TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sumayya tayi murmushi tace “Ruqayyah! Hassan duk duniya bashi da kamar Hussain kuma har a nade ta ba zai samu kamar Hussain ba. Abinda yake cikin ki kuwa zaku kuma samun wadansu har goma ko fiye da haka, kinga kuwa ai ba za’a taba hada soyayyar su a guri daya ba. Amma ke me kika yi masa haka da zafi har ya gaya miki wannan? Na tabbatar kin kure hakurin sa ne” Ruqayyah tace “dama ai ba hakurin ne da shi ba, fada ne dashi da saurin fushi. Shine har da yi min warning wai kar in kara gaya masa laifin Hussain baya son ji”

Sumayya tace “ai tun farko dama sai dana gaya miki, nasan duk boye boyen halinki da kike yi dole sai ya sani tunda shi hali ai baya boyuwa indai har za’a zauna tare ballantana zama irin na aure. Kin nuna masa ke mai hakuri ce da kawar da kai bayan kuma ba haka bane ba yanzu zafin zuciyar taki da mita kika nuna masa ko? Ni bansan halin maza ba amma nasan ko a matan ma ba kowa ne yake son zama da mutum mai mita ba. Ballantana har ki kai ga fadin aibun dannuwansa a gaban idonsa. Gaskiya baki kyauta ba, kuma duk abinda ya gaya miki ke kika jawo wa kanki. Amma nasan hakan daya fada ba wai dan baya sonki bane ba sai don yana so ya nuna miki cewa abinda kike yi din ba dai dai bane ba. Nima kuma na gaya miki ba dai dai bane ba, dan nasan yadda nake sonki nasan kuma ko menene zaki yi na rashin kyautawa ba zan so inji wani ya fada ba ballantana kuma in naji anyi miki sharri”

Ruqayyah ta dago kai da sauri “sharri? Au sharri nake yi masa? Bashi da son a sani ne da nuna wa mutane basu isa ba? Shi fa jinsa yake yi tamkar sama yake da kowa, jin kowa yake yi a kasan sa dan nayi kokarin ankarar da danuwansa shine nayi laifi? Dan shi fa nake yi ba dan wani ba, dan in kwato masa yancinsa nake yi badan komai ba” sai tayi shiru tana kallon hannunta, Sumayya ta gyara zamanta tace “gaya min, menene plan dinki? Me kike so kiyi archiving? What are you up to?”

Ruqayyah ta danyi tsaki fuskarta tana nuna bacin ranta ta share hawayen da ya rage a idonta tace “ke kinfi kowa sanin ban taba tunanin zan auri mutum kamar Hassan ba sai da na ganshi. Na kuma dora raina akan cewa kudin nan nasa ne, na riga na gama saka zuciya ta akan hakan. Bayan naga Hussain naso ace shine Hassan, naso ace shi zan aura, naso ace shine wanda na tarar ranar nan a toilet amma kuma na hakura na karbi Hassan din tunda a lokacin ina tunanin shi yake da kudin, yanzu kuma na fahimci suma kudin ba nasa bane ba” ya danyi tsaki tana girgiza kanta tace

“na tsani wannan Fatiman ta fiya iyayi da gulma da munafurci da nuna isa, na kuma fahimci Hussain yana matukar sonta, sannan yana son Hassan sosai” ta sake yin shiru kamar mai tunani sannan tace “I just want to be her. I want her husband, her house and her power” Sumayya ta zaro ido “Ruqayyah baki da hankali? Ta yaya zaki so mijinta bayan ga naki? Ta yaya zaki so gidan ta bayan ga naki? Ta yaya hakan zata yi wu?”

Ruqayyah tace “hakan ba zai yiwu ba na sani, na fahimci Hussain tun da nazo gidan nan na gane baya kaunata ko kadan, ko kallo ban ishe shi ba, bana jin ko babu Hassan a duniya Hussain zai kalli inda nake sai dai ko da niyyar taimako amma ba da niyyar aure ba. Wannan yasa na hakura dashi. Sannan nake so in mayar da Hassan shi ya koma Hussain din. So nake in mayar dashi CEO”

Sumayya tace “how?” Ruqayyah tace “niyya ta in hada rigima tsakanin Hassan da Fatima, ta hanyar amfani da abinda yake cikina saboda na fahimci irin son da Hassan da shi kansa Hussain suke yi wa cikina. So nake su yarda bata son abinda yake cikina yadda duk abinda ya samu cikin ita za’a yi zargi. So nayi in rura wuta tsakanin su ta yadda Hussain will be forced to choose between them kuma nasan cewa Hassan zai zaba duk kuwa da cewa rabuwa da Fatima zata yi destroying dinsa. And that destruction shi nake after. Idan ya zama ba zai iya cigaba da rikon kamfani ba dole Hassan will take over. Idan kuma something bad ya faru dashi komai ya zamana Hassan din”

Sumayya da mamaki ya ishe ta ta katseta ta hanyar cewa “something bad as in?” Ta daga kafada tace “babu wanda ya san gawar fari dan haka dan Adam babu abinda zai yi fata illar Allah ya bashi rayuwa mai tsaho” Sumayya ta dafe kanta tace “Ruqayyah wai kina nufin kima fatan Hussain ya mutu saboda Hassan ya samu gado” tayi shiru kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace “kowa ma wata rana zai mutu ai”

Ruqayyah tace “exactly, hakan yana nufin kema zaki iya kwanciya yanzu gobe kuma ba zaki tashi ba. Shi kuma Hussain zai iya ya kara shekaru saba’in ko fite da haka a rayuwa. Dan Allah Ruqayyah ki gaya min cewa ba wai kina tunanin harming Hussain bane ba saboda dukiyarsa. Dan Allah Ruqayyah ki gaya min babu wannan tunanin a ranki”

Ruqayyah ta bata rai tace “ni na isa in yi masa abinda Allah bai yi masa ba? Buri na ne dai kawai. Dan Adam kuwa ai ba’a raba shi da buri in dai akwai rai a jikinsa. Kuma wannan burin nawa ba zai cika ba indai har Fatima tana zaune a gidan sa saboy a kowanne lokaci zata iya samun ciki ta haifa masa da, samun da a gurinsa kuwa yana nufin ni da shiga gidan can sai dai da ziyara” ta mike zaune tana kokarin sauka daga kan gadon tace “besides, duk wannan burin nawa yabi iska tunda Hassan ya debi kasa ya watsa min a idona. Hussain zai cigaba da zama da fatiman sa ta haifa musu yaya and they will live happily ever after. Ni kuma da nawa yayan Hassan yayi conderming din mu to life of bakin ciki a karkashin dan uwan sa” sai da takai bakin kofa sannan ta juyo tace “kar ki damu yaruwa ta, the plan is off, shi yasa har nake gaya miki”. Daga nan ta shige toilet.

Sumayya ta jima a zaune tana kallon kofar toilet din, zuciyarta tana gaya mata “anya lokaci bai yi ba da ya kamata ta shigo da Inna Ade da Baba cikin maganar Ruqayyah? Amma bata da mental related issues kuwa?”

Ruqayyah ta jima a toilet tana wanka, tana jin kamar tana wanke bakin cikin da Hassan ya cusa mata sannan tana bin maganganun sa a hankali tana digesting tana so ta fitar da ma’anar su. Abinda ta fahimta shine, babu wani abu daya gane a kanta, frustration dinsa kawai shine maganganun data fada akan Hussain, amma da sannu in ta cigaba a kan wannan hanyar data dauko to sai komai nata ya bayyana gare shi dan haka dole ta rufe wannan babin ta bude sabon babi, this will be the end of her first chapter yanzu zata bude second.

Sanda ta fito daga wankan bata tarar da Sumayya ba, dama ba’a dakin take kwana ba a kasa take kwana saboda bata son ta takurawa Hassan. Ta zauna akan dressing chair tana goge jikinta sai kuma ta dauko wayarta ta nemo number din Minal ta kira sai taji waya take yi, ta ajiye tana saka kayan baccin ta sannan tai Minal din tayi mata flashing, ta dauka tana cewa “ke yanzu da girman ki kike flashing?” Minal tace “ke babu wani girma anan, ke yanzu ai hajiya ce dan haka gwara ke ki kirani dan ni lallaba katin waya ta nake yi. Ya akayi? Ina mijin naki har yanzu baki kwanta ba?” Tace “ni ba wannan ba da Allah can, so nake ki damu lokaci ki zo akwai maganar da nake so muyi” Minal tace “dama gobe nake cewa zan shigo in karbi tsaraba ta, naga baki da niyyar zuwa ki kawo min har gida” Ruqayyah ta kalli cikin closet dinta, ita in ba shiga tayi ba har mantawa take yi ta lodin kayan da Hassan ya siyo mata a matsayin tsaraba, tace “akwai tsaraba kam, in kin zo kya karba” tace “to sai nazo din. Akwai wata magana nima da zamu yi” daga nan suka yi sallama ta kashe wayar ta ajiye sannan tayi shirin bacci ta kwanta tana jin wani freedom a ranta. Yau dai zata kwanta tayi ta juyin ta babu wanda zai dame ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button