TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai dai hakan bai sa baccin Fatima ya dawo gare ta ba, sai dai ta dauki shawarar Aunty bata nuna masa ta fahimci yana boye wani abu ba kuma ta dage dayi masa addu’a da fatan alkhairi aduk abinda yake gabansa……

Sai dai sati daya bayan dawowar ta, sai gashi ya kuma kiranta video call, kuma sai taga yana looking much better than ganinsa da tayi na karshe sai dai shadow din da yake kwance a kasan idonsa. Tace “you look so handsome” yai murmushi yana saka hannu tare da kara gyara gashin kansa yana kashe mata ido yace “Hussain ne fa, Hussain will always look handsome” tayi dariya “kai ka fiya son kanka da yawa” sun jima suna hira, yana tabbatar mata da cewa Hassan ya samu sauki sosai kuma nan da kwana biyu zasu dawo gida. A ranar tayi bacci mai dadi sosai.

Sai dai……….
Washegari a morning news ana fadar major headlines na jaridun kasar nan taga katon hoton mijinta ya cika screen din tvn ta, da rubutu a kasa…..

“Hussain Aminu Abdullahi, H and H boss, is suffering from colon cancer and currently receiving treatment in India”

Ta saki kofin tea din hannunta idon ta a cikin na Hussain din da yake murmushin sa da baya rabuwa dashi. Sai news din ya cigaba yana nuno hotunan Hassan dana Hussain, kunnuwan ta basa jin abinda ake cewa, amma daga hotunan ta fahimci a asibiti ne sannan basu sani ba ake daukan su, kuma yanayin hotunan yana nuna Hussain din ne marar lafiyar. Screen din ya tsaya akan hoton Hussain a kwance akan dago, ga naurori a zagaye dashi, ga kuma doctors a tsaye a kansa.

Kwakwalwar ta tayi blacking out, sannan ita ma ta zame ta bi kofin shayin ta zuwa kasa.

Yarinyar ta da abin ya faru a gabanta ce ta saka ihu, sauran jama’ar gidan suka zo tare da Khadijah wadda tun tafiyar Hussain a gurin ta take, ganin halin da take ciki ya saka Khadijah ta kira aunty ta gaya mata sannan tace a samu driver a tafi da ita asibiti, ita Khadijah sam bata ga labaran ba saboda kafin ta futo daga daki an dauke gurin an tafi wani labarin daban.

Adam aka kira cewa ya kawo mota za’a je asibiti, sai dai yanayin da aka tarar dashi shima a rikice yake, dan shima akan idonsa akayi labarin. “Dama oga Hussain bashi da lafiya? Dama tafiyar da suka yi asibiti ya tafi?” A hakan dai ya dauko motar aka saka Fatima, Aunty da Khadijah suka shiga Aunty tana kiran doctor dinsu tana gaya masa gasu nan akan hanya. Sannan dauko robar ruwan data fito dashi a hannunta tana bismillah tana shafawa fatima a fuskarta, tana kuma zuba mata har cikin rigarta. Ta sauke ajjiyar zuciya a hankali tana dan bude idonta ta dora su akan Aunty. Aunty ta fara jera mata sannu, ta juya ta kalli Khadijah tace “ya dawo? Kun kira shi a waya ya taho?” Khadijah tace “waye?” Fatima ta juya tana kallon Aunty tace “Hussain Aunty ashe abinda yake boye mana kenan?” Sai ta rushe da kuka tana tuno fuskarsa a zagaye da doctors. “Na shiga uku ni Fatima Allah ka tashe ni daga wannan mummunan mafarkin. Dan Allah Aunty ki ce min mafarki nake yi Hussain lafiyar sa kalau” Aunty ta rungume ta “Hussain lafiyar sa kalau mafarki kika yi, ban san me kika gani a cikin mafarkin ba amma mafarki kika yi dan Hussain dina lafiyar sa kalau babu abinda ya same shi dan dazu ma munyi waya dasu” ta rike fuskar Aunty “ba mafarki nayi ba aunty a tv na gani. A labarai na gani sunce Hussain bashi da lafiya wai cancer ce take damunsa yana asibiti, har da hotuna suka nuna Aunty, Aunty Hussain dina…..” Sai ta rufe fuskarta tana kuka mai ratsa zuciya.

Aunty ta fara girgiza kanta “uhm uhm, karya suke yi, makiyane kawai suke yi masa mugun fata, Hussain lafiyar sa kalau, Hassan ma ya warke sun kusa dawowa, karya ne ki daina bata hawayen ki akan karya Fatima. Bara in kira miki shi ya tabbatar miki da cewa karya suke yi. Ko kuma mafarki kika yi Fatima” a haka suka asibitin, sai da suka yi packing sannan Adam ya kira Khadijah gefe ya gaya mata shima yaga labaran da haka ba wai mafarki Fatima tayi ba, nan take Khadijah itama ta rude dan da duk tunanin ta mafarki Fatima tayi dannita tana bacci ne ma taji hayaniya ta tashi. Nan da nan ta bi Aunty a baya cikin asibitin, ta tarar har karbi Fatima daga hannun Aunty, ta ja ta gefe ido a waje ta gaya mata abinda Adam ya gaya mata. Aunty tana girgiza kanta da sauri ta dauko wayarta ta danna number din Hassan ta India

Yau Hussain tunda yayi sallar asuba ya kuma fita yayi exercise din da likitoci suke saka shi yayi dan taimakawa ciwon sa yayi healing da wuri, sai ya dauko diary dinsa kamar kullum ya fara rubutu.

Dear baby

“Na samu sauki sosai, gobe nake shirin guduwa daga asibitin nan saboda naga basu da niyyar sallama ta ni kuma gida nake son komawa gurin mommyn ka, naga ta fara zama frustrated, bana so tayi fushi da yawa kar tayi min bulala. Kaima kabi ta a hankali dan in mayi mata laifi zata ke zane ka but ba wai dan bata sonka ba sai don tana so ka zama yaron kirki, zata so ka sosai na sani amma kuma nasan ba zata yi maka irin son da take yi min ba. Wait, kar kayi kishi, matsayi na daban naka daban”

Hassan ya shigo yana kallon sa yace “an fara rubutun?” Hussain ya rufe diary din yace “hmmm. Duk abinka dai ba zaka gani ba” Hassan yace “ban yi niyyar in gani din ba dai, san da kake sheka uban baccin ka in nayi niyya ai zan dauka in karanta ne” Hussain yace “sata kenan ai” Hassan yace “ni dai ba zanyi fada da kai ba, ni na daina fada da kai” Hussain yayi murmushi yace “makaho ne aka ce masa ga ido yace baya so, saboda yasan ba zai samu ba. So kake muyi fadan kuma ni ba zan kula ka ba” ya rufe littafin yana saka shi a cikin yar karamar jakar da ya siya musamman saboda littafin. Ya sauko daga kan gadon ya zauna a kujera da ke kusa da table din da aka jera musu breakfast, shi dai duk ba dadin wannan abincin yake ji ba, shi babu abincin da yake jin dadinsa kamar na gimbiyar sa.

Bayan sun gama cin abincin ne aka zo aka bawa Hussain magungunan sa yasha, yana ta mita yana cewa ya kusa daina shan magungunan nan dai ya huta, “ko ku sallame ni ko kar ku sallame ni guduwa zanyi” su dai basu ji abinda yake cewa ba, Hassan yana hararar sa sai ya daga kafada yace “ai nayi kokari” a lokacin ne wayar Hassan tayi kara, ya dauka yaga number din Aunty sai yaji hankalin sa bai kwanta ba dan dazu da ya fita waje ita ya kira kuma duk sun gama maganar da zasuyi, tabbas wani abin ne sabo ya taso. Ya dauki wayar ya fita waje yana magana “Aunty” “Hassan duk abinda kuke yi ku bari ku taho gida, makiyan ku suna nan suna yawo a gidajen radiyo suna yada karyar cewa wai Hussain bashi da lafiya, sun ce wai cancar hanji yake fama da ita, sunce wai abinda ya kaiku India kenan” ta karashe maganar cikin muryar kuka.

Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne. In kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number 08067081020Dear Baby

Not edited

Kafin Hassan ya dawo dakin har nurses din sun gama da Hussain sun fita, yana shigowa Hussain yabi fuskar sa da kallo sannan ya bude hannun sa yace “now what?” Hassan ya jawo kujera ya zauna yana kallon sa yace “zamu tafi Nigeria gobe da safe insha Allahu” maimakon Hussain yayi murnar cewa Hassan ya goyi bayan tafiyarsu sai fuskarsata nuna madaukakiyar damuwa, yace “me ya faru? Dawa kukayi waya yanzu?” Hassan ya gyara zama yana kallonsa yace “Aunty ce, ta kira tace duk abinda muke yi mu koma gida yanzu” ya dan sosa kansa “wani gidan tv dazu yayi broadcasting cewa baka da lafiya, sun fadi ciwon da yake damunka da kuma asibitin da kake kwance” Hussain ya mike “what?” Hassan yayi shiru bai ce komai ba. Sai Hussain ya mike, ransa a tsananin bace ya doshi kofar fita yana huci, Hassan ya mike shima da sauri ya rike hannunsa yana cewa “me zaka yi? Ina zaka je?” Hussain yace “zanga management na asibitin nan ne, zanji dalilin da yasa suka yi releasing information dina to the press bayan sunyi min alkawarin secrecy” Hassan yace “how do you know cewa sune? Anything can happen. Yanzu mutane sun koma kiwon mutum bana dabba ba. It ca be anyone har wadanda ba zamu taba zarga ba” Hussain ya juyo yana huci yace “waye to? Hatta iyalan mu basu san abinda yake faruwa ba mu kadai muka sani sai asibitin nan, dan haka dole sune suka fitar da bayanin nan. Wallahi sai na yi sueing dinsu, wannan ai keta privacy ne. Allah kadai yasan dawa dawa ye suka ji labarin nan a yanzu” sai kuma ya dawo ya zauna akan kujera yana dafe kansa yace “Fatima! Oh my God” ya mike da sauri ya fara neman wayarsa. Hassan ya riga shi gani sai ya dauke ya saka a aljihun sa yace “don’t worry about Fatima, she is fine, yanzu ka shirya zanje in karbar mana takardar sallama gobe mu tafi” Hussain yace “ba zan kai gobe a kasar nan ba. Bani waya ta. Bana so inyi fada da kai Hassan ka bani wayata in kira Fatima” Hassan bai ce masa komai ba sai ya kuma yi. Hanyar fita yana cewa “yau ko ni ko mai asibitin nan sai ya gaya min uban da ya bashi damar fitar da information dina” Hassan ya kuma rike shi “Hussain, take this easy, zata iya yiwuwa basu bane ba, akwai patients a asibitin nan kuma nasan a cikin su ba za’a rasa wanda suka zo daga Nigeria ba, ba za’a rasa wanda ya san fuskarka ko tawaba especially yadda kake watsa hotunan mu a media, wani zai iya gayawa wani, shima wanin ya gaya wa wani har maganar taje gurin yan jarida su kuma duk abinda zai dauki attention din mutane shi suke so su buga. Creating scene a asibitin nan ba zai gyara komai ba sai dai ma ya bata. Maybe yan jaridar suna waje suna kallon mu, maybe suna daukan hoton duk wani motsin mu, creating scene zai kara musu labarin da zasu buga ne, abu kadan yanzu suke nema su kara gishiri da magi su sake bugawa” Hussain ya juyo ya dawo dakin yana zura hannunsa a cikin gashin kansa, ransa a matukar bace. Ya juya bayansa ya dora goshinsa a jikin bangon dakin. Ko wanene wannan in ya kamashi Allah kadai zai raba su, it pains him that someone will make use of ciwon da yake yi ya in this way. Ko waye yayi wannan abin ko me yake tunanin zaiyi gaining???

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button