TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Hassan ya kama shi ya zaunar dashi a bakin gado yace “na kira airport, babu jirgi zuwa Nigeria a yau, tomorrow da sassafe zamu tafi” Hussain ya dago kai yana kallon sa, sai Hassan ya mika masa wayarsa yace “call her” Hussain ya karbi wayar yana jujjuya ta, shi bai ma san me zaice mata ba idan ya kirata din. Ya san dole dama zata sani tunda zata ga tabon surgery din a jikinsa but so yayi ace shi zai gaya mata da kansa at his own convenient time, har ya gama shirya kalaman da zai yi mata yadda ba zata tayar da hankalin ta sosai ba, amma yanzu bai ma san ta inda zai fara ba. Ya runtse idonsa sannan ya ajiye wayar a gefensa. Hassan ya mike yana dan bubbuga kafadar Hussain da niyyar bashi courage, sannan ya nemi huka ya saka ya dan rufe fuskarsa kadan sannan ya fita daga dakin.
Hussain ya jima a zaune a inda Hassan ya barshi, zuciyarsa tana yi masa zafin abinda aka yi masa, sai kuma ya dauki wayarsa ya lalubo number din Fatima ya tura masa text
“am sorry”
Hassan ya je ya shigar da complain din abinda ya faru ga management din asibitocin, sannan kuma ya nemi a basu sallama. Farko doctor din da yake kula da Hussain ya ki amincewa da hakan amma kuma da yaga Hassan din ya dake har yana threatening kai karar asibitin sai ya hakura sai dai amma sai da ya hada su da wani doctor a Nigeria wanda zai cigaba da monitoring lafiyar Hussain din tare kuma da yarjejeniyar cewa bayan wata uku Hussain xai dawo a sake gwada shi, kuma kafin nan in dai ya ji wani chanji a tare dashi zai dawo. Hassan duk ya amince, suka gama komai aka bashi takardar sallama.
A dakin ya dawo ya tarar da Hussain a kwance akan gadon ya rufe idon sa, ya zauna a kusa dashi, sai ya bude ido yana kallon sa yace “ko da wani ya ganninko kai a asibitin nan ba lallai ne yasan takamaiman me yake damu na ba, zai dai san cewa bani da lafiya, sai dai in asibitin su zadu fadi me yake damuna” Hassan yace “Hussain……it doesn’t matter. Let it go please….” Hussain ya tashi zaune yana kallon Hassan yace “babu wanda kuka yi maganar dashi?” Hassan ya girgiza kansa yace “babu” Hussain yace “ko Ruqayyah?” Hassan ya bata rai yace “what? Kana zargin Ruqayyah? Shikenan kuma dan baka son ta jinin ku bai hadu ba sai ya kasance duk wani bad abu zata iya aikatawa? Hassana ba zata taba aikata wannan aikin ba, ballantana ma ban gaya mata ba. Nasan abinda nake yi ai” Hussain ya koma ya kwanta ya mayar da idonsa ya rufe, yayi alƙawarin ya daina fada da Hassan, but zuciyarsa tana kan Ruqayyah. Hassan ya cigaba da magana. “ko da ace na gaya wa Ruqayyah ba zata taba aikata hakan ba, kar ka mata secondary school kadai ta gama, bata da wata exposure a rayuwa, bana jin ma tasan ta yadda zata fitar da maganar” Hussain yana kwance still idonsa a rufe yace “kace baka gaya mata ba, case Closed”.
A ranar suka bar asibitin, washegari da sassafe suka dauko hanyar Nigeria bayan sun kira Aunty sun gaya mata cewa gasu nan tahowa. Sai a lokacin suka samu labarin cewa Hassana ta haihu, ashe itama taga labarin kuma tashin hankalin ne ya tayar mata da nakuda ta haifi danta namiji, lafiya lau take sai dai jinin ta da ya hau sosai dan haka tana asibiti har lokacin.
Kowa yaje taryen su a airport amma banda Fatima, duk kuwa da cewa an sallame ta daga asibiti amma har lokacin kuka take yi musamman da ta ga message din Hussain da yake bata hakuri, hakan yana nuna mata cewa abinda aka fada gaskiya ne kenan, shi yasa tayi zamanta a gida dan bata jin kafafuwanta zasu kaita airport din.
A airport din ne kuma suka tabbatar da cewa maganar ta watsu sosai, dan sun ga yan jarida suna ta daukan su hotuna amma sai suka share suka nuna kamar basu lura dasu ba. Hussain ya bi dukkan yan uwansa ya rungume su daga bayan daya, yazo kan Ruqayyah sai ya karbi twins a hannunta yace “welldone babbar yaya” tayi murmushi tace “barka da dawowa gida” ya juyi yana kallon Hassan yace “ga mijin ki nan na dawo miki dashi in one piece kamar yadda nayi alkawari” tayi faffadan murmushi, sai yake ji a ransa kamar murmushin nata yafi karfin na ganin mijinta, kamar a can cikin idonta akwai wanda boyayyen abu. Daga airport din asibiti suka wuce gurin Hassana, suka duba ta suka kuma ga sabon dansu. “Hussain ya rike hannunta yace “kin ganni lafiya kalau ko? Kar ki kuma tayar da hankalin ki akaina girlfriend” haka yake ce mata tun suna yara, ta goge kwallar idonta, “amma ai gashi nan naga duk ka ka rame boyfriend” yayi dariya yace “ke kuma kinyi kiba ba, wa ya sani ma ko ke ce kike tsotse ni?” Ya fada cikin tsokana dan yasan bata son ki ba kwata kwata, ta bata rai “bata kiba nayi ba yaya H2, kumbura nayi kuma zan sace ne kafin suna”. Ya zauna a kusa da ita tmya dauki babyn yana yi masa addu’a, sai yaji a ransa yana fatan inama inama.
Basu dade ba suka tafi gida saboda ita ma yanzu ake shirin sallamar ta tunda bp din ya fara normalizing, kuma shi hankalin sa duk yana kan Fatima musamman saboda ganin yadda tunda suka zo Ruqayyah take makale da Hassan. Shima sai yaji yana son yaji tashi matar a jiki sa. Sai dai yasan akwai drama a tsakanin su.
Shi kadai ya shiga part dinsa, duk yan rakiyar sun tafi gurin Aunty, Hassan kuma da matarsa sun tafi nasu gidan. Bata kasa, ya hau sama zuwa part dinta ya zarce har Bedroom dinta inda ya same ta a kwance akan gado ta lullube har kanta. Yayi sallama amma sai ya tsaya a bakin kofa ya kasa karasowa, ta yaye rufar da sauri tana kallonsa da kumburarrun jajayen idanuwan ta, sai yaji a jikinsa cewa tun juya take dakin a kwance kuma tun jiyan kuka take yi, sai zuciyarsa ta raya masa ko ya zata yi ranar da yayi tafiyar da babu dawowa, nan take zuciyarsa ta karye yaji kamar zai taya ta kukan amma sai ya hadiye dan baya son ya kara mata damuwa, ya kama kunnuwan sa da hannayensa biyu ya fara yin sama da kasa kamar mai frog jump, ta sauko daga kan gadon da sauri taa kallon sa ta cikin hawayen ta sai taga ya cije baki alamar ciwo, da sauri ta karaso ta rungume shi tana saka kuka, sai suka zube a kasa gabaki daya, ta saka hannu ta daga rigarsa tana kallon ɗinkin da akayi a kasan cibiyarsa, ga shi nan raw ko warke wa bai gama yi ba. Ta kara karfin kukan ta “na shiga uku ni Fatima, Allah kar ka dora min kaddarar da ba zan iya dauka ba” ya kamo fuskarta yana kallon idanuwan ta da suka fada ciki yace “Allah, Fatima Allah baya taba dora wa bawansa abinda yasan ba zai iya dauka ba, duk abinda kika ga ya samu bawa jarrabawa ce dan a gwada karfin imanin sa, wannan ciwon jarabawa ta ce, idan wani abun ya faru dani ta sanadiyyar ciwon to jarabawar ki ce ke kuma” ta fara girgiza kanta tana neman shide masa “wayyo Allah na, babu abinda zai faru da kai Hussain babu abinda zai same ka” ya gyada mata kai yana kokarin ya dawo da ita cikin nutsuwar ta yace “eh Fatima, babu abinda zai same ni. Look at me, na warke kin gani an yi mini aiki kuma na warke kinji, babu abinda zai same ni” sai ta kara makalkale kamar mai shirin tsaga kirjinsa ta shige ciki. Ya zagaye ta da hannayensa yana jin zuciyarsa tana yin nauyi a kirjinsa. Ya runtse idonsa a ransa yana addu’a “Allah in har ka kaddara zaka dauke ni, Allah give Fatima the strength to bear it”.