TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta tarar da shi a kwance da Yusuf akan cikin sa yana yi nasa wasa yaron yana bangala masa dariya, ta zauna a gefen gadon tace “ashe Hussain ya dawo, no sai ji nayi ance a kawo twins inji Hussain” ” eh ya dawo” yace mata. Tace “amma ko ka gaya min? Ai da na shoga nayi masa sannu da zuwa ko?” Ya juyo yana kallon ta yace “da aka aiko ki vada Twins din ai kinsan ya zo din kenan, idan da kinyi niyya da zaki iya fita a lokacin kice masa sannu da zuwa” tace “to ai ban tambayeka ba ko? Ya zanyi in fita ba tare dana tambaye ka ba” yace “okay, sorry. Nayi tunanin kina da number waya ta ashe baki da ita” ta ji daci a ranta, tayi shiru tana kallon yadda ya cigaba da wasa da yaron sa ko ta kanta bai bi ba.
“Kayi hakuri” tace tana kakaro hawaye, “dan Allah kayi hakuri ni bana son wannan fushin naka wallahi ni sai inji gidan gabaki daya yayi min zafi, mi duniyar ma gaba daya zafi take min in kana fushi dani. Tun jiya nake ba ka hakuri fa, sai maganganu kake gaya min dan nayi kuskure sau daya” ya ajiye Yusuf yace “kin kwantar da Aminu? Kar ki bar min yaro akan kujera ya fado yaji ciwo” daga haka ya mike ya shiga toilet.
Har washegari basu dai daita ba, wannan yada bata samu damar tambayarsa zuwa gurin dinner din ba sai text din ban hakuri ta tura wa Minal sannan ta kashe wayarta dan tasan ba zata barta ta huta ba da masifa. Shi kuma Hassan, washegarin neman yadda zasu zauna da Hussain yake yi saboda ya samu ya tambaye shi abinda yake damunsa. Basu samu zaman ba har yamma, yana shigowa gidan ya gansu sun shigo shi da driver dinsa Adam.
Adam ya fito ya gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa kamar kullum, amma yau sai ya kara da “yaya karatu?” Adam ya shafa kansa yace “alhamdulillah oga” Hussain ya fito yana cewa “can you believe yaron nan First class yaje ja a school? Gashi wai yanzu har suna level two kamar fa yau suka shiga” Hassan ya kirkiro murmushi yana “good for him” sai ya juya kan Hussain “yalllabai ina son magana da kai fa, tun dazu nake neman ka kana can kana gantali” Hussain yace “ba gantali na tafi ba, napeps din nan ne aka kawo su naje gani, dama ina so mu zauna ayi shortlisting wadanda za’a bawa” Hassan ya gyada kai. Haka Hussain yake fitar da zakkar sa duk shekara, baya rabon kudi ko kayan abinci, wadannan sai dai idan normal kyauta ne amma zakka yafi son ya bayar da abinda mutum zai yi sana’a dashi. Ganin yadda Baba yake morar Napep dinsa ya sa ya yanke hukuncin zakkar bana ta Napep zaiyi ga matasa.
Tare suka jera zuwa cikin gidan Hussain sannan suka hau har samansa suka zauna a palon sa. Ya dauko takardar da aka kawo masa ta list din eligible mutane kowa da description dinsa yace “a cikin wadannan za’a zabi wadanda za’a bawa” Hassan ya karbi takardar yana noticing yawan mutanen sai ya ajiye ta a gefe yace “forget about them. Tell me about you. Me yake damunka?” Hussain ya saki baki yana kallon sa yace “ni? Me ka gani a tare da ni? Ni babu abinda yake damuna ni lafiya ta kalau” Hassan ya gyara zama yace “hmmm really? Wannan maganar da kayi ita ta tabbatar min akwai abinda yake damun naka kuma ta nuna min cewa abin is related to your health. Tunda ni dai ban yi maganar ciwo ba amma har kace lafiyar ka kalau” Hussain ya saka hannunsa a cikin gashinsa sannan ya cire yace “to mr smarty-pants, ni babu abinda yake damuna health wise ko other wise”.
Hassan ya kwantar da kansa a jikin kujera yana kallon Hussain din da yake ta rarraba ido a dakin kamar yau ya fara ganin dakin. Sannan yace “is it about the fertility?” Hussain ya bata fuska yace “no. In baka yarda ba ma bara in dauko maka result din ka gani, sun ce komai lafiya lau sun kuma bamu drugs da kyma shawarwari. Ni ka tuna min ma, ya kamata in tafi gurin matata yanzu…..” Hassan yace “to idan ba akan fertility bane ba akan menene?”
Hussain ya mike yace “na gaya maka babu komai, babu komai fa. Please ka bar maganar ta wuce haka nan” Hassan ya mike shima yace “bani kadai ba, hatta Aunty sai da ta lura akwai damuwa a tattare da kai. Tell me damuwarka, that’s all I asked” Hussain yace “damuwata a yanzu itace yadda ka damu da abinda babu. Ni babu abinda yake damuna” Hassan ya daga kafada yace “shikenan, fine, kar Allah yasa kayi min magana din” ya juya ya bar gurin amma a ransa yana mamakin girman abinda har Hussain yake boye masa shi, mostly shine mai boye magana ba Hussain ba, Hussain zai fadi abinda yake ransa ne kawai ko a mutu ko ayi rai.
A gida ya tarar Ruqayyah ta shirya masa abinci, taci kwalliya da shigar kananan kayan da tasan yana so. Yana hawowa sama ta mike da twins are both arms dinta tace “sannu da zuwa mijina. Muna nan muna ta jiran ka ni da boys” ya karaso yana pinching cheeks din yaran da suke ta kokarin miko masa hannu. Yace “yauwa sannunki, ya gida?” Ba tare da ya jira amsar ta ba ya zagaye ta zai wuce, cikin muryar kuka tace “wai kai ba zaka hakura bane ba, na baka hakuri na baka hakuri, nayi kuka nayi kuka, kuskuren da nayi guda daya amma ba zaka yafe min shi ba”
Ya juyo yana kallon ta, yana kallon hawayen da take matsowa daga idanunwanta, sai yaga kukan nata yayi masa kama da kukan karya, hawayenta yayi kama da crocodile tears, sai ya samu kansa da tambayar kansa in wannan shine irin kukan da take yi masa all the times kuma me yasa bai taba lura da cewa ba kukan gaskiya bane ba sai yau? Ya dawo ya karbi Aminu daga hannunta yace “ni bance miki ba zan yafe miki ba ban kuma ce miki ban hakura ba kawai dai ina bukatar tume alone to process things, am surw zamu dawo kamar yadda muke ada ko? Besides, love concurs all”
Ta dan yi murmushi tana goge hawayenta tace “yes, love. Shine abinda na sani, abinda na sani shine ina son mijina sosai bana kuma son bacin ransa. Kaga fa yau ake yin dinner din Minal amma saboda bana so in tambayeka ranka ya baci shi yasa ban ma tambaya ba ballantana inje” ya karasa share mata hawayen yace “good girl. In ba kyason bacin raina ba dinner din Minal ce kadai ba zaki je ba, harka da Minal din gabaki daya nake so ki daina. Yes, nasan childhood friend dinki ce saboda makotan ku ne and all, but ni kuma yanzu mijinki ne kuma nace bana son harkar ki da ita” ta sunkuyar da kanta sannan ta gyada kai da sauri, yace “good” ya juya zai tafi daki tace “ga abinci fa, abincin da kafi so shina dafa maka” ba tare daya juyo ba yace “zan ci, sai nayi wanka na huta tukunna”.
Har sati ya zagayo Ruqayyah bata gane inda Hassan ya dosa ba, tayi amfani da hawayen, tayi amfani da kalaman, tayi girkin, har sanitation din dakinsa tayi masa amma sai ya gyada kai yace mata “Nagode” yayi tafiyar sa. Shi kuma Hassan ba wai case din Ruqayyah bane ba kadai a ransa, da akwai case din Hussain, tunda ya dawo ya kasa gae kansa yanzu ma gani yayi kamar yana avoiding dinsa baya son su zauna su biyu a guri daya sai dai in da third party Saboda yasan suna kadaicewa zai dame shi da tambayar menene problem dinsa. Shi kuma akan sa Hussain ya ki barin zuciyarsa tayi processing abinda doctor din ya gaya masa, ya san cewa akwai chances na cewa doctor din is wrong but tunda maganar ta daki kunnensa yaji a jikin sa cewa gaskiya ne maganar.
Tun da yayi hankali, kullum zuciyars tana kan mutuwa, kullum gani yake ba zai kai gobe ba zai mutu kuma bai taba jin cewa hakan ya dame shi ba, but he always thought about sudden death, accident da sauran su. Sannan kuma abinda yasa maganar ta taba shi sosai shine rashin Da, yaci burin ya haihu kafin ya mutu, yadda sunan sa ba zai taba ba, blood line dinsa zai cigaba da tafiya a duniya. Amma kuma sai da yake tsaka da neman haihuwar sannan wannan labarin zai riske shi.