TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta lumshe idonta a lokacin da jirgin yake dagawa dasu zuwa sararin samaniya, ya bita da kallo har sai daya tabbatar bacci ya dauke ta sannan ya jawo diary din ya cigaba da rubutu.

Dear Baby.
Idan kana tare da littafin nan hakan yana nufin baka tare dani, dan in har ina raye ba zan baka littafi ba zan zauna ne in saka ka a gaba in yi ta baka labarin irin son da nake yi maka. Idan har bana tare da kai, Idan har ban samu naga fuskar ka a duniya ba, ina fatan ka zama yaro na gari kayi aiyukan alkhairi dan in samu damar ganin ka a lahira. A aljanna…………..

Kiran wayar Hussain ce ta tashi Hassan daga bacci, yayi juyi yana kifta idonsa yana jin kansa yana yi masa ciwo saboda baccin da bai samu ya ishe shi ba. Ya dauki wayar “ya akayi?” Hussain yace “wai bacci kake yi? Karfe nawa ne a nan? Nan da 30 minutes zamu taso” Hassan yace “zaku taso kuma? I tot jiya kace min sai next week, what’s up?” Hussain yace “nothing kawai na chanza shawara ne, kawai nayi missing dinka ne” Hassan yayi tsaki “neman magana dai kake yi. Ni ka katse min bacci ka sa kai na zai fara ciwo. Okay sai kun karaso” ya kashe wayar tun kafin Hussain ya bashi amsa, ya koma ya kwanta tare da dora pillow a kansa yana so ya koma bacci amma shi kansa yasan wasa yake yi.

Dama jiya da kyar bacci ya dauke shi saboda abubuwan da suka yi masa yawa akai. Ruqayyah. Ta bashi mamaki ba kadan ba kuma maganganun ta sun taba zuciyarsa ba kadan ba, gidan arziki, you have nothing, wadannan sunfi duk sauran kona masa zuciya. Bai taba tsammani ba in wani ne ma ya gaya masa cewa ida zata fada masa haka to kuwa tabbas ba zai yarda ba. Abu daya daya gano a gurinta shine ta bawa kudi wani babban matsayi a zuciyarta. Wannan wani abu ne da tayi matuƙar kokari gurin boye masa tun haduwar su sai jiya ya fahimta, bayan wannan kuma bai san what other things ta boye masa ba, bai san how many lies ta gaya masa ba.

Ya mike ya shiga toilet ya hada wa kansa ruwa mai zafi yayi wanka wai ko zaiji ya watstsake, ya fito ya kalli dining yaga babu alamar an bude shima, ya kalli dakin Ruqayyah bai ji motsin kowa ba sai ya fito ya tafi gidan Aunty. A palo ya tarar dasu suna ta hayaniya suna ta cin abinci, ya gaishe da Aunty sannan ya ce Khadijah ta zuba masa abinci, Aunty tace “ina Ruqayyah kuma?” Yace “bata jin dadi, ta kwanta kuma bana so in tashe ta” Aunty tayi murmushi tace “ai ko wadannan guntayen yaran aka barta dasu sai sun saka mata ciwo” Safiyya tace “kai Aunty, salihan yara irin wadannan da ko kuka basa yi?” Aunty tace “basa kuka fa, amma duk wanda ya dauke su shine zai yi kuka dan sai sunyi masa duka” Nafisa tace “lafiyar kenan Aunty, duk yaran da kika ga ya zauna shiru to kuwa tabbas bashi da isashshiyar lafiya” Aunty tace “sai kuyi tayi ai, ku da ba’a taba muku yaya” Hassan dai yana jinsu bai tanka ba yana ta murmushi, duk wata magana data shafi gudan ransa yana sonta.

Ya jima a gurin Aunty suna shawarwari akan shirye shiryen bikin Safiyya da Jabir daya gaba to, ga kuma Hassana da tsohon ciki, sannan ga graduation din Khadijah tace sai an shirya mata party. Shi so yayi manemin Khadijah ya fito a hada bikin dana Safiyya a huta amma hakan ba zai samu ba saboda ya tafi karo karatu sai ya dawo za’ayi, kafin nan ta gama service dinta. Sosai yake jim dadin yadda rayuwar kannen nasa take tafiya duk da maraicin uba amma abinda suke samu ko da ace suna da uban ba lallai ne su samu kamar haka ba.

Sai da ya gama zai fita sannan ya fada wa Aunty zancen dawowar su Hussain yau. “daga nan zan dan leka gurin Jabir sannan sai in wuce dauko su” sai yaga jikin Aunty yayi sanyi tace “Allah dai yasa lafiya, Hussain bai taba cancelling trip dinsa ba sai dai in da babban dalili” Hassan ya mike yana cewa “rabu da shi Aunty, kin san halin Hussain, he can be dramatic sometimes, wai missing gida yake yi sai kace wani jariri” Aunty tace “to Allah ya kawo su lafiya. Ai gwara hankalin nasa yake dawowa gida, gwara ya zauna a gida muma mu samu mu ganshi sosai”.

Sai daya biya gurin Jabir suka gama tsare tsaren su na shirin da suke yi zuwa Gombe gaisuwar iyaye, sannan yayi masa sallama ya tafi airport dan ya lokacin isowar su Hussain ya gabato. Bai jima da zuwa ba suka zo. Tun daga kallon farko da yayi wa fuskar Hussain ya fahimci akwai damuwa a tare da shi, kuma yaji gabansa ya fadi damuwar da take zuciyar Hussain ta wuce har zuwa tashi zuciyar ta kuma samar masa da damuwa. Ko menene yake damun Hussain to babba ne dan Hussain bashi da damuwar, da wahala kaji abinda zai bata masa rai balle har ya nuna a fuskarsa. Kuma duk da haka ma a yanzun in ba Hassan din ba da wahala wani yace akwai damuwa a fuskarsa, sai dai ko Aunty.

To ko an samu problem ne a fertility test din nasu?

Sai dai kallon fuskar Fatima ya saka ya fahimci ko ma menene problem din Hussain bai shafi Fatima ba kuma bata da masaniya akan sa. Hannunsu sarkafe dana juna suka karaso gaban Hussain “hello bro” sai kuma ya jawo Hassan ya rungume shi a jikinsa, d Hassan felt the tighness of his grief. Fatima tayi dariya, “Lallai Hassan da gaske anyi missing dinka” yayi murmushi yana cire Hussain daga jikinsa yace “iyayi, in yayi niyya kuma gobe ma ya ce wata tafiyar zai sake yi”.

Har suka je gida Hassan yana lura da ya yanayin Hussain, yana kuma kara tabbatar wa da kansa da cewa akwai abinda yake damun Hussain din. Suna zuwa yayi packing, Hussain ya fito yana mika yace “home sweet home” sannan yabi kannensa da suka taho tarensa har Hassana ita kowa yayi hugging dinta sannan ya wuce har cikin gidan yayi hugging aunty itama. Duk suna tayi masa dariya, shima dariyar yake yi yace “baku san yadda nake son ku bane ba, you are all here, my life is all here” sai kuma ya tuno da twins yace “ina yaya na? Aje a dauko min yayana”.

Ranar nan suka karasa wuni tare, sukayi lunch tare dinner ma haka sannan mijin Hassana yazo ya dauke ta, Fatima da Hussain ma suka tafi saboda sun dauki gajiya gashi basu huta ba. Hassan ma yayi wa Aunty sallama bayan ta bawa yaran ta su Yusuf sun mayar dasu gurin Ruqayyah, sai ta tsayar da hassan tace “menene yake damun Hussain?” Ya daga kafada yace “ban sani ba Aunty, tun da suka sauka na lura akwai abinda yake damunsa amma gobe zan tambaye shi” ta gyada kai tace “ka tambaye shi kaji, naga damuwa a fuskarsa. Sai da safe, ka duba Ruqayyah da jiki” ya gyada kai tare da ajjiyar zuciya, ambatar sunan Ruqayyah da tayi ya tayar masa da mikin da ke cikin zuciyarsa a kan Ruqayyan. Har baya son ya koma gida ma, amma babu yadda zaiyi dole ya koma.

A palo ya tarar da ita da plate din abinci a gabanta tana waya tana dariya, da alama hirar tayi mata dadi. Ta dan dauke wayar daga kunnenta tayi masa sannu da zuwa, ya amsa babu ya bo ba fallasa. Yaran suna kwance akan kujera Aminu yana bacci Yusuf kuma yana kokarin rigima. Ya saka hannu ya dauke shi yana mishi wasa ya wuce dashi dakin sa.

Ta bi bayansa da kallo sannan ta koma kan wayarta. “Na gaya miki Minal ba lallai bane ya barni inzo, ynazu ma kin ganshi ya shigo gidan ko kallo ban ishe shi ba duk uwar kwalliyar da naci” Minal tace “k kika so ai, na gaya miki ki zo mu koma gurin mutumin nan kin ki, bawan Allah jiya ma sai da ya tambaye ni ke yana cewa ya kike ciki. Ki je kawai a rufe miki bakin Hassan yadda ko Aunty kika zaga sai dai ya kalle ki ya dauke kai” Ruqayyah tace “hmmm. Ke dai bar ni kawai in tashi in je kar in kara wani laifin akan wani” ta katse wayar tana tauna shawarar minal a zuciyarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button