TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai ta juya gurin drivern da fuskar tausayi tana ta shashshafa pockets dinta “I can’t find it. It must have been stolen at school” ya juyo yana kallonta sannan ya kawo hannu kamar zai taba ta yace “let me help you check. Da azama ta rike hannun daya miko, idanuwa a waje, sai ya kawo daya hannun, Sumayya tayi saurin rike shi shima. Abin duk ya faru ne in seconds. A take kuma Ruqayyah ta bude baki da niyyar zunduma ihu, sai Sumayya ta saka hannu ta rufe bakin tana girgiza mata kai sannan ta juya tana kallon driver din tace “please, please sir, we are sorry, let me go and get you the money”

Sai ya zare hannayensa daga nasu yana kallon Ruqayyah yace “ki bata hamsin din jikin ki sai ta karbo wata hamsin din ta kara akai” sai tsoron fuskarsu ya juye zuwa mamaki. Ya daga kafada yace “I might not be hausa, but ina jin hausa kamar jakin kano, dan haka you picked the wrong target” ya bude musu kofar motar yace “get out of my car. Da nayi niyyar ganin karshen drama dinki, but naji tausayin twin sister dinki dan naga kamar ita ta gari ce” a salube Sumayya ta fito daga motar, Ruqayyah kuma ta fito tana kumbura baki sannan ta juya tana kallon sa ta rike kugu tace “aikin banza aikin wofi, dan kana jin hausa kuma sai me? Dan kaji abinda muka ce sai me? Naira darinka din banza, drivern taxi kawai”

Sumayya ta sunkuyo ta window tace “dan girman Allah kayi hakuri. Ni ka tsaya ma dan Allah in karbo maka kudinka a cikin gida, ta boye hamsin din kuma nasan ba bani zata yi ba” ya juya hannun sa yace “ki barshi kawai. Na bar miki, ita ma na bar mata hamsin din tayi arziki da ita. Sannan ki fada a gida a kara muku kudin mota in ba haka ba wata rana zaku samu wanda zai daki kudinsa. Sannan ki saka ido akan twin sister dinki, bata da kirki” ta gyada kanta da sauri yayinda Ruqayyah take neman irin zagin da zata yi masa, da sauri sumayya tace “dan Allah kar ka kulata” ya kalli Ruqayyah yana tayar da motarsa yace “I will not, am not her mate” daga nan yayi tafiyar sa.

Ruqayyah ce ta fara shiga gidan su a fusace kamar zata tashi sama. Inna Ade tana gaban murhu tana zubawa yan samarinta abinci wadanda suma dawowarsu kenan daga tasu makarantar.

Duk da cewa daga Ade har Yusufa basuyi karatun boko ba hakan bai hana su saka nasu yayanba, amma sai sun tabbatar cewa sunyi sauka kuma sunyi hadda. Hatta karamin su zunnur yayi hadda, duk iskancin Ruqayyah babu ayar da zaka bude mata ba tare da ta karanta maka ba. Bayan Alqur’ani kuma sun san sauran littattafan addini.

Bata ko kalli inda suke ba ta wuce su da sauri tayi hanyar dakinsu. Suleiman yace “kububuwa! yau kuma wanne mai tsautsayin ne yayi wasa da jelar damisa?” Zunnur ya kwashe da dariya. Inna Ade tace “Allah yasa ta jiyo ku, in ta kama ku tana jibga babu wanda zan ceta” Sumayya ta shigo da sallama, ta zarce kan baranda ta ajiye jakarta da robar abincin su sannan ta dawo inda suke ta gaishe da Inna Ade, Suleiman yace “wa ya taba Rukee ne yau” Sumayya tace “ina ruwanka? Bana son tsegumi” daga nan babu wanda ya kuma tambayarta dan sun san babu wanda zai samu amsa, sai dai ita kanta bata iya bin Ruqayyah zuwa daki ba sai tayi sallar ta anan sannan ta debi ruwa ta fara wanke musu uniform dinsu wanda zunnur ta aika ya dauko na Ruqayyah, sai data gama sannan ta daukar musu abincin su ta shigar musu dashi daki, tasan dai zuwa lokacin Ruqayyah ta sauko, dama ita saurin hawa ne da ita da kuma saurin sauka.

Ta tarar da ita a kwance tana karanta littafinta na makaranta. Ta zauna ta bude shinkafa da miyar da akayi har da yankakken salak a sama. Rukayya ta mike zaune tare da karbar chokali a hannun sumayya suka fara ci babu wanda yayi magana, sai da suka kusa gamawa sannan Ruqayyah tace a hankali “duk laifin Baba ne” Sumayya ta dago kai cikin rashin fahimta tace “laifin baba kuma? Menene laifin nasa? Shinkafar ko miyar ko kuma salak din?” Ruqayyah tace “talauci. Talaucin da muke ciki. Shine ai yake da alhakin kula damu, shi yake da alhakin nema mana abinda duk muke bukata a rayuwa amma kuma ya gaza, ya gaza sauke abinda yake dole ballantana abinda yake ganin ba dole bane ba” sumayya tace “kina da hankali kuwa Ruqayyah? Kin manta Allah? Ina karatun ki ya tafi? Shin arziki da rashinsa ba duk na Allah bane ba” Ruqayyah ta ajiye spoon din hannunta tace “Allah ba zai taba taimakon wanda ba ya taimakon kansa ba. Allah ba zai taba baka abu in baka tashi ka nema ba” Sumayya tace “amma kuwa in zaki yiwa Baba adalci ke kanki kinsan yana neman ai. Kinga yadda hannun Baba yake kuwa? Kanta ce fa a hannunsa saboda tsabar leburancin da yake yi. Shine aikin labura shine gini, har dako fa baba yi yake yi, kuma duk dan mu yake yi dan muci abinci muyi suttura muje makaranta. Tunda muke bamu taba kwana da yunwa ba, shin ba zamu gode Allah ba? Shinkafa muke ci da rana, gidajen masu hali irin na Baba nawa ne suke samun shinkafa a sati? Jiya fa ina jin Inna ade taji kina complain kin gaji da cin mai da yaji shine fa ta karbo wankau tayi na tabbatar kudin da aka bata shine ta siyo kayan miya da salak din nan tayi mana. Kuma duk dan kar muga gazawar sune a matsayin su na iyayen mu. Kar ki zama butulu mana”

Duk maganar da Sumayya tayi abinda Ruqayyah taji kawai shine kalmar butulu, “nice butulun ko? Ni zaki kira da butulu ko? To ki jira, in dai nice muna nan dake zaki ga nayi kudi. Gabaki daya gidan nan sai na saka an rushe shi anyi mana sabo, an zuba mana kayan alatu irin na gidajen masu kudi. Inna Ade sai ta manta da cewa ta taba yin wani abu wai shi wankau ballantana har a goranta min a saboda shi” Sumayya tace “oh oh, Inna Aden ce zata yi miki gori? Kenan biyanta kike nufin zakiyi na hidimar da tayi dake? Duk kudin da zakiyi Ruqayyah kin isa ki biya iyayenki wahalar da suka sha a kanki? Ballantana ma baki da tabbas din zaki yi kudin”

Nan take rigima ta kuma kachamewa. Inna Ade ta shigo ta tsaya tana kallonsu. “Ya ilahi, yaran nan ko hanjin junan su suke gani ne ni ban sani ba? Ba yanzu kuka gama wani fadan ba har kun sake wani? Kuma in an tambaye ku me ya hada ku ba zaku fada ba ballantana a sulhunta ku?” Ruqayyah ta mike zata fita daga dakin tana kunkuni. Inna Ade ta jawo hannunta “ke Ruqayyah ban hanaki in ana miki magana ki fita ki bawa mutane guri ba? Wato bama zaki tsaya kiji abinda za’a gaya miki ba ballantana kiyi aiki dashi ko?” Sumayya tace “kiyi hakuri Inna” Inna tace “ke ce bakinta? Ita bata da bakin magana ne?” A hankali Ruqayyah tace “Allah ya baki hakuri” Inna Ade ta sake ta ta fita daga dakin zuciyarta babu dadi.

Sai da suka yi sallar laasar suka yi wanka suka shirya sannan suka fito tsakar gida, yau thursday dan haka masu zuwa daukan karatu basu shigo ba sai Ruqayyah ta dauki tsintsiya ita kuma Sumayya ta harhada kayan wanke wanke suka fara gyaran gidan. Suna gamawa Sumayya ta hada wuta ta dora tuwon dare Ruqayyah kuma ta dauko dutsen guga ta hada wuta ta fara goge musu kayan gugar su daya taru. A lokacin Inna Ade ta rufe Alqur’anin da yake gabanta tana karantawa tunda tayi laasar, ta shimfida tabarma kusa da inda Ruqayyah take guga ta zauna. Kamar hadin baki sai ga Sulaiman ya shigo tare da Zunnur, suka zauna suka gaishe da Inna Ade suma bata labarin shagon da suke zuwa koyon dinki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button