TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari da safe Sumayya ta shirya tace gida zata tafi. “Naga kin warke ai, kuma kina da yan aikin ki gwara in koma gida in cigaba da taya inna ayyukan gida” Ruqayyah ta bata rai “ba dai akan maganar jiya zaki tafi ba ko?” Sumayya tace “maganar jiya ai mun gama ta tunda kince kin rufe wannan babin, ni dai zan yi ta miki addu’a kullum, sauran kuma tsakanin ki da mijin ki ne”.

A lokacin Hassan ya fito daga dakinsa, daga dukkan alama yanzu ya tashi dan fuskarsa da alamun bacci. Sumayya ta gaishe shi Ruqayyah ma haka, ya amsa yana kallon Ruqayyah ita kuma ta dauke fuska gefe tana kara bata rai yace “Sumayya ya na ganki da jaka haka da sassafe ko karyawa baki yi ba?” Tace “na karya ai duk kuna bacci. Akwai abinda nake so inyi a gidan ne da safen” yace “ohh. To bara in dauko key sai in kaiki ko?” Tace “lah, kayi zamanka, ina fit zan samu abin hawa” yayi murmushi yace “I insist” daga nan ya koma daki ya fito yana cewa “Precious bara in kaita in dawo ko” can kasa tace masa “a dawo lafiya” sai yayi murmushi, yasan fushi take yi.

A hanya suna tafiya yace da Sumayya “ina saurayin ki? I half expected to see him a waje yana jiranki, na dauka shi kuka yi dashi zai kai ki gida” ta danyi dariya tana wada da bakin hijab dinta tace “yana gidan mu ai yanzu. In kaje zaka ganshi a can in dai har ba zasu fita da sassafe da Hussain ba” ya dan bata fuska yace “gidan ku kuma? Me zaiyi acan da sassafe bayan kuma ke kina nan gidan?” Tace “karatu, karatu yake zuwa dauka acan kullum da assuba sannan kuma da daddare in ya gama da Hussain” ya maimaita “karatu?” Tace “yes, kasan ai….” Yace “I know, but kawai nayi mamakin boldness dinsa da zai je gidan surukai koyon karatu” ta dan ji kunyar kalmar surukan da yace. Suka cigaba da tafiya shiru, sannan yace “a gida Ruqayyah tana da fada ko? Baba ya taba ce min tana da fada” ta dan kalle shi tana hango damuwa a fuskarsa sai taji tausayinsa har ranta, tace “haka ne, kasan kowa da halinsa, amma I believe zata daina” ya gyada kai yace “eh zata daina, nima haka nace da baban a lokacin. Sai me take dashi bayan fadan?” Tayi shiru, a ranta tana tunanin wadannan tambayoyin Hassan kamata yayi ace yayi su tun kafin ya auri Ruqayyah ba wai yanzu da take dauke da cikin sa ba.

Ta dan yi murmushi a lokacin da yake packing tace “a hankali duk zaka fahimci yar uwata. Kai dai yanzu kayi ta addu’a kana hakuri kuma kana saka ido, komai zai wuce” ta bude kofa ta fita.

Bayan Hassan yayi breakfast, wanda shi kadai yayi kayansa dan kafin ya koma Ruqayyah har ta gama nata ta shiga daki, sai ya shirya ya leka ya ganta a kwance ya gaya mata ya fita. Yana so ya zauna suyi magana amma kuma akwai abinda zasuyi a office yau dashi da Hussain dan haka dole ya fita da wuri.

Da rana Minal tazo, Ruqayyah ta tare ta sannan ta jata zuwa dakinta. Minal tace mata “ke wani gara ne fa na samu nake wanka, shine ya kawo ni gidan nan ma yanzu. Har ya fara yi min maganar aure” Ruqayyah tayi dariya “kuma shine kike ce masa gara?” Minal tace “ke babba ne fa, a haife zai haife ni wallahi, zan baki labarin sa amma gaya min abinda yasa kika kirawo ni”.

Sai Ruqayyah ta bata labarin rigimar da suka yi da Hassan jiya. Tace “to ni yanzu duk komai ya kunce min wallahi. Shawara nake so ki bani ta inda zan dora”

Minal tayi tsaki tana hararar ta tace “ke matsalar ki shine har yanzu baki ware ba wallahi, gidadan ci ne yake damun ki ba kadan ba. Ba tun yau ba na baki shawarar yadda zaki yi amma kin kasa fahimta. Kuma wallahi in kika cigaba a haka to ina yi miki albishir da komawa gidan Baba a matsayin bazawara” Ruqayyah taji wata irin faduwar gaba tace “Allah ya tsari bakin ki, kije ki kuskure bakin ki dan Allah. Kin ga ni fa aurena da Hassan mutuwa ce kawai zata rabamu” Minal tace “ai kuwa kina gab da tafiya in gaya miki. Mutanen nan fa wayayyu ne kuma ilimi ya ratsa su ta ko’ina, ba zaki taba iya hada su ba wallahi saboda kafin ki gansu ke sun ganki. Kinga wannan gimbiyar, to wallahi idan ke baki kore ta ba tabbas ita zata kore ki with just a blink of her eyes. Dole sai kin ajiye wannan zafin kan naki da wannan gidadan cin naki. Kinsan abinda yake zaune da ke a gidan nan? Son da mijin ki yake yi miki ne ba wani abu ba. In kuka cigaba a haka kuwa son zai dusa she then zaki zama baki da sauran wani madogara kuma”

Ruqayyah tace “ni duk ba wannan ba, ki gaya min abinda zanyi nace ba wai kike min bitar abinda na riga nayi ba” Minal tace “na gaya miki ai, kissa xaki bisu da ita, ki kama mijin ki ki kama surukarki ki kama yan uwan mijinki. Kinga wannan fatiman? To itace gidan nan ki kama ta hannu bibbiyu ina gaya miki. Zan je gidan Aunty Hafsa yanzu xan gaya mata halin da kike ciki zata saka ki a group dinsu na matan aure zasu koya miki duk yadda zaki bi da su. Sannan kuma sai kin hada da addu’a, ke kina yi kuma kina sakawa ana yi miki, kina musu kissa kuma kina toshe bakin su da addu’a yadda ko sun ga wani abu ba zasu iya magana ba. Akwai wani malami da Hajiya Binta kawar Aunty Hafsa ta hada ni dashi yayi min addu’a akan wannan garan da nake gaya miki. Kinga shi matarsa ce bata haihuwa shekara da shekaru ga uban kudi kamar ya kashe shi, shi kuma son matar yake kamar me, ya kasa yi mata kishiya, da kyar Alhaji Kabiru ya hada ni da shi yana ta yanga amma dana samu naje aka tottofe min shi shikenan. Yanzu bina yake kamar jela”

Ruqayyah tana girgiza kai tace “bana son harka da bokaye, bana son in rasa sallolina na kwana arba’in” Minal tace “ke dalla can ba boka bane ba, malami ne, da ayoyin Alkur’ani da sunayen Allah zai rufe miki bakunan su gam”

Wannan littafin na siyarwa ne, in kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki ki neme ni through WhatsApp ta wannan number 08067081020The Fortune Teller

Ruqayyah tayi shiru tana kallon Minal, abubuwa da yawa suna yawo a cikin kwakwalwar ta zuciyarta tana rabuwa kashi kashi, ta girgiza kanta. “Minal tsoro nake ji, irin wadannan malaman da su da bokaye duk tafiyarsu daya. Baki san wanda yasan Alqur’ani yasan irin sirri kan da ke cikin sa kuma in zuciyarsa bata da kyau to there is no limit to what he can do ba? Kuma wadannan laifin su yafi na boka muni ba? Kinga kakan mu, Malam Shehu? Babu abinda ba zai iya yi da ayoyin Alqur’ani ba amma baya yi din, ya zabi yayi aikin alkhairi dasu saboda ya zabi lahirar sa akan duniyar sa, inna Ade ma haka, ko kin san Inna Ade tafi baban su ilimin Alqur’ani? Amma ta zabi ta koyar da shi ga mutane saboda shine abinda take so. Nima nasan iya kacin abinda na sani, banbanci na dasu shine ni ina so in samu duniya sannan itama lahirar in samu yayinda su kuma suka ajiye duniyar a gefe suke neman lahirar. Duk iskanci na Minal bana wasa da ibada ta, ba zance bana zunubi ba dan ina yin karya da sauran kananan zunubai amma ban taba aikata wani a cikin manyan zunubai ba kuma ba zan fara ba. Kinga zuwa gurin boka ko malamin tsubbu to shirka ce, ita kuma shirka ita ce oga kwata kwata saboda in kayi ta tamkar ka bar addini ne, wanda kuwa duk ya bar addini kuma ya mutu ba tare daya dawo hanyar dai dai ba to ya mutu a kafiri. Ni kuwa Minal ba zanso in mutu a kafira ba bayan ita kanta duniyar ba samunta nayi ba, two zero kenan”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button