TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Have you taken your pills today?”
Sai ta saka hannu ta cire ta ta yar. Ta jawo drawer din da birth control pills dinta suke ta kwashe su gabaki daya taje ta zuba a waste bin. In yasan wata ai bai san wata ba. Ta kashe fitilar dakin ta kwanta, tana jin haushin sa a ranta, har da gori ma yayi mata wai ya siya wa baban ta gida.
Tana jinsa ya shigo dakin, ya jera mata yayan ta a kan gado, yayi musu addu’a ya shafa musu sannan ya tashi ya fita. Ta juyo tana kallon yaran, sai kuma tayi murmushi, dolen sa yayan ta ne yaya kuma dole sai uwarsu.
And yes. Hussain da Fatima sunje sunga fertility doctor a Washington DC. Doctor din yana kallonsu yana murmushi yace “one year you said?” Hussain ya daga kafada yana kallon Fatima da take twisting hannunta yace “she insisted sai munzo” doctor din ya juya yana kallon ta yace “am sure babu wani abu madam, but zamuyi running some tests dan mu tabbatar babu komai din. Pregnancy takes longer to get in some couples than in others ba tare da wani dalili ba”.
Daga nan aka fara yi musu tests, a dauki jini a dauki fitsari, vaginal swab, sperm samples da sauransu. Kwanan su biyu ana ta faman abu daya, Hussain dai yana zuwa ne saboda ya farantawa Fatima amma shi a ransa yasan babu mai bashi haihuwa sai Allah. A week after aka kira su karbar result, suka zauna kamar yadda suka zauna last week, Fatima looking very nervous while Hussain is relaxed yana ta tsokanar ta. Doctor din shima ya dan tsokane ta kadan sannan yace “results dinku gasu nan sun fito gabaki daya, amma babu wani problem da muka gani, gabaki dayan ku lafiya lau kuke kuma zaku iya samun haihuwa a kowanne lokaci. Abinda zamu iya yi muku na taimako kawai shine zamu baku magunguna da zasu yi boosting fertility dinku sannan zamu baku shawarwarin da zasu taimaka muku sosai da kuma diet din da shima zai taimaka wajen boosting fertility din. Most importantly kuma ke Madam dole kiyi relaxing ki kwantar da hankalin ki saboda anxiety, rashin kwanciyar hankali, yawan tunani da damuwa duk suna affecting fertility din mace” Hussain ya juya yana kallon Fatima tare da kama kunnensa daya yace “kina dai ji ko? To babu ruwa na” tayi murmushi.
Aka gama yi musu bayanin duk da za’a yi musu, aka basu drugs dinsu aka sallame su. A hanya Hussain ya tasa Fatima da tsokana. “Sai kin shirya fa, tunda dai kinji sunce yawan yin abin nan yana kara chances, to double za’a ke yi yanzu” ta harare shi “to ayi double din ma mana, kasan dai ai bana jin tsoro ko?” Yace “kar ki cika baki fa? Sai kuma anzo gurin kuma ki fara neman a tausaya miki. To babu tausayi yanzu yarinya in…..” Ta rufe ido “ka daina dan Allah kunyar ka nake ji fa” yayi dariya “to zamu karasa maganar a turaka”.
Washegari da safe karar wayarsa ce ta tashe shi, ya daga cikin muryar bacci yana cewa “Hello. Who is on the line please?” Daga can aka yi masa bayanin cewa doctor din daya gansu ne yake son ya dawo shi kadai, akwai maganar da za’a yi masa. Ya ajiye wayar yana danyin tsaki, ya koma ya kwanta yana kara jawo Fatima jikinsa sai kuma ya mike, ya sake tsaki sannan ya shiga toilet. Mintuna kadan har ya fito, motsinsa ya tashe ta ta dago kai tana kallonsa “ina zaka je?” Yana daura agogo yace “zan dan fita, ki koma baccin ki yanzu zan dawo. Zan yi musu magana su kawo miki breakfast” ta tura baki “bayan ka hana ni bacci da dare ba dole in rama ba yanzu? Ba sai sun kawo ba dan ni banga ranar tashi na daga wannan baccin ba. In ka dawo ka taho mana da shi” yayi murmushi, “better eat something Madam, kar in dawo kuma kice ke ga zance ga magana. Cos da nayi niyyar mu koma Nigeria gobe but yesterday night ta saka na chanja shawara, sai next week zamu koma. Anan za’a yi making baby din” ta dauki pillow ta jefa masa, sannan ta rufe fuskarta da wani pillown.
Direct gurin doctor din ya koma, zuciyarsa tana ta yi masa sake sake iri iri. Doctor ya kalle shi da murmushi yace “kar ka damu da wannan kiran, I hope bamu tayar maka da hankali ba” Hussain yace “it is okay. What’s up?” Doctor yace “result din da aka baku still stands, babu wani chanji. But a cikin gwaje gwajen da muka yi muku munga something da muke tunanin ya kamata ka sani kuma kayi taking action akai. It is just a suspicion Sir, we are not sure. Sai dai in ka yarda zamu tura ka gurin doctor din da zai sake maka wasu tests din for confirmation” Hussain ya gyara zaman sa yace “menene wai doctor, just say it” doctor ya gyara zama yace “we suspect that you have a column cancer”
Yana shiga hotel room din ya bude labulen da sauri, haske ya shigo ya haske dakin. Fatima ta daga kanta tana kifta ido tana adjusting to light din sannan tace cikin muryar bacci “har ka dawo? Ka taho da abincin?” Yace “tashi ki shirya, we are taking the next flight back to Nigeria” ta mike zaune tace “What? Why?” Yace “I said we are taking the next flight back to Nigeria” yanayin muryarsa ya sa ta san da gaske yake, ta san kuma something has happened.
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani guri na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020The Brothers
Cikin mimtuna kadan suka gama hada kayansu, ita dai duk bata yarda da yanayin sa ba tace “wai me ya faru a Nigeria ne? Ko wani ne ya mutu aka gaya maka?” Ya kalle ta yana kokarin kirkirar murmushi yace “babu wanda ya mutu fa, kawai ji nayi ina missing Hassan” ta kalle shi kawai amma a ranta bata yarda da uzurinsa ba tace “Hassan din da kuna haduwa zaku fara rigima? A waya ma ina jin ku kuna yi” yace “mun daina daga yau, daga yau ba zan sake fada da Hassan ba ko ya neme ni da fadan ma cewa zanyi ni bana fada” tayi dariya, shima yayi, at least ta dan ji dadin ganin yayi dariya hakan yana nuna mata ba mutuwar akayi ba, but something is definitely up.
Sai da suka fito sannan suka samu abinci suka ci, har lokacin tana ta yi masa nacin sanin inda yaje da safe kuma me aka ce masa dan tasan abin yana da alaka da wannan tafiyar ta gaggawa amma sai yace mata abokin kasuwancin sa ne kawai ya gani, kuma kawai ji yayi yana son su koma gida. A hanyar airport ya kira Hassan ya gaya masa gasu nan zasu taho yanzu. A airport yaga wani bookshop, kawai sai ya shiga, a cikin jerin book yaga wani diary mai kyau mai girma kuma daga ganin sa zai yi kwari sai ya dauka tare da pen ya biya ya fita. Suna zama a cikin jirgi ya dauka dairy din ya bude front page ta fara rubutu.
Dear Baby…….
Fatima ta leko tana cewa “me kake rubuta wa ne haka?” Ya rufe littafin yana zare mata ido “ke, sirri ne” tayi murmushi “fada min, love letter kake rubuta min?” Yace “in kalaman soyayya zan gaya miki Fatima ba zan rubuta su a takarda ba, zan kalli cikin idonki ne in gaya miki, ko kuma in rada miki a kunnuwan ki” ta bata fuska “to wa kake rubuta wa?” Ya bude littafin ya nuna mata inda ya fara rubutu yace “our baby” tayi dariya tana shafa rubutun tana jin son babyn da ko cikinsa babu. Sai ta gyara zaman ta ta kwantar da kanta a kafadar sa tace “me zaka rubuta masa?” Yace “a letter. Daga yau kullum zan dinga rubuta masa letter har sai ranar da aka haife shi. In ya girma ya iya karatu sai in bashi ya karanta” tace “kullum? Me zaka ke rubuta masa kullum?” Yace “duk abinda nayi a ranar zan bashi labari, maybe a ciki zai dauki wani darasi na rayuwa”.