TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai data nutsu sannan yayi mata bayanin yadda ciwon yake da aikin da akayi masa, ya kuma gaya mata irin confidence din da doctor din yake dashi a aikin, da kuma assurance din daya basu na cewa aikin will be a success. Ya fahimci hankalin ta ya fara kwanciya, tana ta jera ajjiyar zuciya, sai ya cigaba da bata positive vibes har sai daya ga tayi murmushi, sannan ya sake assuring dinta “I am fine princess, babu abinda zai same ni kinji?” Ta gyada kai, yana kallon kayan jikinta yace “anya kuwa kinyi wanka yau?” Sai ta boye fuskarta a kirjinsa tana jin kunya, yace “tashi muje inyi miki wanka”
A ranar da daddare ya tara yanuwansa gaba ki daya ya gaya musu gaskiyar abinda yake damunsa, yayi musu bayani kamar yadda yayi wa Fatima sannan ya kwantar musu da hankali kuma sosai hankalin nasu ya kwanta musamman sabod yadda suke ganin murmushi a kwance a fuskarsa babu wata alamar damuwa a tare dashi. A lokacin ne kuma ya fada musu kudirin sa, tafiya yake so suyi gabaki dayansu zuwa Umrah tunda ga azumi ya gabato sai suyi amfani da damar gurin roka masa lafiya a gurin ubangiji tunda shi kadai ne zai bashi lafiya. Zasu zauna a can har zuwa lokacin aikin hajji suyi sannan su dawo. Gaba ki daya za’a yi tafiyar har su Ruqayyah da twins dinta, Hassana mai jego kadai za’a bari sai jikinta yayi karfi sannan zata bisu a baya.
Washegari yan dubiya suka fara zuwa, labari ya bazu kowa ya sani, Hussain ya sauko babban palon gidansa ya zauna tare da Fatima a kusa dashi suna karbar duk wanda yazo duba shi hannu bibbiyu, duk kuma wanda yazo sai ya fahimci cewa ciwon ba yadda suke dauka bane ba. A cikin yan dubiyar har da Sumayya, wadda ta taho daga makaranta bayan Ruqayyah ta kira ta ta sanar da ita.
Part din Hussain ta fara shiga ta duba shi kuma suka gaisa da Fatima, Hussain yana ta tsokanar ta wai ita tana karatu amma maimakon take ramewa kamar yadda Zulaihat take yi sai take yin kiba. “ko dai Adam ne yake miki karatun bamu sani ba?” Ta sunkuyar da kai tana jin kunya, Fatima ta tambaye shi “Adam din gidan nan? Kai amma wannan abu yayi min dadi” Hussain yace “sun dace ko?” Sai Sumayya ta tashi da sauri tana yi musu sallama, suka yi ta mata dariyar kunyar ta.
A part din Ruqayyah, tana shiga ta dauki Yusuf “ubana na kaina, ubana yafi na kowa” Ruqayyah tayi dariya tace “zama dai ki cigaba da fada har masu gidan su jiki kina cewa baban ki yafi nasu” Sumayya ta daga kai tana kallon sama tace “ai ba haka nake nufi ba, salon magana ne kawai amma shima uban masu gidan ai ina son shi” ta karasa tana daukan Aminu, Ruqayyah tace “zaki sha kwana ko?” Sumayya ta zauna tana kiran A’isha ta kawo muta ruwa. “Daga school nake, kishi na yunwa kamar zan tafi barzaq” Ruqayyah tayi dariya “ai kuwa dai baya nuna wa a jikin ki, sai wani kyau kike yi yarinyar nan kamar kece a cikin daular da nake ciki. Ninkuma gashi kullum karewa nake yi kamar kudin guzuri” Sumayya tace “ai abin ba’a daula yake ba Ruqayyah, ni babu abinda zai hana ni kiba tunda babu abinda na nema na rasa, hankali na a kwance yake, karatu kuma ina ganewa sosai kuma zuciyata fes take, lafiya lau nake bacci na” Ruqayyah ta harare ta “to me kike nufi? Waye tasa zuciyar ba fes ba?” Sumayya tace “ni fa ba wani abu nace ba, salon Magana ne kawai”.
A’isha ta kawo mata ruwa da lemo, ta daga robar ta kusan shanye wa sannan ta ajiye. A lokacin Hassan yake saukowa daga sama “manya manyan yan jami’a, tun da naji gidan nan ya cika da hayaniya nasan ke ce kika zo, kin ga matata ita ba mai surutu ba ce ba” Sumayya ta ajiye robar ruwan tace “shi yasa gidan naku ai kullum yake yanayi da gidan makoki, sai nazo nake mayar dashi lively” ya karasa saukowa yana cewa “lallai wannan makarantar kullum kara kilar da ke take yi, ko kuma Adam ne yake yawar da ke?” Tayi murmushi tana dan saukowa daga kujera yayin da take gaishe shi, ya zauna yana amsawa “yasu babana da inna ta” tace “lafiya lau suke, nasan maybe da yamma zadu zo su duba oga Hussain” yace “ohh kema kin fara bin bakin Adam ko? Oga Hussain oga Hassan” ta danyi dariya, Ruqayyah tayi tsaki.
Sumayya tace “ohh har zan manta ma, Baba yace a gaya muku yana gayyatar ku walima” Ruqayyah tace “walima? Walimar menene” Sumayya tace “walimar saukar Adam” Hassan ya bude ido “sauka? Yaushe Adam din ya fara karatu ballantana har ya sauke? Allah yasa dai ba saukar zuƙu yayi ba” Sumayya tace “haba dai, Baba ne fa malamin sa, idan baka yarda ba ma zaka iya kiransa kayi masa exam da kanka” ya gyada kai yace “na yarda, tunda kika ce Baba ai na yarda kuma. Allah yasa na tsoron Allah yayi” Sumayya tace “ameen” Ruqayyah tace “kuma shine Baba zaiyi masa walima?” Sumayya tace “eh fa, Baba da kansa ya shirya masa walimar. Kunsan cewa yake yi shine babban dan Baba” Hassan yace “a’a, ki ja masa kunne ya daina shiga hurumin da ba nasa ba, wannan position din nawa ne sai dai ko ya zama shine na biyu” ya mike tsaye yana cewa “zamu zo insha Allah, kiyi masa murna inji ni, in mun hadu ma zanyi masa da kaina”
Sai daya fita sannan Ruqayyah ta sauke tsakin da take ta rikewa “lallai Baba da barnar kudi, har wata walima za’a shirya wa wani kedari can? A dauri kashi ko a bata igiya?” Sumayya ta bata rai “kinga fa abinda yasa bana son zuwa gidan ki kenan kwanan nan. In dai har kinsan ba zaki fadi alkhairi a kan Adam ba dan Allah kar ki sake maganar sa. Kuma baban kike cewa zaiyi barnar kudi? Kudin ki ne?” Ruqayyah tace “ko ba kudi na bane ba ai kudin mijina ne. Ko kim dauka van san cewa duk wata yana kai wa Baba kudi ba?” Sumayya tace “still ba naki bane ba, in ya kai masa ma ai ba rokar sa yayi ba kuma ko babu kudinsa yana da aikin yi yana daukan albashi zai iya komai da kudinsa. Wai ni in tambaye ki Ruqayyah, menene matsalar ki da Adam ne? Menene laifinsa? Me yasa ba kya sonsa?” Ruqayyah tace “ba son shine bana yi ba, bana son shi tare da ke dan sam baku dace ba wallahi” Sumayya ta mike tana yin hanyar kitchen tana cewa “matsalar ki ce wannan kuma. Ni ina sonsa shi yana sona iyayena suna sonsa dan ke ba kya son sa bani da problem” Ruqayyah ta sake tsaki, dole ta sake shiri na musamman, babu yadda za’a yi ta bari Sumayya ta auri inyamurin drivern kanin mijinta.
An gabatar da walima lafiya, Adam ya gayyaci friends dinsa na gida dana school dinsu, Hussain da Hassan duk sunje sannan Hussain yayi masa kyautar zuwa aikin hajjin bana, murna a gurin Adam kamar bakinsa zai yage, su Baba suna ta taya shi godiya. Ruqayyah bata samu zuwa walimar ba saboda rashin lafiyar da take fama dashi, a jikinta ta fara tunanin ciki ne da ita dan haka tayi home pregnancy test kuma ya tabbatar mata da zargin ta, hakan yasa ta fahimci tun kafin tafiyar su Hassan India cikin ya shiga, amma sai ta boye abinta a ranta saboda tana tsoron kar ta fada ace ba za’a yi tafiyar nan da ita ba, tafi son in anje can a gane, sai ta nuna cewa itama bata san dashi ba. Ko babu komai ta samu abin nunawa Fatima.
Aka kammala duk shirye shirye, ranar tafiya tayi suka tashi gabaki dayan su Aunty, Hassan da Hussain, Ruqayyah da Fatima, Safiyyah, Khadijah, Nafisa, Zulaihat. Tunda suka je suka dukufa gurin gaya wa Allah bukatun su, babbar bukatar su ita ce ta neman lafiya ga Hussain, babban fatan su shine in Hussain ya koma asibiti a tabbatar masa da cewa ya rabu da wannan cancer din. Ruqayyah kam nata bukatun take roka babu ruwanta da wani Hussain, bata rokar masa rashin lafiya ba kuma bata rokar masa sauki ba.