ji. Am I clear?”

Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani wajen to na sata ne, in kina so ki karanta halal dinki ki yi min magana ta wannan number din 08067081020New Chapter

Ji tayi jikinta gabaki daya ya zama kamar na statue, ko hannunta ta kasa motsala, ko idonta ta kasa kiftawa, zata iya rantsewa cewa hatta zuciyarta ta tsaya da aikin buga jini zuwa sassan jikinta. Ya kawo bakinsa dai dai kunnenta ya sake cewa cikin rada but harshly “is that clear?”

Automatically kanta ya motsa da alamar eh, ya saki fuskarta sannan ya dan buga kafadar ta yace “good girl” sai kuma yayi kissing side din fuskarta ya juya ya bar gurin. Ta lushe idonta tana jin zuciyarta data zama kankara tana narkewa ruwan yana taruwa a idanunta, ko a cikin mafarkinta bata taba tsammanin Hassan zai iya furta mata wadannan kalaman ba, yes, ta san he is strong tun sanda yana zuwa zance gurin ta amma bayan bikinsu, irin son da taga yana yi mata ta dauka ta kama shi a hannun ta, musamman a matsayin da take rike dashi na wadda tayi saving life dinsa ga kuma darajar abinda yake cikin ta. Ta dauka zai zabe ta akan kowa a duniya, amma shine ya furta mata to her face cewa yafi son Hussain akan komai, harda jaddada mata in yace komai yana nufin komai, harda misaltawa da abinda yake cikinta, wato ita bama ta cikin layin da Hussain din yake ciki.

Taji duk wani shiri nata yana kuncewa yana bin iska. Taji duk wani abu da yake kanta yana sauka kasa yana farfashewa. Taji duniya tayi mata zafi.

Tasa hannu da niyyar goge hawayen da ya taru a idonta amma sai taji babu. Ita dama haka take in ranta ya baci irin wannan to sai hawaye yaki zubar mata sai dai tayi na zuci. Sai dai in kukan karya ne to da gudu hawayen yake zuwa. Ta mayar da hankalinta zuwa inda Hassan yayi forcing dinta ta kalla taga Hussain har yanzu yana tsaye hannunsa rike dana Fatima suna dariya tare da wasu mutanen su da suka rako waje. Ta dauke kanta gefe tare da rufe idonta, mafarkin ta yana karasa tarwatsewa a gaban idanun ta.

Ta saki karfen, sannan ta juya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta shiga dakin Hassan, ta jiyo motsin sa a toilet daga dukkan alama wanka yake yi sai ta fita daga dakin a ranta tana cewa “yau sai dai kaje ka rungume Hussain ba dai ni ba”

Dakin ta ta tafi ta yar da jakar hannunta a kasa sannan ta haye kan gado tana kara jin zafin maganganun Hassan a ranta. Tabbas sai ya san ita ya gaya wa haka, sai yayi nadama. Ta jima a kwance taji motsin shigowar Sumayya, sai ta jita ta murda dakin ta shigo da sallama. Bata motsa ba har tazo gaban gadon ta dan taba ta tana cewa “Ruqayyah ki tashi ki cire kayan ki mana, a haka zaki yi bacci? Kiyi wanka mana ki tafi dakin mijin ki” ta karasa maganar cikin nishadi, da alama tana cikin farin ciki, to mai zai hana ta farin ciki ita kuwa tunda bata da wani problem a rayuwa? Komai yana tafiyar mata yadda take so ga Adam kullum yana kara cika ta da kaunarsa?

Jin Ruqayyah bata ce komai ba yasa ta kuma taba ta, ta dauka bacci take yi. Sai taga ta bude idonta tana kallonta a take gabanta ya fadi, tasan irin wannan jan idon tasan irin wannan kallon, tace “Ruqayyah? Me ya faru?” Ruqayyah tayi juyi tana kara hayewa can saman gadon, tana jin kamar zuciyarta zata fito waje ida bata gayawa Sumayya ne yake damunta ba.

Sumayya ta zauna a kan side drawer tace “me ya faru Ruqayyah? Wani ne ya bata miki rai a gurin taron?” Ruqayyah ta dauke kai gefe tace “mijina ne, baya sona kuma yanzu, yace yafi son Hussain a kaina. Kamar yadda Baba yace yafi son ki a kaina” sai kuma hawayen suka fara zuba. Sumayya ta hau kan gadon ta jawo ta jikinta tana cewa “Ruqayyah, ba wai ke ce ba’a so ba kuma kema kin sani, duk muna son ki sosai da sosai kawai wasu daga cikin halayen ki ne ba’a so. Na tabbatar shima wani abu kika yi masa har ya fadi haka, amma son ki daban a ransa son Hussain kuma daban, ai ku din ba abu daya bane ba kowa da gurbin da yake zaune a kai” Ruqayyah ta fara kokarin kwace jikin ta daga Sumayya tana cewa “cewa fa yayi har abin da yake cikina zai iya hakura dashi saboda Hussain yayi murmushi, wanne irin so ne wannan? Wacce irin magana ce wannan?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button