TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A lokacin kuma Baba ya shigo, da sauri yan samarin suka mike suna karbar kayan hannunsa suna yi masa sannu da zuwa. Ya amsa yana zama akan tabarma kusa da Inna, Sumayya ta ajiye rariyar hannunta da take tankade da ita ta wanke hannun ta ta debo masa ruwa a randa. Ya karba yayi mata godiya, yasha ya ajiye kwanon sannan inna ta gaishe shi, yace “yauwa Sa’adatu. Ya gida?” Ta amsa da fara’arta, “ka dade yau baban biyu, har na fara tunanin in aika gidan maman Minal in aro wayarta a kira ka muji ko lafiya” Yace “wallahi na je gurin wannan neman aikin da na gaya miki ne, wannan sabon kamfanin da aka bude, H & H to naji sanarwa a gidan radiyo cewa sun fara daukan kanana da manyan ma’aikata shine naje ko Allah zai sa a dace su dauke ni ko aikin gadi ne inke yi musu, ko wani aikin dai daban, aikin dai da za’a ce mutum kullum in ya fita yana da aiki kuma duk wata zai samu albashinsa” Inna tace “insha Allahu muna da rabo a aikin nan. Mun gaya wa Allah kuma insha Allahu zai dube mu” yace “ameen” sannan ya jawo ledar daya shigo da ita yace “ga garin masara nan na auno mana uwar biyu, sai a lallaba ya kai mu wani satin” ta shafa ledar tana jin yawan garin tace “wannan baban biyu ai har wani satin zai kaimu in sha Allah. Mungode Allah ya kara budi, jazakallah bi khair” yace “ameen. Amma bance ake yin tuwo kadan ba dan kar gari ya kare, a yi isashshe wanda yara zasu ci su koshi da safe a dumama suci kafin su tafi Makaranta. Bana so suke zuwa makaranta da yunwa” Inna tana murmushi tace “lallai masu ‘ya’ya” ya jawo wata karamar leda yace “wannan busasshen kifi ne na siyo dan ake saka wa a cikin miyar kaɗi, saboda yara suji dadin cin ta” Inna Ade tace “Lallai yara yan gatan baban su, komai dai ace dan yara, ni ba a yin komai dan ni” ta fada da sigar tsokana, Zunnur yace “ai sai dai kiyi hakuri Inna mum kwace miki power a gurin Baba” duk sukayi dariya banda Ruqayyah da take ta gugar ta kamar bata gurin.

Inna ta tashi ta dauko masa abincinsa ta kawo masa, yana bude wa yace “lala, uwar biyu miya akayi mana haka harda salak? A ina kika samu kuɗi?” Ta dan bata rai tace “saboda nasan kana so shi yasa na danyi wani aiki na samu kuɗi nayi dan in faranta maka. Ni dan kai nayi ba dan yara ba” duk akayi dariya har da baban shima, sai kuma yace “to ai ke nasan baki da matsala, tunda ke kika zabe ni kika ce kinji kin gani, su kuwa yara basu suka zabi zama yayan mu ba, bana so suke sha’awar iyayen wasu suna cewa ina ma dai sune nasu” Sulaiman yace “haba dai Baba, ni da ace za’a sake haihuwa ta ace in zabi iyaye ai da ku zan zaba sau goma, kunyi mana komai sai fatan Allah ya saka muku da alkhairi ya bamu ikon yi muku biyayya da faranta muku”.

Sai a lokacin Baba ya juya yana kallon Ruqayyah da take ta gugar ta kanta a kasa yace “Hassana. Baki ga na shigo ba ko gaishe ni baki yi ba?” Ta dago da murmushin yake a fuskar ta tace “na gaishe ka Baba, baka ji ni bane” ya girgiza kansa kawai ya fara cin abincin sa.

Sai da yayi nisa da cin abincin suna yar hirarsu da Inna sannan ya dago kai yana kallon Sumayya yace “Hussaina yaya jarabawar taku? Ana dai kokari sosai ko?” Ta rufe tukunyar data ke juyawa ta taho tana cewa “Baba alhamdulillah, ai mun kusa gama wa ma insha Allahu nan da sati biyu zamu kammala gabaki daya” Ruqayyah ta ajiye iron din hannunta wanda ta gama guga dashi tace “nan da sati biyu zamu gama Neco Baba, saura Waec” yayi shiru sannan yace “ita ce wadda ba’a biya muku bako?” Sumayya tayi saurin cewa “ai bata da wani muhimmanci Baba. Kaga Minal ita fa waccan shekarar ta gama amma har yanzu bata karbo waec dinta ba tunda taci duk abinda ake bukata a Neco” Ruqayyah ta zauna akan tabarmar tace “muhimmancin ta daya shine idan mutum bai ci Neco ba, ko kuma yaci rabi bai ci rabi ba, zai iya hada wa da waec sai ya samu duk abinda ake bukata a jami’a” Baba ya gyada kai kawai bai ce komai ba, amma fuskarsa ta nuna damuwa.

Inna Ade tace “maganar jami’a fa naji kuna yi, ita minal din bata gaya muku uban kudin da mamanta take bani labarin an kashe kafin a saka ta a jami’a ba? Ita kadai ma ballantana ku biyu?” Baba yace “abin ai na Allah ne, insha Allahu, indai sunci wannan jarabawar kuma suna so zasu je. Ko ba zan iya turasu su biyu a lokaci daya ba sai in saka daya wata shekarar sai a saka dayar. Abin ai na Allah ne”

Friday bayan sun tashi daga makaranta, suna tsaye a bakin titi suna jiran abin hawa sai ga wata taxi ta tsaya a gaban su. Ruqayyah ta sunkuyo da niyyar yi wa driver magana sai taga mutumin ranar nan ne, ta ja tsaki tare da komawa baya tana hade rai. Sumayya ta leka itama ta gashi zata matsa taji yace “ku shigo in kai ku” Ruqayyah ta leko tace “ko babu motocin haya a titin nan gwara mu tafi a kafa” ta kuma komawa baya ta tsaya. Yace da sumayya “ke shigo in kaiki” ta girgiza kanta “bazan iya tafiya ba tare da sister ta ba” yace “I understand” tace “mungode bawan Allah” yace “yes, ni bawa ne na Allah but sunana Adam” Ruqayyah ta leko “babu wanda ya tambaye ka sunanka saboda babu wanda ya damu daya sani” Sumayya ta kalle shi tana murmushi tace “Sunana Sumayya, yar uwa ta kuma sunanta Ruqayyah,”.

Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only???????? TAGWAYE ????????

By

Maman Maama

Free Episode

Episode Six : Chloroform

Hira tayi dadi tsakanin Hussain da gimbiyar sa, har lokaci ya tafi ba tare daya sani ba, tun suna kan kujera suna hira har suka sauko kan carpet suna ta magana cikin yiwa juna murmushi da dariya, kasancewar duk su biyun masu fara’a ne sosai. Suna cikin hirar ne alarm ya kada a wayar Fatima, ta dauka ta kashe tace masa “lokacin tafiyar ka yayi kar kayi missing Flight dinka” yana kallonta da mamaki yace “wai kina nufin har alarm kika saka min?” Ta juya idonta tace “nasan zamu iya mantawa, kuma tafiyar ka tana da muhimmanci, bana so inso kaina da yawa”

Ya jinjina kansa yana jin soyayyar ta tana karuwa a zuciyarsa, sosai yake son yadda take gudanar da al’amuran ta, komai nata a tsare yake, komai nata a nutse take yinsa. Har airport ta kai shi sannan sukayi sallama a ransu suna jin kamar kar su rabu, Hussain yana ji a jikinsa cewa in sukayi aure duk tafiyar da zaiyi tare da ita zai ke yi tunda dai matarsa ce kuma babu abinda zata zauna tayi a gida.

Cikin sauri yaje gida, ya tarar Hassan ya gama hada masa kayan tafiyar sa ya zuba masa a mota dan haka wanka kawai yayi ya chanza manyan kayan jikinsa zuwa ƙanana sannan ya shiga mota Hassan ya mayar dashi airport. A hanya babu wanda yayi magana har suka je, haka kawai Hussain yaji jikinsa yayi sanyi and for the first time tunda ya fara tafiye-tafiye yaji cewa baya son tafiya, yaji cewa baya son ya rabu da danuwansa.

Sai da Hassan ya karkada masa key a fuska sannan ya juyo yana kallonsa yana kirkiro murmushi. Hassan yace “what’s wrong? Tsoron jirgin kuma kake yi yau ko me?” Hussain ya duba agogon sa yana noticing mintinan daya rage kafin jirgin su ya tashi, wata zuciyar tana gaya masa ya juya ya koma gida amma sai yayi sauri ya girgiza kansa yace da Hassan “take care of yourself bro. Bazan jima ba dan bana jin zan wuce sati daya. Duk abinda ya kamata ayi to ayi kawai kar ace sai an jira ni. Ka bawa Aunty hakuri kace tafiyar ta zama dole ne bana so auction din nan ya wuce ni” Hassan ya rike dariyar da take taso ma sa yace “Badan na sanka ba da sai ince kamar tsoro nake gani a fuskarka kuma nake ji a muryarka, amma na sanka kuma nasan Hussaini baya jin tsoron komai, shi jarumin jamurai ne” Hussain yayi murmushin da ya tsaya a lips dinsa yace “bana jin dadi ne kawai. Amma nasan kafin mu sauka zan ware” ya sake kallon abogon hannunsa sannan yace “take care of yourself bro” Hassan yace “you already said that bro” sai hussain yayi murmushi yana bude hannu yace “okay take care of everyone at home” sannan ya bude kofa ya fita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button