TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Hassan ya mike ya mammayar da kayan da Hussain ya baza, sannan shima yaje yayo alwalar ya fito ya tayar da tasa sallar.
Hussain ya hakura ya yarda za’a yi masa aiki amma sam babu walwala a fuskarsa, sai Hassan ya fahimci kamar aikin yafi damunsa a kan ciwon ma gabaki dayansa. A haka har aka gama preparation ya zama saura kwana daya ayi aikin sai suka tafi asibitin zasu kwana acan, a lokacin ne zuciyar Hassan ta karye yace da Hussain “ina ganin a fasa aikin nan Hussain, ni bana jin dadin yadda kake reacting to it ka ƙi kwantar da hankalin ka bayan kuma kai ba mai yawan tayar da hankali akan abu bane ba, ni duk sanyaya min jiki kake yi wallahi, na kasa fahimtar if am doing the right thing or not. Please bro, ka gaya min cewa ba wai takura maka zanyi ayi maka aikin nan ba, dan Allah ka gaya min” sai Hussain yayi masa murmushi yace “ba wai ka takura min bane Hassan, ba kuma na yarda bane saboda kayi threatening cewa zaka gaya wa Fatima ba, na yarda ne saboda kai, saboda ina so in faranta maka, saboda ina so kaji cewa you did your best kar kayi feeling cewa ka gaza gurin kula dani. But ina so kai ma kayi mini wani alkawari Hassan. Ina so kayi min alkawarin cewa wannan shine surgery na farko kuma na karshe da zaka saka ayi min akan wannan cutar” Hassan ya sunkuyar da kansa kasa, Hussain ya dago fuskarsa yana kallon idonsa yace “say it. Kace kayi min alkawari” Hassan ya karbe fuskarsa sannan yace “nayi alkawari. Kuma nasan ma wannan aikin akwai nasara a cikin sa, mun gaya wa Allah kuma ya dubi kokarin mu. Zamu samu nasara am sure” sai Hussain yayi murmushi yace “good” . Sai ya koma ya kwanta ya rufe idonsa har aka zo aka tafi dashi.
The surgery took 3 hours. A cikin 3 hours din nan Hassan sai da yayi nadamar da basu gaya wa kowa ba, at least da an taya su addu’a, dan ji yake yi kamar bakin sa shi kadai yayi kadan a addu’ar. A cikin awa ukun nan har wata irin rama yayi.
Yana tsaye aka fito da Hussain, aka tura shi recovery room, inda kuma anan ne zai cigaba da karbar treatment dinsa.
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020The Email
Washegarin da akayi aikin aka fara yiwa Hussain chemotherapy treatment tare kuma da radiation therapy, at the same time kuma ana monitoring warkewar gurin da aka yi masa aiki internal da external. It has not been easy on him duk da cewa Hassan yana tare dashi kuma likitocin suna kulawa dashi sosai, magana mai dadi, karfafa guiwa, da tabbatar da cewa he is comfortable. Shi kansa yasan ya rame, tun kafin ayi aikin kuma ya rane din dan Fatima tasha yi masa mita a waya cewa ya rame, tun yana kakkaucewa har dai ya daina kiran ta video call itama kuma inta kira baya dauka sai yace mata phone dinsa ta samu matsala.
A haka har ya fara jin dadin jikinsa, su kansu doctors din suna yabawa da yadda jikin nasa yayi kyau, ya rage yin amai sosai wanda yana daga cikin side effect na chemotherapy kuma shi yake saka rama, saboda jikinsa ya fara sabawa da magungunan da ake bashi. Sai kuma ya dage da cin abinci, ya kuma cire damuwa a ransa nan da nan ya kara murmure wa. An gama radiation therapy din, magunguna ne kawai yake sha dan haka ya fara maganar yana son ya tafi gida. Da farko doctor din yaki yarda, ya fi son ya kara kwanaki ciwonsa ya kara warkewa duk da cewa ba zasu tabbatar da cewa surgery din is a success ba sai bayan wata uku sannan zasu sake dubawa su gani idan cancer din bata dawo ba, still daga nan ma ba za’a saki kiji ba za’a cigaba da dubawa bayan wata uku uku har sai an tabbatar ta tafi.
Sai daya tabbatar jikinsa yayi kyau sannan ya kira Fatima video call, suka yi hirar su ya tabbatar mata nan da kwana biyu zasu dawo, dan shi kam ya gaji ko ba’a sallame shi ba guduwa zaiyi.
Nigeria
Tun bayan tafiyar su Hassan sai Ruqayyah ta samu sake, a lokacin ne ta samu damar zuwa ta ga dakin Minal. Gidan ta mai kyau kuma mai girma part dinta daban na uwargidan ta daban, shi kuma mijin ya raba kayan sa a tsakanin su tunda akwai dakin sa a kowanne part. Minal ta baje sosai abinta ta na zuba wa uwargida rashin kunya son ranta yayin da shi kuma mijin ya ja bakinsa yayi shiru, yan uwan miji ma sun fara dawowa gurin Minal musamman uwar mijin da shekarun ta suka riga suka ja kuma bata da buri irin taga jikokin ta daga ɓangaren Alhaji Kabiru kuma a yanzu dukkan hopes dinsu yana kan Minal tunda suna ganin cewa rashin haihuwar daga matar ne ba daga mijin ba. Wannan yasa uwargidan mai suna Hajiya Baraka ta ja kofar part dinta ta rufe, bata gani ba ballantana ranta ya baci, babu mai shigar mata sai nata bakin idan sunzo, sai kuma mijinta idan ranar kwanan ta ce.
Ranar wuni suka yi suna hira, farko Minal ta nuna fushin ta akan kin zuwa bikinta da Ruqayyah tayi, daga baya kuma sai ta sauko ta nuna dama ai tasan wannan matsolon mijin na Ruqayyah ne zai hana ta zuwa dan kar ya kashe kudi. “Ni dai Ruqayyah da Allah ya bani miji irin naki gwara in yi ta xama a gida, ya za’a yi ina kallon dukiya kuma ace ba zanyi abinda nake so da ita ba? Kema walllahi da laifin ki, ai wallahi idan ni ce ba ka isa ba, a matsayin na na matar ka sai nasan yadda nayi na lankwasa ka kabi ra’ayi na wallahi” Ruqayyah ta tabe baki tace “kema dai kya fada Minal, ke ni fa duk kwanan nan abubuwa sun cushe min wallahi, ji nake yi ma kamar ba ya sona yanzu. Irin soyayyar da nake gani a idonsa yanzu duk sai inga kamar babu” Minal tace “haba dai! Kuna nufin ki ce min babban makamin naki ya ragu? Soyayyar da yake miki ce fa take rike dake a gidan, wallahi kar ki bari ta tafi, chafdi, ki zo mu koma gurin Malam a juyo miki da hankalin sa kachokan ya dawo kanki. Ke ba ki ga yadda mai gidan nan da yan uwansa suke rawar kafa a kaina ba? Ai ba haka na barsu ba fa”.
Ruqayyah ta dauke kai gefe tace “ke raba ni da wannan malamin duban, ki barni kawai zan samar wa kaina mafita dan ni tsoron malaman nan nake yi wallahi, na tabajin ance aikin su gaba yake ci sannan ya dawo ya ci baya, ku barni in lallaba kawai” Minal tace “sai kiyi ta lallabawar ai. Ni kam babu wata lallabawa da zanyi a rayuwa” sai kuma tace “ni bamu yi maganar wannan maganar da Malam yayi a kanki ranar nan ba, na cewa zakiyi kudi. Kinga fa maganar sa ta fara tabbata tunda gashi kin haifi yara biyu kamar yadda yayi alƙawari” Ruqayyah tayi murmushi tace “maganar da nake miki kenan ta lallaba war ai, na sani duk wani kudi da zan saka ran yi to ta hanyar Hassan zai taho, dan haka nake lallaba abuna har zuwa lokacin da zamu ga abinda rayuwa zata zo mana dashi kuma” Minal tayi dariya tana dan dukan Ruqayyah tace “munafuka, ashe dai kim yarda da Malam din tunda kin yarda da maganar sa. Ina tabbatar miki da cewa abinda ya fada zai faru din. Ni dai fatana daya shine Ruqayyah kar ki samu duniya kuma ki manta dani, ko me kika samu ina so na zama a hannun daman ki” Ruqayyah tace “a’a ban yi miki wannan alkawarin ba Minal, za dai ki zauna a hanun hagu na amma Sumayya ita ce a hannun dama na” Minal ta bata rai, “shikenan tunda wariya za’a nuna min, hannun hagun ma ban raina ba”.