TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sannan ta juya gurin Ruqayyah tace “dama tun ranar da muka yi magana dake na gaya masa ta WhatsApp cewa zamu zo” Ruqayyah tayi dariya “wai kina nufin malamin ne yace WhatsApp?” Minal tace “to me za’a fasa, na gaya miki fa ba irin wadanda kike jin labarin su bane ba. Mu shiga ciki zaki kara tabbatar da abinda na gaya miki” suka shiga cikin wani palo suka zauna, Ruqayyah tana ta mamaki “yanzu dama ana samun irin wannan kudin a harkar malinta shine malam Shehu yake zaune a gidan kasa? Duk ilimin sa?” Minal tace “shi ya zaba. Kinga shi fa wannan yan siyasa suna zuwa gurinsa yayi musu addu’ar nasarar zabe, a haka ya gina wannan gidan ya kuma sayi motoci har biyu, ko da yake dayar ance min kyautar ta aka bashi”

Suna nan zaune malamin ya fito, middle age mutum ne mai kamala da komai, ya saka manyan kayan sa da babbar riga hannunsa rike da charbi yana ja ya zauna suka gaishe shi yace “Ruqayyah ko? Amina ta gaya min zaki zo. To madallah Allah yayi albarka. Yanzu mu fara yiwa Annabi salati kafa goma tukunna” suka yi salatin nabiy a tare kafa goma sannan yace su karanto sunayen Allah 99 a tare, suka karanta sai ya jefar da charbin sa a gaban Ruqayyah yace ta miko masa, ta dauko ta miko masa sai ya rike gefe da gefen inda ta taba ya kirga adadin beats din da suke gurin sannan ya kalle ta yayi murmushi yace

“Amina ta gaya min bukatar ki, dukiya ce ta kanin mijinki ke kuma a ranki kina so ta zama ta mijin ki. Shine kike so ayi miki addu’a Allah yayi miki jagora akan wannan kudiri naki” Ruqayyah ta gyada kai tace “haka ne”

Yace “to ai malama Ruqayyah ni dai abinda na gani a tattare dake shine arziki, naga dukiya fiye da wadda kike saka ran samu, na ga budi, indai kudi ne wadanda ake kira da kudi na gansu. Amma kuma naga kadaici. Zabi ya rage naki Ruqayyah, nan gaba kadan wata damazata same ki wadda zata barki da zabi guda biyu, ke da kanki zaki zabi rayuwa cikin dauka marar iyaka ko kuma rayuwa a karkashin masu daula marar iyaka. Zabi ya rage naki. Idan kin je gurin zaki fahimci abinda na gaya miki kuma sai a lokacin zaki biya ni kudin aikina da kanki ba tare da wani ya tuna miki ba” Ruqayyah ta mike da sauri tana jin uneasiness, wannan ai duba yake yi, malamin duba ne Minal ta kawo ta gurinsa. Ba tare da tace komai ba ta yi hanyar waje, tana zuwa bakin kofa yace “Allah ya sauke ki lafiya Ruqayyah. Ki gaishe min da Hassan da Hussainin da zaki haifa”.

Babu shiri ta karasa fita tana hada hanya, tana shiga mota bata jira Minal ba tace da drivern su tafi, gabanta yana ta faduwa amma maganganun malamin suna ranta kamar yayi zane akan dutse.

Sunanan, malaman tsibbu da yan duba da suke yaudarar mutane da sunayen Allah da ayoyin Alqur’ani. Su ja su fassara maka amma su jaka ku aikata shirka tare. Mu kula, mu kiyaye, mu ji tsoron Allah.

Me zaki nema a gurin ubangiji wanda ke da kanki ba zaki iya tambayarsa da kanki ba bayan shine yace yafi jijiyoyin wuyan mu kusan ci da mu? Wacce addu’a ce da ba zaki iya yiwa kanki ko ki gayawa mahaifiyarki in tana da rai tayi miki ba har sai kinje gurin wani mai amsa sunan malami yayi miki?

Wannan littafin na siyarwa ne, in kin ganshi a wani gurin to na sata ne. In kina so ki karanta halaliyar ki to kiyi min magana ta wannan number din 08067081020The Twins

Sai da ta kusan zuwa gida sannan kiran Minal ya shigo mata, tana dagawa ta fara yi mata bala’i “shine dan kuturun wulakanci zaki tafi ki barni ko? Wato ke ga mai mota ko? Laifi nane ni da na dauko ki na kawo ki inda za’a taimaka miki. Kuma kinyi da yar halak in dai ni Amina kika yiwa haka wallahi zaki gane kim wulakanta ni a gaban mutane” Ruqayyah tayi ajjiyar zuciya tace “kiyi hakuri Minal, wallahi ba zan iya bane ba tsoro nake ji, kema ki daina zuwa gurin sa duba yake yi. Ko waye ya gaya mishi ina da ciki har zai gaya min abinda zan haifa? Ki bashi hakuri kawai ki ce ba zan iya ba” ga mamakin ta sai taji Minal tayi dariya tace “bai ji haushi ba ai. Yace in gaya miki kiyi kokari ki aiko masa da date of birth na Hassan da Hussain da kuma na Fatima, rana da wata da shekara, da su za’a yi amfani gurin yi miki adduar” Ruqayyah ta girgiza kai tace “ni fa babu abinda zan bashi, ban sani ba kuma ko na sani ba zan gaya masa ba. Ke da jin wannan kinsan malamin tsibbu ne irin su kuma sunfi boka hadari” Minal tace “if you say so bazan yi miki musu ba, ni dai nasan bai bani komai na binne ba kuma bai bani komai na barbada ba. Dan haka ni banga tsibbu a cikin abinda yake yi ba, besides, burika na suna ta cika tunda yanzu gashi yayi min albishir cewa Alhaji Ahmed ya kusa aikoda kudin aurena, daga na shiga gidan na haifa masa yaya shikenan gidan ya dawo hannu na matar sa sai dai ta bini da kallo kawai” suka yi dariya tare, Ruqayyah tace “Allah ya bada saa, amma nikan ba dani ba” suka yi sallama Ruqayyah ta karasa gida.

A compound din ta hango Hassan da Hussain suna tsaye suna ta magana suna dariya, daga gani suna cikin murna ne. Tana zuwa Hussain yace “yauwa gata nan ta karaso, shawara nake bashi cewa ya ke turo ki kullum kina zuwa kina gaishe ni ko Allah zai taiamake ku ku haifi yaya masu kama da ni, kin dan ni din fa kyakykyawa ne” ta tabe baki tace “Allah ko? Ni dai ban gani ba” yace “ohh baki gani ba? Zo muje in nuna miki” ya wuce gaba zuwa part dinsa Hassan yana binsa a baya yana cewa “kar kasa matata a cikin maganar nan walllahi ranka zai baci. In ka sake kayi forcing dinta tace ka fini kyau ko? Ni kadai nasan me zanyi maka” suka shiga palon Hussain, Ruqayyah ta tsaya daga bakin kofa dan bata taba shiga gurin ba sai yau. Ya juyo yana kallonta yace “common in, ki fadi kuma tsakanin ki da Allah waye ya cinye hoton nan” ta shigo tana kallon hoton da yake nuna wa.

Su biyu ne a hoton, kamar kuma a wannan palon akayi saboda taga kujerar irin ta palon ce, Hussain yana zaune akan kujera ya harde kafafunsa fuskarsa da murmushin da yake bayyana dimple dinsa, Hassan a tsaye a bayan sa, ya dora guiwar hannunsa akan kafadar Hussain looking as serious as ever. Ta danyi murmushi tana rarraba ido tsakanin fuskokin su, ita sai yanzu take kara tabbatar da kamannin da suke yi sai dai banbancin fatarsu tana boye kamannin nasu. Ta jiya tana kallon Hassan ya bata rai yace “don’t say it” tayi dariya tana kama hannunsa “me zance? Ai ko makaho ya shafa yasan mijina yafi na kowa kyau” Hussain yace “kin dai so kanki kawai” ta dauke idonta daga kan hoton tana kallonsa yace “ka manta da maganar hausawa da suka ce so duka so ne amma son kai yafi?” Hassan ya zagayo tabayanta ya tsaya suka jeru shima yana kallon hoton yace “gobe za’a kawo mana namu, this is just a sample. Hussain ne ya saka aka yi mana wai za’a kafe a duk kamfanonin sa dan kowaya shiga gurin yasan su waye masu gurin” ya karasa maganar yana dora habarsa a kafadarta. “Kin san halin kanin naki”. Ta dan yi murmushi a ranta tace “kai zaka fada amma ni ban isa in fada ba sai aji haushi a gaya min magana”.

Bayan sun koma part dinsu ne Aunty ta aiko musu da abincin dare da kuma sakon cewa cook dinsu zata fara zuwa gobe. Suka zauna suka ci abinci yana tambayar ta ya mutanen gidan su suke, tana yi masa bayani amma hankalin ta yana kan maganganun wannan mai duban, yace dama zata same ta wadda zata iya zabar abu daya cikin biyu, ko dai ta zabi yin kudi fiye da kudin da take saka rai ko kuma ta zabi xama a karkashin masu kudi, bata bukatar amsa tasan idan lokacin yazo wanne choice din zata dauka, tabbas tasan kudi zata dauka dan shine babban burinta a duniya amma kuma abinda bata sani ba shine yadda zabin zai zo mata, yace zata yi rayuwar kadaici, wanne irin kadaici yake nufi? Indai kuwa har zata yi kudi to kuwa ai babu zancen kadaici saboda tasan mutane kamar magnet suke da kudi, duk wanda yake da kudi shine yake da mutane, misali Hussain da Fatima kullum gidan su a cike yake da mutane saboda suna da kudi, ita ma in ta samu irin wannan haka nata gidan zai ke cika irin nasu. To kuwa in dai abinda ya fada gaskiya ne then bata bukatar bata lokacin ta gurin korar Fatima ko raba Hassan da Hussain ko duk wani abu da yake on agenda din ta. But ita kanta tasan ba komai da yan duba suka fada ne yake zama gaskiya ba, kuma tasan yadda da abinda suka fada shirka ne saboda babu wanda yasan abinda gobe take tafe da shi sai Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button