TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Fatima ce ta fara lura da chanjin yanayin Ruqayyah kuma direct ta gaya mata cewa tana zargin tan da ciki, ta kuma raka ta asibiti kamar lokacin cikin Twins sannan kuma aka tabbatar mata da zargin ta. Kowa yayi murna da kasancewar hakan, amma kuma kirikiri suka ringa nuna wa ina ma dai Fatima ce mai cikin amma sai Hussain ya ringa basarwa duk kuwa da cewa duk sujjadar da zaiyi sai ya roki Allah ya bashi magaji kafin ya karbi ransa.
A haka suka gama azumin su, lokaci ya kuma tafiya har lokacin aikin hajji yayi, a lokacin ne Adam da Sumayya wadda Hassan ya biyawa suka taho tare da Hassana, suka hadu da sauran family din suka gabatar da aikin hajjin su sannan kuma suka juyo zuwa Nigeria. Sai dai Hassan da Hussain su ba Nigeria din suka taho ba India suka tafi inda za’a sake duba Hussain dan a tabbatar da warkewar sa ko akasin hakan.
Suna zuwa aka sake yin wani colonoscopy din aka dauki sample daga hanjin Hussain sannan aka tura shi lab dan gwadawa. Fir Hussain yaki zama ya jira result din yace sai dai a aiko masa ta email dan haka kwanan su biyu a India suka bi iyalinsa zuwa Nigeria.
Yana zuwa Nigeria ya tarar Fatima babu lafiya, wai tun a jirgi ta fara amai kuma har yanzu yaki tsayawa. Da kansa ya dauke ta zuwa asibiti “wato da banzo ba zama zakiyi tayi ba zaki je asibiti ba ko Princess?” Tace “ni bana son allura” amma a ranta tsoron ta daya, tana ta saka ran cewa ciki ne da ita tana jin tsoron kar a gwada ta ace babu, wannan heart break din take tsoro, shi yasa duk yadda Aunty tayi da ita akan zuwa asibitin taki yarda.
Tashin farko PT aka rubuta mata, aka yi mata kuma aka bata result sai dai ta kasa budewa, idonta har hawaye ne ya taru a ciki, ta mikawa Hussain tace ya bude, shima tsoron budewar yake yi sai ya mika mata yace ta bude. Doctor din yayi dariya yace “to ni ku bani in bude tunda naga kamar tsoron takardar kuke yi” suka mika masa sannan suka zauna suka zubawa juna ido, doctor din ya karanta yana murmushi sannan yace “to a bani goron albishir da kuma ladan karantawa. You are going to be parents in the next seven months”
Basu san sanda suma tashi suka rungume juna a gaban doctor din ba, Fatima sai kuka, Hussain yana dariya, doctor yace “kar a manta da goron albishir dina” Hussain ya juyo yana kallon sa yace “just name it, ko me kake so in dai ina dashi ya zama naka”.
A ranar kaf gidan babu wanda bai san da labarin cikin nan ba, hatta masu gadi sai da suka sani dan aljihunsu sai da yayi nauyi, rabon kudi har mutanen waje sai da suka samu nasu.
A ranar ne kuma e-mail ya shigo wa Hussain daga doctor.
“Dear Hussain Aminu Abdullahi, we regret to inform you that the operation performed on you was not successful in eliminating the cancerous tumor, it has regrown. We suggest performing another surgery as soon as possible”
Ya rufe e-mail din sannan ya rufe system din tare da kwanciya ya rufe idonsa, mintuna kadan sannan ya bude su ya mike ya dauko diary dinsa da biro ya fara rubutu.
Dear baby .
A yaune aka tabbatar min da cewa kana nan kan hanyar ka ta zuwa duniya, a yaune kuma aka tabbatar min da cewa ni kuma ina kan hanyata ta barin duniya. Tunani na daya shine “ko zan ga fuskar ka kafin in tafi?”
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020The News
Ya rufe diary din da sauri dan ji yayi kamar zuciyarsa ba zata iya cigaba da rubutun ba, sai ya koma ya kwanta yana mai dora diary din akan kirjinsa tare da rufe idonsa yana tunani, Fatima ce ta fara fado masa a rai, tunda doctor ya karanto musu result din PT dinta har yazu ta kasa rufe bakinta dan murna sai yaji baya son ya katse mata murnar ta da wannan mummunan labarin, baya son ya katse mata murnar ta har abada. Zai so ace murmushin da yake kan fuskarta zai dore ne har karshen rayuwarta.
Sai ya dauki wayarsa ya fita valcony tare da rufe kofa, ya kira number din doctor din daya duba shi a Indiya, doctor din was so sympathetic yana kuma jaddada masa muhimmancin komawa a sake yin wani aikin. Bai musa ba ya nuna masa zai dawo as soon as possible amma kuma sai ya roke shi wata alfarma guda daya, alfarmar ita ce yana so ya sake turo masa wani email din stating cewa ya warke completely daga ciwon da yake damunsa “my wife is pregnant, and I don’t want to break her heart” da farko doctor din kin yarda yayi saida Hussain yayi ta nace masa ya kuma tabbatar masa da zai dawo sannan ya amince, washegari da safe kuwa sai ga wani e-mail din da sa hannun doctor din da logo din asibitin da komai amma a ciki an yi bayanin cewa Hussain ya warke completely babu sauran trace na Cancer a tare dashi. Hussain yana samun wannan sai ya koma baya ya goge wancan da aka fara turo masa dashi. Sannan sai ya dauki system din ya tafi dakin Fatima da murmushi a fuskarsa. A palonta ya same ta tana saka turaren wuta, tun daga nesa ya hango annurin fuskarta ya kuma san tun na jiya ne, tun na albishir din doctor ne. Yace “hey princess” ta juyo tana kallonsa tare da kara fadada murmushin ta, sai ta ajiye incent burner din hannunta ta taho gurin sa da sauri. Kafin ta karaso yace “albishirinki” sai ta dakata zuciyarta tana ayyana mata albishir din da zaiyi mata dan ita yanzu bayan sakon doctor na jiya to wani sakon doctor din ne kadai zai faranta mata maybe ma fiye da wancan, dan lafiyar Hussain ta fiye mata komai yawan yayan da zasu haifa. Ta fara kokarin studying fuskarsa dan ta tabbatar da abinda yake mata albishir din akai, sai ya gyada mata kai kamar mai kokarin tabbatar mata da zargin ta sannan ya juyo mata da screen din system din da take hannunsa “read this”.
Da sauri tayi yawo da idanunta akan screen din, tana taking information din at ones sannan tayi tsalle tana rufe baki, idonta kamar zai fado daga fuskarta, haka ma zuciyarta. “Ka warke! Hussain ka warke. Oh my love, ohh Allah na na gode maka, Alhamdulillah” ya ajiye system din yana kokarin rike ta amma taki rukuwa, farin cikin da take ciki yafi karfin tsayawa a guri daya sai ta fara zagaye a palon tana tsalle yana binta har ya samu ya kama ta ya daga ta sama yana zare mata ido “ke! Garin murnar mijinki ya warke kuma shine zaki je ki sabauta shi?” Bata kula fadan da yake mata ba sai ta kama fuskarsa da hannayenta sannan ta fara kissing duk inda ta samu a fuskar, sai shima ya fara dariya a ransa yana hoping ina ma inama? Ina ma farin cikin su mai dorewa ne.
Haka yayi ta juyi da ita a palon sai da suka gaji sannan ya zauna da ita a kan cinyarsa yana nishi “yarinyar nan fa nauyi ne dake wasa wasa” tayi dariya tana juya idonta “kasan dai bani kadai bace ba yanzu ko? Dan haka nauyin ba nawa bane ni kadai” ya dora hannunsa a marar ta “ayyah, bawan Allah za’a yi masa sharri dan anga bashi da baki ko?” Sai ya kai fuskarsa kusa da cikinta yace “hello angel, this is your father speaking, maman ka tana yi maka sharri tace kai dan lukuti ne kamar ta” ta dago kansa tana hararar sa “wace lukutar?” yace “wai da” sai ta dauki pillow ta fara dukansa dashi, ya tashi yayi daki da gudu ta bishi.
A ranar labari ya kai wa duk wanda ake tunanin ya kamata a gayawa cewa result din Hussain ya fito kuma ya warke tas babu sauran abinda yake damunsa. Aunty da kanta ta shirya musu dinner gaba ki dayansu to celebrate the news. Ta ai kawa kowa sakon azo part dinta a ci abincin dare, har Hassana da mijinta da kuma Jabir wanda sati uku ya rage bikin su da Safiyya. Da kuma Ruqayyah da Hassan.