TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari weekend, haka kawai Hassan ya tashi da aikin gyaran gida, sai yau ya gama kwashe kayansa daga tsohon dakinsa ya kuma shirya komai tsaf a dakinsa na yanzu. Ita dai tana ta binsa a baya tana yi masa hira har ya gama sannan suka yi wanka suka zauna breakfast. Bayan sum gama ne ya dauko littafi karami da biro ya zaunar da ita ya rubuta wasu adadin kudi a jiki yace mata “jiya anyi mana salary, wannan shine salary na” ta kalli numbers din mentally tana calculating abinda zata yi dasu ranar da tayi kudin da take saka rai, sannan ta kirkiro murmushi tace “masha Allah, Allah ya sa musu albarka” yayi murmushi yana jin dadi yace “ameen Precious. Yanzu kinga lissafi na shine, 50% zan ajiye, su zanke tara mana na ginin gidan mu” sai kuma ya shafa kai yana kallonta da murmushi a fuskarsa yace “though, ga babies kuma a hanya, but we can manage kudin su isa har hidimar babies din” ya cigaba da rubutu yace “20% zamu siya daily needs din mu, komai na bukatar gida da kuma personal needs din mu for a month, 10% zamu kaiwa Baba, 10% percent kuma ina so in bude miki account sai kike ajiye wa kema duk sanda kike bukatar wani abu sai dai kawai ki dauka ba sai kin tambaye ni ba. Ko zaki yiwa wani kyauta ko dai wani abu mai muhimmanci haka, kamar harkar makarantar su Zunnur zaki yi musu out of your pocket. Ragowar 10% din kuma sai mu ajiye a gida in case of emergency. Ya kika gani? Lissafin yayi?” Ta cire tagumin da tayi tun da ya fara lissafin sannan tayi murmushi tace “gaskiya baiyi ba, kusan komai a kaina zai kare? Kai kuma fa? Ni banji ka ware wasu kudade kace naka ba ne ba” ya dago kai yana kallon ta fuskarsa cike da yana yin da yake nuna yaji dadin maganar ta har cikin zuciyarsa yace “don’t worry about me, kin manta all that 50% yana gurina? Sannan kuma already ina da kudade a account dina zan iya dauka inyi duk bukatu na. Ke dai kawai kiyi managing wanda zan baki. Kar kike siyan unnecessary things. Kin san yadda nake siyayya ta?” Ta girgiza kai yace “duk abinda na dauka zan siya sai in tambayi kaina “do I really need this? Can I live comfortably without this? Ko kuma da akwai wani abu da nake bukata more than this? Idan har na tabbatar bana buƙatar abin sai in ajiye shi inyi gaba. That is how I avoid unnecessary spendings” tayi dariya tace “nima na koya to, haka zan ke yi” ya shafa fuskarta yace “good girl” sai ya mike tsaye yana cewa “monday sai muje a bude miki account din ko? Bara in shirya in an jima zan kai su Hussain airport” tace “airport? Ina zasu je?” Ya juyo yana kallonta yace “Thailand zasu je, zai ji signing wani contract ne da wani kamfanin shinkafa a can” ya juya ya shiga ya barta da sakakken baki “kuturin kare! Wato mijin wata yana can yana daukan matarsa tana rakashi business kasar waje ni nawa yana lissafa min albashin sa a takarda?” Sai taji duk ranta ya baci, taji ta raina albashin nasa gaba ki daya ko da kuwa gabadayan sa zai bata.
Tana nan zaune har ya fito, yana daura agogo yana cewa “so nake in shiga gidan Aunty muyi rigima da ita, dama na gaya mata aure ba zai zaunar da Hussain a gida ba, in yayi auren ma daukan matar zai ke yi suna tafiya tare” sai kuma ya lura da chanjawar yanayin ta, yace “what’s wrong?” Ta dago kai tana kallonsa, tace “babu komai, kawai dai zanyi missing din su ne” yayi mata murmushi sannan ya durkusa yayi kissing goshinta yace “kar ki damu, I will be here to keep you occupied” ya kashe mata ido, tadan dungure masa kai kadan ta juya baya tare da kwanciya akan kujera. Ya tashi yana dariya yace “sai na dawo. Please ki rubuta list din duk abinda muke bukata a gida kafin na dawo. Make sure you include everything. Ni kuma in na dawo zan biya in kaiwa Baba nashi kudin”.
Yana fita taja tsaki. “Ni bansan wanne iyayin ne ma yasa Hussain ba zai dauki driver ya kaisu airport din ba sai yasa Hassan ya kai su sai kace wani yaron su” ta sake tsaki tana jin bacin ranta yana karuwa, sai kuma ta mike ta shiga daki ta dauko hijab ta saka ta fita. A part din Aunty ta same su suna ta magana suna dariya har da Fatima, ta gaishe da Aunty da take rike da hannun Fatima sannan ta gaishe da Hussain tare da yi masa fatan alkhairi. Tace da Fatima “yanzu kuma shine zaku tafi ko sallama babu?” Fatima tayi murmushi tace “ban san baki san da tafiyar ba ai, tun jiya nake ta zuba idon ganin kin shiga munyi sallama” Ruqayyah ta juya ido, wato ita ba zata shiga tayi mata sallama ba saboda ita yar sarki ce…..
Lokaci ya cigaba da tafiya, Ruqayyah ta lullube kanta da barguna na mutum mai kirki ta yadda a gurin Hassan ta zama the best wife he could have ever asked for, sometimes tana dan kwace mata ta dan saki baki haka ko tadan nuna halin ta kadan amma sai tayi saurin basarwa, shi kuma in hakan ta faru yana dangana hakan ne da maganar da Baba ya gaya masa na cewa Ruqayyah tana da zuciya tana kuma da saurin fada. Dai ya dage wajen ganin duk abinda tayi ba dai dai ba sai ya nuna mata ya kuma gyara mata ya gaya mata wanda zata yi dai dai din. Tsakanin ta da mutanen gidan kuma dai mutunta juna, duk da ita ta sani suma kuma sun san cewa ta sani sunfi son Fatima akanta saboda Fatima ta fita sakin jiki da su kuma ta fita kyauta. A tsakanin lokacin ne kuma Sumayya da Adam suka samu admission a tare suka fara zuwa makaranta, Hussain ne ya dauki nauyin komai na Adam, Baba kuma yabiya na Sumayya duk da cewa Adam ya so ya biya mata amma pride din Baba ya hana ya barshi ya biya din. Shigar su makaranta tare ta kara shakuwa a tsakanin su ta yadda har sai da Inna tayi wa Sumayya magana kan cewa ya kamata ta rage alakar ta da Adam saboda shaidan ya kan iya shiga even the most purest of hearts, wannan ya dan taka musu birki kadan, amma kuma bai rage musu kaunar junan su ba ko da da kwayar zarra. Sai dai har yanzu bai fito officially neman aurenta ba saboda bai san ta inda zai fara ba, bai kuma san ko za’a bashi ita da considering ko shi waye, duk da dai bai taba ganin kyama ko kiyayya a idon Baba ba.
Bangaren Hussain da Fatima soyayya sai abinda ta karu, amma kuma even after months da bikin su babu ciki, abin yana ransu duk da cewa a tsakanin su babu wanda ya taba furtawa dan uwansa damuwarsa akan hakan, sai dai kullum suka zauna sai sunyi zancen haihuwa, har list ne dasu na sunayen da zasu saka wa ƴaƴan su, in an samu wani sunan kuma sai a kara sannan a rage wani. Da wahala su zauna tsahon wata daya a Nigeria, kullum Hussain yana tafe harkar neman kudin sa kuma duk inda zai je Fatima tana gefensa.
Ruqayyah ciki ya girma. Tun kafin ya tsufa kusan duk wanda ya santa ya san tagwaye ne a cikin ta kuma babu wanda yayi mamakin hakan saboda daga ita har mijinta duk hakan ne, sai dai duk yadda Hassan yaso ta yarda a duba musu gender din babies din kin yarda tayi tace babu kyau, amma a cikin zuciyarta tana tsoron abinda zata gani ne, idan maza ne to maganar wannan mutumin mai duban nan zata tabbata kenan idan kuma mata ne to sauran maganar sa ma zata kasance karya ce kenan kuma hakan yana nufin dole ta sake sabon shiri dan ba zata iya cigaba da wannan zaman ba kullum cikin bakin cikin yadda Hussain da Fatima suke bushasha da kudi ita kuwa tana faman lissafi.