TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta bata rai tana kara kwanciya a jikinsa tace “tuwon ma babu dadi ai” ya jawo plate din yace “me ya same shi?” Tace “har na shiga kitchen din zan fara girkin kuma amai ya hanani, bana son mixed kamshin abubuwan girki, shine na barwa yaran nan suyi kuma gashi bai yi dadi ba” ya ture plate din yana cewa “it is okay, bara in samo mana wani abun ko a gurin aunty ne” tace “aunty kuma? Kar ka takura mata mana” ya mikar da ita tsaye shima yana mikewa yace “no, babu wani takura ai tasan baki da lafiya, daga nan ma sai ce ta samo mana cook mai tsafta sosai tunda dai babies sun hana maman su girki” ya karasa yana tsokanar ta sannan ya fita, ta zauna tana jin kalmar maman babies tana bata mata rai, sai kace ita ce Inna Ade da ake cewa uwar biyu.

Sumayya bayan ta shiga gida su Inna suka yi ta mamakin ganin ta haka da sassafe, sai tace musu kawai tayi kewar gida ne shi yasa ta dawo, amma Inna Ade ta lura da damuwa a fuskarta. Sai data bari ta shiga daki tana gyara kayanta sannan ta bita ta zauna tace “ya kika baro su Ruqayyah? Jiya da dare da muka ganta naga tayi girma sosai, kamar hankalin ta a kwance yake ko? Bata da damuwa ko?” Sumayya ta ajiye kayan hannunta ta dawo kusa da Inna Ade ta zauna tace “bana jin Ruqayyah tana da damuwa Inna, ki kwantar da hankalin ki, mijinta da surukan ta suna da kirki sosai kuma suna son ta sosai” sai kuma ta dan yi shiru idanunta a kasa, Inna Ade tace “sai dai kuma me? Akwai magana a bakin ki ki gaya min mana wani abun ya faru ne?” Sumayya tace “kawai dai ina tsoro ne Inna, kin san halin Ruqayyah tun tana gidan nan, yanzu kuma tayi aure ga kuma irin gidan da tayi auren a ciki, cikin yan kwanakin nan da auren nata har idanunta sun kara budewa sosai, ta kara chanjawa sosai, ina tsoron nan gaba kar ta kauce hanyar da kika dora mu akai Inna, so nake kiyi tayi mata addu’a Inna” Inna Ade tayi ajjiyar zuciya tace “ko sau daya ban taba cire wannan tunanin daga zuciyata ba Sumayya, kullum ina yi muku addu’a gabaki dayan ku kullum dare sai na tashi nayi muku addu’a neman tsari daga shaidan, mutum da kuma aljan. Kuma na tabbatar ubangiji ba zai jiyar da addu’a ta ab saboda yayi alƙawarin amsar addu’ar uwa akan ƴaƴanta. In sha Allah yar uwarki ba zata tabe ba. Xan kara wata addu’ar akan wacce already nake yi kullum.

Sumayya taji dadi kuma taji hankalin ta ya dan kwanta, tasan babu abinda addu’a ta bari dan karfin addu’a yakan iya chanza kaddarar mutum gabaki daya.

Cikin kwana biyu Ruqayyah ta kuma dawo da mijinta gare ta, ta kuma fara shiga cikin yan uwansa kamar yadda Minal ta bata shawara. Idan ya fita itama sai ta shirya ta tafi part din aunty tayi zamanta acan, ba zata dawo ba sai yayi mata waya yace gashi nan zuwa sannan zata debar musu abinci ta tafi can ta kuma shirya tayi masa kwalliya kafin ya dawo. Wannan yasa shima ya wanke zuciyarsa gaba ki daya akan waccan maganar yake enjoying matarsa.

Motocin su da Hussain ya siya musu ita da Fatima sun iso kuma Ruqayyah tayi murna sosai dan bata dauka haka motar ta hadu ba sai da tagan ta kiri kiri sannan ta kuma fahimtarta. Hassan ne yayi suggesting ya kamata ta shirya taje gida ta nuna musu motar dan tun da suka dawo bata je gidan ba. Dan haka ta dauki kayan tsarabarsu sannan shima kuma ya dauki kudi masu kauri ya bata yace ta kai musu, sai ya hada ta da driver yace ya kaita tunda bata fara koyon motar ba tukuna. Dan haka hankalin ta kwance ta tafi a zuciyarta tana plan din daga can zata biya ta gidan su Minal suje gurin malamin nan mai addu’a.

Tana shiga soron gidan taga Adam yana fitowa daga dakin su Sulaiman. Yana shafa kai yace “welcome Madam” ta watsa masa harara tare da jan dogon tsaki ta wuce cikin gidan sai yayi murmushi kawai ya fita. Tana shiga Zunnur yana ta murnar ganinta amma ita da fada tafara “me wancan kedarin yake yi a gidan nan? Duk ya cika masa gida da warin karti” Sumayya da take daki suna waya da Adam yana gaya mata ya gama zai tafi ta fito tana kashe wayar ta nuna ta “kar ki kuma, wallahi Ruqayyah ki fita daga idona na gaya miki” Ruqayyah tace “in na kuma nace sai me? Me zakiyi min? Wallahi sai ya daina zuwa gidan nan ai badan irin su Hassan ya sai gidan ba” Sumayya tace “to maza, yi mana gorin cewa mijinki ne ya siya mana gida, dan ma dai ba rokar sa mukayi ba kuma daya siya din ba ke ya siya wa ba Baba ya siya wa dan haka baki da iko da gidan” Ruqayyah tace “amma dai saboda wa ya siya? Saboda ni ya siya baby girl amma ina da say akan waye zai ke shiga gidan nan yana fita kuma wancan katon kedarin baya daga cikin su”

Inna data rike baki tana kallon su tace “to kuyi dammara ku daku a gaban kannen ku kunji. Akan saurayi zaki yi fada da yar uwarki Sumayya? Ke kuma akan wata akida taki ta daban zaki yiwa yar uwarki damu iyayenki gori cews mijin ki ya siya mana gida? Ruqayyah? Har kin kai haka? Har kin yi girman da zaki yi mana gorin gida Ruqayyah?” Ruqayyah ta zauna taa magana kasa kasa “ni ba gori nake muku ba inna, ni kawai mutumin nan ne bana son yake zuwa gidan nan wallahi. Na tsane shi bana son ganin sa” Sumayya ta bude baki zata yi magana sai kuma ta kalli Inna ta juya ta koma daki tana rufo kofa. Tana ragawa Ruqayyah akan komai amma ta rasa me yasa bata iya raga mata akan Adam. Ko da wasa bata son Adam yaji irin maganganun da Ruqayyah take fada akan sa, babwai dan tana son sa a matsayin saurayi ba sai don tana sonsa a matsayin sa na wanda yayi loosing everything for islam.

Inna ta jima tana yiwa Ruqayyah fadan abinda tayi sannan kuma ta koma yi mata nasiha, daga nan kuma sai suka shiga hira. Su Sulaiman da suka tafi dauko kaya daga mota suka suka dawo suna baje kayan anan tsakiyar palo kowa yana diban nasa. Ruqayyah ta dauko na Baba ta bawa Inna ta ajiye masa sannan ta bata nata itama. Ta ware na Sumayya gefe tace “ita kuma wannan inntaga dama ta fito ta dauka to in kuma tayi fushi in kinyi bakuwa inna ki bayar” Sulaiman yayi dariya yace “babu wanda zai shiga tsakanin ku dan duk wanda ya shiga to kuwa zai ji kunya” duk suka yi dariya amma ita Ruqayyah bata ga abin dariya a cikin fadan su da Sumayya ba, ita bata san me yasa suke daukan lamarin Adam for granted ba. This is very serious issue amma su suna dariya akai.

Sai daga baya Inna da kanta ta aika aka kirawo mata Sumayya ta fito suka cigaba da hirar si tare, Ruqayyah tana ta nuna musu hotunan guraren da suka je da kuma abubuwan da suka yi, sannan tace “ohh ni na manta ma, ga mota can Hussain ya bani kyauta. Tana waje” sai murna da ihu. Suka fita waje gabaki daya har da Inna, suna ta gani suna saka albarka, Ruqayyah ta saka drivern ya dauke su ya dan zaga dasu unguwa sannan ya dawo dasu.

Anan Ruqayyah ta kusan yini har laasar, sai da Baba ya dawo ta gaishe shi sannan ta fara shirin tafiya. Inna tace “da wuri haka zaki tafi?” Tace “yace kar in kai dare ne, yace in koma gida kafin ya dawo kuma karfe biyar yake dawowa” Inna Ade ta gyada kai tana jin dadin yadda Ruqayyah take wa mijinta biyayya. Ta dauko kudin da Hassan ya bayar ta ajiye musu sannan tayi musu sallama suka raka ta har bakin mota, Baba yana sakawa motar albarka.

Suna fita daga layin ta saka driver ya dauke kan motar zuwa gidan su Minal, ta dauko waya ta kira ta ta gaya mata gasu nan zuwa dan haka suna zuwa ta fito ta shiga motar suka tafi. Basuyi wata tafiya mai nisa ba suka zo gidan malamin, sai Ruqayyah tayi mamakin ganin hadadden gida ba irin gidan malam Shehu ba dan tasa ran ganin dan karamin gida mai dakin almajirai a soro da kuma malami a zaune akan buzu a kofar gidan amma sai taga an bude musu gate sun shiga hadadden gida drive in, suka fito daga motar kamar zasu shiga cikin gidan sai Minal ta kira wani a gurin tace a gaya wa Malam sunzo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button