TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan shi yasa ya gudo daga America, saboda baya son ayiasa test din ballantana a tabbatar masa da abinda likitan ya fada, ya fi son ya cigaba da rayuwarsa without having to go through all that cancer treatment processess sai dai in mutuwar tazo kawai ya tafi. Ya san babu mai kara masa ko da numfashi guda daya ne akan wanda aka riga aka rubuta masa.

But…….ten days after.

Ya tashi da safe ya gama using toilet sai yaga jini, and his heart sank. A kasan toilet din ya zauna ya dafe kansa da hannayensa biyu yana lissafo rayuwarsa tun daga wayonsa zuwa yanzu da yake jin tana crashing down on him. So yake yaga mistakes dinsa ko zai iya gyarawa, so yake yaga abubuwan da yake so yayi kuma bai yi ba dan yayi kokari yayi su yanzu. Ba mutuwar ce damuwar sa ba sam, rabuwa da loved ones dinsa ne damuwarsa. A wanne hali zasu kasance bayan babu shi? Wacce irin damuwa zasu shiga ta rashin sa a tare da su?

Ya tuna Hassan, he is going to be broken to pieces but with time zai yi surviving saboda yana ga kakkarfar zuciya duk kuwa da yasan ba zai taba komawa dai dai ba, saboda su biyun kowannen su tamkar sashi ne na ruhin danuwansa dan haka rayuwar Hassan will take a sharp change without him, sai dai yayi masa addu’ar Allah ya bashi strength din da chanjin zai zama for the better.

But halin da Hassan zai shiga bai yi breaking heart dinsa ba kamar halin da Fatima zata shiga. His poor innocent princess. Sai yaji kamar bai yi mata adalci ba daya aure ta, ya cika ta da soyayyar sa ya mayar da ita karamar bazarawa without even a child to look at and remember him. Auren Fatima is the best thing that happened to him and rayuwar da yayi da ita so far are the best days of his life. Looking at his life sai yaga his only regret is not having a child of his own, someone to carry on his name tunda dai duk yadda yake da Hassan babu ta yadda za’a yi yayan Hassan suyi bearing sunansa.

Ya fara lissafin abinda ya kamata yayi yanzu, shin ya tara family dinsa ne gabaki dayan su ya gaya musu halin da yake ciki su taya shi da addu’a ko kuma ya barsu sai mutuwar ta zo sa sani?

Ya tashi ya shiga shower ya kunna wa kansa ruwa, kafin ya fito ya yanke shawarar abinda zaiyi. Bai samu Fatima a dakin ba, ya san tana kitchen tana shirya masa abinda zai ci. Poor sweet thing. Da sauri ya shirya ya fita ta hanyar da yasan ba zasu hadu da Fatima ba dan baya son ta ganshi a wannan yanayin dan zata iya karanto wani abu a fuskarsa. Yana so yaje ya samo wa kansa strength dan haka inda zai samu ya tafi.

A palon kasa ya tarr da Ruqayyah daga dukkan alamu aiki take yia kitchen, ta saki baki tana kallonsa da mamaki sai kuma ta gaishe shi, ya amsa yana tanbayarta Hassan tace yana daki, “bara ayi masa magana” ya dakatar da ita “no, yi aikin ki kawai, bara inje” daga nan ya wuce ta ya hau saman. Ta bishi da kallo, tana jin motsinsa har taji ya bude kofar Bedroom din Hassan ya shiga, ta tabe baki, “yau kuma wani kuturin wulakanci ne ya tashi za’a shigar min har dakin miji?”

Hussain ya shiga dakin yana karewa tsarin dakin kallo, it has Hassan written all over it, tas tas komai a arrange kamar yadda yake a kowanne dakin sadaya sani. Babu ko digon datti a kasa. Ya zauna a bakin gado yana jin kewae Hassan already tana ra tsa zuciyarsa. Sai ya jawo pillow ya kwanta ya kifa fuskar sa a kai.

Hassan ya fito daga toilet da robe a jikin sa hannunsa kuma rike da towel yana gige ruwan kansa. Ya tsaya yana kallon Hussain da sakakken baki, yace “kai! Me kake yi min a kan gadon aure na?” Hussain ya dago kansa yana kallon sa da lumsassun idanuwa yace “kar ka yi min gori Malam, nima ina da gadon auren a gidana, klin kana son ka rama kaje ka kwanta kaima akai” Hassan yace “ni ai ina da hankali, ba zan kwanta a gadon matarka ba. Kuma wannan pillown na Ruqayyah ne ba nawa bane ba” Hussain yayi jifa da pillown ya jawo dayan, Hassan yayi dariya yana cigaba da goge kansa.

Hussain yace “ka tuna sanda nake baro dakina in taho naka in kwanta in ce acn dakina bata da sanyi?” Hassan yace “kuma in kazo ka takura min kace sai akan pillow na zaka dora kanka wai yafi laushi” Hussain yayi dariya yace “har zuwa kake ka siyo min pillow dan in bar maka naka, ka saka aka zo aka gyara min ac amma duk ban dai na zuwa ba” Hassan yace “ai dama babu abinda ya samu acn, kawai dai kana so ka takura min ne ka hana ni jin dadin bacci”

Hussain ya danyi shiru yana kallon wani hoton su a cikin karamin frame a gefen gado, da uniform din secondary school a jikin su duk kanin su suna murmushi, ya tuno ranar da aka dauki hoton ranar da suka yi wani match ne kuma suka yi winning, a lokacin Hussain cewa yayi footballer zai zama tunda yaga suna saurin yin kudi, ya juyo yana kallon Hassan yace “ba wai dan in takura maka bane nake zuwa dakin ka ba, ina zuwa ne dan ina son ka, bana son rabuwa da kai” Hassan ya tsaya da towel din a hannunsa yana kallon Hussain amma ya kasa cewa komai, Hussain yace “promise me idan na mutu kullum zaka ke zuwa kabarina kana yi min addu’a” Hassan ya saki towel din hannunsa yace “stop it” amma bai ga alamar wasa ko murmushi a fuskar Hussain ba, sai ma yaga murmushin da yake masking damuwarsa da shi ya gushe sai damuwar ta bayyana gabaki dayan ta. Ya bude baki a hankali yace “I am dying bro”

Hassan yace “No!” Da kakkaurar muryar da sai da dakin ya amsa. Sannan ya tako zuwa gaban Hussain fuskar sa babu ko digon annuri ya nuna shi yace “don’t ever say that again”. Hussain ya juya fuskar sa gefe yace “ko da hakan ne gaskiya? Baka son in fada maka gaskiya? Ni da nazo da niyyar in samu kwarin guiwa daga gareka sai kuma ka satar min da guiwa ta? Zuwa nayi fa dan ka bani courage, dan bani da inda zan je inda yafi nan gurin ka”

Hassan ya zauna a kusa dashi yana juyo da fuskarsa yana so ya karanto alamar wasa a idonsa amma ya kasa karantowa yace “yau ba 1st of April bane ba, ka tuna ranar da kayi min April pool kace min dakina ya kama da wuta? You are fine brother, you look good, very good even.” Hussain ya dan yi murmushi yace “Cancer ce Hassan, colon cancer” Hassan yana girgiza kansa da sauri ya sake cewa “no! Karya suke, duk likitan daya gaya maka karya yake yi, he is a crook doctor da yake using fake machines”

Sai Hussain ya bashi labarin yadda suka yi da likitan daya duba su shida Fatima a america, sai Hassan yayi murmushi yana jin sanyi a ransa yace “you see? Kana tayar da hankalin ka a banza kana kuma tayar min da hankali Hussain. Ta ya fertility doctor zai diagnosing Cancer? Karya yake yi, he is wrong, he is very wrong” Hussain ya girgiza kansa yace “he is not wrong bro” sai ya bashi labarin jinin da ya gani yayi a toilet.

Murmushi Hassan yabace sai kuma ya sake yin wani yace “that doesn’t mean anything, zata iya yiyuwa basir ne ko rana ko wani abu na daban. Wannan zaman da kake yi a jirgi ma ba dole basir ya kamaka ba?” Hussain ya girgiza kansa cikin raunanniyar murya yace “Hassan Please, don’t give me false hope mana” Hassan bai bashi amsa ba sai ya mike ya dauko wayar sa da take jikin chargi ya kira family doctor dinsu yace “ina so dan Allah ka bincika mana best oncologist ko a wacce kasa yake kayi mana booking din ganinsa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button