TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Hassan ya bishi da kallo har ya shiga kofar departure hall, sai daya daina ganin sa sannan ya tayar da motar ya bar gurin yana jin part of him ya tafi tare da Hussain. Amma dama ya saba da wannan feeling din, kullum in basa tare da Hussain sai yaji kamar rabin sa ne a gurin rabi kuma yana inda Hussain din yake, tun suna yara haka yake ji, duk fadan su duk rigimar su amma duk duniya babu abinda yake so sama da Hussain, baya jin kuma akwai wani abu da zai raba shi da Hussain.

Direct gida ya koma, yana ta lissafin abubuwan da suke gabansa abubuwan da ya kamata ya yi kafin dawowar Hussain daga Beijing. Dazu dai yayi wa kananan ma’aikatan da za’a dauka aiki a sabon kamfanin interview kuma har ya riga yayi grading dinsu, sai ya zauna zai yi final zabe sannan sai a kira wadanda aka zaba din a sanar musu. Shi komai yafi so yayi a hankali, ya tuna yadda suka yi da Hussain a lokacin da suke maganar daukan ma’aikatan. “Kaga Hassan, don’t stress yourself akan maganar nan. Kananan ma’aikata ake magana fa ba manyan ma’aikata ba, ba takardu zaka duba ba ba komai ba, kawai just look at their physique ka tambaye su akan past experiences dinsu shikenan. Wanda kaga ya dace ka bashi aiki kawai a take wanda bai dace ba ka sallame shi kace masa babu aiki dan kar yaje gida yayi ta saka ran zai samu”

Hassan yace “so kake mu dauki baragurbi kenan mu bar masu kyau? Ai shi lamari na daukan ma’aikata a nutse ake bi ayi interview idan da hali ma sau biyu dan aga mai juriya, ni har medical certificate nake so suje suyi saboda in tabbatar da lafiyar su, sannan sai na zauna a nutse sai in tace wanda naga sun cancanta” Hussain ya mike tsaye yana bude hannu yace “do whatever you want. Ni dai abinda na sani shine, duk wanda Allah ya tsara yana da rabon samun aiki a H and H ko ka bashi yau ko kuma kayi ta delaying sai nan da shekara daya still dai sai ya samu. To gwara ka bashi ka huta shima kuma ya huta”.

Hassan yayi murmushi yana kashe motar bayan yayi packing a compound din gidan su. Tun suna yara kusan kullum sai sunyi irin wannan musun kuma har yau babu wanda ya taba chanza ra’ayin danuwansa.

Ya shiga gidan. A kan dining ya hango yar autar su Zulaihat da takardu a gabanta tana karatu, shirye shiryen ssce take yi dan yanzu haka sun kusa kammala neco sauran su waec. Dama ita kadai ta rage a secondary School sauran yammatan duk suna jami’a dan Hassana har ta kammala ta kuma yi service dinta, ta kuma samu mijin aure dan yanzu so ake yi ma a hada bikin nata dana Hussain.

Zulaihat ta amsa sallamar sa tana binsa da kallo sannan ta kalli bayansa da sauri sai kuma ta sake kallonsa “ina yake?” Ta fada tana kara kallon kofa. Ya jawo kujera a can karshen dining table din ya zauna tare da jawo food warmer din daya gani a gurin, yasan duk gidan sunfi son Hussain a kansa, sunfi sabawa da Hussain saboda ya fi shi faran faran da wasa da dariya, ya fishi kuma kashe musu kudi da shagwaba su, shima kuma yana taya su son Hussain din. Ta sake tambaya “yaya H1 ina yaya H2 yake? Bai dawo daga kanon ba?” Ya fara zuba abinci sannan yace mata “ya tafi China” ta bude ido da baki tana kallonsa sannan ta ajiye littafin hannunta ta tashi a guje ta tafi saman Aunty. Yayi murmushi yana cigaba da zuba abincinsa. Sai daya fara ci sannan yaji saukowarsu kusan gabaki dayansu . Duk suka taho inda yake, Aunty ta zauna a kujera tana kallonsa “ina Hussaini?” Ya dago kai shima yana kallonta yace “ya tafi China, suna kan hanya ma yanzu”.

Ta fara fada “yanzu lamarin Hussain har ya kai haka Hassan? yanzu ni a gidan nan ban ma isa a gaya min in za’ayi tafiya ba ballantana in saka ran za’a nemi izini na kafin ayi? Yanzu har sai yayi tafiyar ma sannan zai aiko ka ka gaya min?” Bai ce komai ba har ta gama fadanta sannan ya ajiye spoon din hannnunsa yana kallonta yace “tsakanin ku ne Aunty, kun fi kusa. Nasan in ya sauka zai kira ki sai ki yi masa fadan. Nima sai dana gaya masa rashin dacewar hakan amma sai yayi min bayanin cewa in ya gaya miki hana shi tafiya zakiyi kuma in kika riga kika hana shi ba zai iya tsallake maganar ki ba, sannan kuma tafiyar mai muhimmanci ce sosai saboda injinan da za’a yi amfani dasu a sabon Companyn yin flour nan su zai siyo, in ya aika kuma za’a iya siyo masa fake shi yasa ya tafi da kansa. Kinsan halin Hussain, he settled for nothing less than the best”

Tayi shiru tana tunani, yayin da yammatan suka fara mita, Safiyya tana korafin ai yayi mata alkawarin tare zasu tafi kuma shine ya tafi ya barta. Aunty tace “yanzu yaushe zai dawo kenan?” Hassan yace “sati daya yace zaiyi” tayi ajiyar zuciya tace “Allah ya kaimu, ya kuma dawo mana dashi lafiya. Ni wallahi na ƙagu azo ayi bikin nan nasa ko zai rage wannan yawon, tunda naga yana son Fatima sosai dole zai ke son zama anan tare da ita” Hassan yayi murmushi yace “in yana son yawon zai iya daukan matarsa su tafi tare, menene a ciki?” Aunty ta bata rai “don’t put that idea into his head” yayi dariya yana bude hannu “nayi shiru. Amma ina tunanin already idea din tana cikin kan nasa sai mu jira ayi auren mu gani. Hussain ne fa, bana jin aure zai saka ya zauna guri daya”

Suka yi shiru gabaki daya, Hassan yana cin abincin sa amma kuma yana jin idon Aunty a kansa, take ya fahimci tunanin me take yi, sai yaji tace “kai kuma fa?” Ya gane me take nufi amma sai yayi keeping blank expression yace “ni kuma me aunty? Ni ma yaushe zan tafi chinan?” Ta hade rai tace “kai ma yaushe zaka yi auren? shine abinda nake tambaya, kai ko budurwar nan ma ta zamani baka da ita, kaki kula duk yammatan da suke sonka”

Nafisa tayi saurin cewa “ai kuwa Aunty akwai wata course mate dina, baki ga yadda take son shi ba, kullum sai ta tambaye ni ina yake” ya harare ta yace “hala bata ga Hussain ba? Am sure tana ganin sa zata ce shi take so bani ba” Aunty tace “Hussain ai ya riga ya samu matarsa, a very good girl from a very good family. Family dinta is one of the best a duk fadin kasarnan. Kai ma ya kamata ka kara kokari ka samo wa Fatima yaruwa” ya shafa kai yace “za’a samo wa Fatima yaruwa Aunty, amma sai a hankali, kuma ba irin Fatima za’a samo ba dan ni bana son abinda yake all covered in gold and praises. Saboda nasan most of the books with good cover basu da good contents. Ni am more interested in the content” Aunty tana girgiza kai tace “ai kuwa ana samu Hassan, ana samun wanda yake da goodness in both the cover and the content, ko ita fatiman ai haka muke fata” ya girgiza kansa yace “I am not going to take that risk gaskiya, nafi son in nayi aure ya zamana har abada, mace daya in na samu irin wadda nake so ta ishe ni har abada. Nafi son in auri mace from a lower background than ours, yadda ba xata ke looking down on us ba, yadda zata ke girma ma ku iyaye na kuma ba zata ke yiwa sisters dina magana anyhow ba kamar yadda take yiwa bayin gidansu. Nafi son wadda duk abinda na bata, no matter how small zata yi appreciating ba zata raina ba saboda ta saba da wanda yafi shi. Nafi son me low life style irin nawa not extravagant kamar Fatima”

Aunty tace “to Allah ya kawo mana ita, Allah yayi muku zabin alkhairi baki daya” ya amsa da ameen. Sun jima suna hira, yana updating dinta akan shirye shiryen bude sabon company, sai gata ta dauko masa wani dogon list wai daga Gombe aka aiko dashi inji uncles da auntys dinsu na mutanen da suke so a dauka aiki. Ya karba kawai yayi murmushi amma shi a ransa yasan babu wanda zai bawa aiki sai wanda ya cancanta sai dai duk abinda za’a ce ace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button