TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Minal tayi tsaki tace “ke kam ana baki kina kin karba. Na gaya miki ba boka bane ba kuma malamin tsubbu bane ba. To gaya min, shi Malam shehun da kike yin magana akan sa mutane basa zuwa gurinsa ya taya su da addu’a akan wani abu daya shige musu duhu ko wani abu daya taso musu?” Ruqayyah tace “suna zuwa mana” Minal tace “exactly, shima wannan haka yake. Na gaya miki sunayen Allah kawai zai kira sai kuyi addu’a ku shafa shikenan. Kinsan ita addu’a baki baki ne, wani yana yi kamar yankan wuka haka take wani kuma sai yayi tayi bai samu nasara ba. Ke kina yi shima can yana yi miki shikenan” Ruqayyah dai tayi shiru tana tunani sannan tace “baya duba kasa?” Minal tayi dariya tace “babu kasa ma a gidan sa. Charbi kawai zaki gani da Alqur’ani a gaban sa”.

Ruqayyah tace “shikenan, zan zo muje din amma in naga wani abu da bai kwanta min ba zan gudu, ehe, dan ba zan zo duniya a banza in koma a banza ba sannan in tarar da can din ma wayam”

Sai suka shirya plan akan cewa Ruqayyah zata je gidan su ta kai musu tsarabar tafiyar da tayi, daga nan zata ce zataje gidan su Minal din ta kai mata tata tsarabar daga nan zata wuce gida. In yaso sai suje gidan malamin tare.

Bayan tafiyar Minal ne Ruqayyah ta shiga kitchen dinta. Yau ne rana ta farko data shiga kitchen din da niyyar girki, ta bude freezer taga akwai naman da bata ma san lokacin da aka zuba shiba, sai data tambayi yan aikin ta suka gaya mata ranar da zasu dawo Aunty ta aiko aka zuba musu duk kayan amfani a kitchen dinsu. Ta bude store taga akwai kayan garar ta suna nan suma jingim dan babu wanda aka raba wa duk zuba musu kayan su akayi a store. Har da drinks a jere a gefe wanda shima aka ce aunty ce ta aiko da shi.

Tayi shiru tana tunanin me ya kamata ta dafa ne, in dai har zata bi maganganun Minal to dole ta koyi abubuwa da yawa a ciki kuwa har da girki dan ta rike Hassan a hannunta. Ta tuna Fatima tayi mata alkawarin zata koya mata girki in sun dawo Nigeria amma yanzu kuwa anya in taje zata kulata? Maybe ma ta bita da bakar magana. Ta danyi tsaki, gaskiya lamarin nan sai ta dage sosai sannan zata cimma burinta, ita zuciyarta a kusa take, ita bata iya munafurci ba shi yasa har suka fara harbo jirgin ta. Amma dole ta koya koda kuwa a gurin Hassan ne dan dama shi tun tana gida take rufe shi a bai bai kuma yake rufuwa yanzu ne dai kawai frustration dinta akan Fatima ya saka ta fara bude masa kanta shi kuma a take ya buga mata warning.

Ta kalli yan aikin tana realizing ita ko sunayen su ma bata tsaya ta wani rike ba, tace “wace ta iya girki a cikin ku?” Duk su biyun suka ce sun iya. Tace “to ayi mana girki, tuwon shinkafa miyar agushi a saka nama sosai” suka ce shikenan ? Ta daga kafada tace “eh shikenan” sai bayan ta tafi sai ta tuna ai yan gayu abinci ba kala daya suke yi ba ko? Kamar har da snacks ake hadawa da kuma dan farfesu haka. Sai ta koma ta gaya musu suyi farfesun kaji sai su saka naman kasuwa a cikin miyar. Suka gaya mata babu fresh kayan miya sai markadaddu, babu kuma kayan kamshi, ta koma sama ta dauko kudi ta basu tace su bayar a waje wani ya siyo. Tayi kamar zata zauna suyi aikin tare, maybe ta koyi wani abu, amma sai ta kasa zaman kar su fahimci bata iya ba su raina ta. Ta debi drinks ta tafi dasu sama ta zuba a fridge din daya ke can ta kunna sannan ta koma dakinta ta gyara inda suka bata ita da Minal ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atampa wanda daya ne daga cikin dinkunan da ta bayar kala ashirin kafin su tafi honeymoon. Tayi kwalliya irin wadda taga Fatima tana yi, daurin dankwalin ma shigen nata tayi. Sannan ta saka awarwarayen gold kamar yadda taga tana yi sai tayi sallar azahar sannan ta koma kitchen din ta tarar sun kusa gama abincin. Sai ta dawo sama ta kunna tv tayi kwanciyar ta akan kujera tana danna wayarta. A lokacin ne taga an saka ta a sababbin groups, ta kuma fahimci aikin Minal ne, taga wata ta aiko a bata shawara akan uwarmijinta da ta sako ta a gaba, mutane kowa yana fadar albarkacin bakinsa wasu suna bata shawarar da hatta ita Ruqayyah ta fahimci ba dai dai bane ba wasu kuma suna bata shawarar dai dai, masu cewa tayi addu’a kuma suna ta fada. Tayi shiru tana ta lissafi, tabbas social media guri na na samun abubuwa da yawa, alkhairi da sharri dukka, ya danganta da menene a zuciyar mutum.

Tana nan a zaune yan aikin suka hawo da abincin suka shiga dashi dining room sannan suka tambayeta in akwai wani abu kuma, da hannu tayi musu alamar suje kawai, har laasar tayi sannan ta tashi ta koma daki tayi sallah tana jin anya kuwa zata iya cigaba da jiran Hassan dan ita yunwa take ji already, sai ta tunawa kanta da cikin da yake jikinta dan haka tana fitowa ta tafi gurin abinci ta bude zata zuba. Kallo daya ta yiwa tuwon tasan bai tuku ba, tana saka shi a plate kuwa ya fara tarwatsewa. Tayi tsaki tana jin ranta yana baci, ta tuno da tuwon da taci ranar nan a part din aunty wanda ko kwayar shinkafar baka gani a ciki. A bude miyar taga babu laifi a ido, ta dan zuba tana ci taji gishiri yayi yawa. Ranta bai kara baci ba sai data bude farfesun. Gaba ki daya kazar ta narke romon kuma yayi ruwa tsululu. Ta zauna ta zuba tagumi, yanzu ya zata yi kenan? Ita da taso in abincin yayi dadi ta nuna masa kamar ita ce tayi? Wannan ai ita suka bawa kunya.

Kamar daga sama taji sallamar Hassan, tayi kokarin kirkirar murmushi dan ta tare shi amma sai ta tuna cewa fada fa suka yi kuma har yanzu basu shirya ba, dan haka ta bata rai ta koma ta zauna tana cika tana batsewa. Taji motsinsa ya shiga dakinta sannan ya dawo palon sannan ya taho dining din, ya tsara yana kallonta ita kuma ta maze tan cigaba da jujjuya abincin gabanta. Ya jawo kujerar kusa da ita ya zauna yana kokarin leka fuskarta sai ta dauke kai gefe, ya danyi murmushi mai sauti “haba my Precious wife, wai fushin ne har yanzu vaki gama ba?” Ya kama hannunta tayi kokarin kwacewa yace “look. Nasan abinda na fada jiya ya bata miki rai, but dole ce ta saka na fada. Kinga munyi aure ne ba tare da mun fahimci halayen junan mu ba, dama nasan dole watannin farkon auren mu a going to be rough on us, tunda a lokacin ne zamu fahimci kanmu, ina son duk abinda nayi miki, ko menene wanda kika ga ba kya so dan Allah ki fada min dan in san cewa ba kya so kinji? Ni ma kuma in kika yi min abinda bana so zan gaya miki kinji? Kamar jiya, na gaya miki bana son jin magana marar dadi akan Hussain saboda bana so din, idan kuma ban gaya miki ba ai ba zaki sani ba ko? I know I was harsh a magana ta but kiyi hakuri raina ne ya baci saboda abinda kike fada kina kara maimaita wa. Na sani Hussain dan Adam ne kamar mu, kowa kuma yana da bangaren sa mai kyau da marar kyau dan haka duk wasu halaye na Hussain na sani bana bukatar ki gaya min su. Kinji?” Ya saka hannu ya juyo da fuskarta da take zubar da hawaye yana kallo sannan ya girgiza mata kai yace “ya isa haka, ko nima so kike inyi kukan?” Ta turo baki “ba kai ne kace baka sona ba wai kafi son Hussain a kaina” yayi dariya “ohh kukan kishi ne ashe kike yi. To bara in gaya miki Hussain side dinsa daban a zuciya ta kema haka. Kin san wani abu? Sai da na aure ki ne fa na zama complete mutum, Hussain yana tare da ni tun a ciki amma ba zai iya completing dina ba sai ke ce kika iya. Kin gane banbancin?” Ya kamo ta yana dawo da ita cinyarsa, ya dora kansa ya wuyanta yace “ga kuma babies zaki bamu, abinda Hussain ba zai taba iyawa ba. Kuma bara kiji, kamar yadda nayi defending Hussain a gabanki haka zanyi defending dinki a gaban Hussain idan ya taba ki because you are my precious wife”. Tayi kokarin tashi ya dake riketa, “Please ki ce min kin hakura komai ya wuce kinji? In ba haka ba tuwon nan ba zai iya wucewa cikina ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button