TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Shi arziki ba komai bane ba illa wata hanya da ubangiji yake jarabtar bayinsa, sai ya baka kudi yaga abinda zaka yi dashi ko kuma ya hana ka yaga abinda zaka yi. Ida har ka nemi kudi ka samu to Allah ne ya baka, idan kuma baka samu ba to shine ya hanaka. Idan ka samu dama ka nemi kudi ta hanyar halak, idan zaka kashe su ka kashe su ta halak. Idan kana dashi ka taimaka wa wanda bashi dashi, idan baka dashi ka nemi na kanka ta hanyar halak kar ka zama mai matacciyar zuciya ko mai roko a gurin mutane.
A duk lokacin da dama ta same ka tayin wani abu to kayi shi a lokacin kar ka jira sai wani lokaci, dan ba kai kake da lokacin ba. Duk abinda kaji kana son yi to kayi abinka, as long as bai sabawa ubangijin ka ba kuma ba zai zamanto cutarwa ga wani abin halitta ba ba to kayi abinka kar ka damu da abinda mutane zasu ce dan su mutane ba’a taba iya musu, in kabi ta tasu ba zaka yi achieving komai ba.
Ka zauna da clean heart, kar ka nufi kowa da sharri kar kuma ka rike kowa a ranka, always think positive dan shi negativity yana huda zuciya ne ya kuma hana ka ganin alkhairi ko da yana gabanka
Bana tunanin halin da zan barka saboda nasan na barka da best mother in the world da kuma best father in the world. Na san ko ban bar maka ko kwandala ba Hassan zai iya yin dako ya ciyar da kai. Dan haka indai a kan wannan ne bani da damuwa”
Shigowar Fatima tasa yayi saurin rufe wa, ta tsaya tana kallon sa “wannan diary, ina jin kwanan nan a karkashin pillown ka zaka ke sakawa saboda tsabar baka so a karanta” yace “kar ki damu, shi wanda nake rubutawa da kansa xai karanta miki wata rana. Have patience” ta zauna da kyar tana cewa “Allah y kaimu, a gabanka zai karanta min ai, sai inji in ka rubuta abinda ya shafe ni a ciki” ya taso yana rungume ta ta gefe yace “a duk page da akwai sunan ki Fatima. Idan babu ke babu ni Princess” ta shafa fuskarsa tana murmushi tace “kaima in babu kai babu Fatima ” sai ya dora kansa a kafadar ta ya lumshe idonsa.
Hajiya Ruqayyah an haihu, da namiji na uku kenan data haifawa Hassan kuma tana tutiya a ranta cewa ko a haka ta barshi ta riga ta zamar masa karfen kafa, ta zamar masa kadangaren bakin tulu duk kuwa da cewa a yanzu ta fara fitar da ranta daga dukiyar Hussain musamman bayan ganin tulelen cikin Fatima da tayi duk da bata san me nene a ciki ba amma tana ganin haihuwar Fatima zata kara nesanta ta da H and H. Duk da cewa Hassan yayi signing takardun da Hussain ya bashi amma bai gaya wa kowa ba hatta Aunty, and definitely not Ruqayyah dan yasan in ta sani to kuwa ba zata haihu a Nigeria ba cewa zata yi ya fita da ita waje ta haihu a can. Amma duk da haka sai data matsa masa ya bata uban kudi kawai tayi ta siyan kaya wai na fitar suna, kayan babu kuwa haka tayi su daki guda duk dacewa akwai kayan twins wadansu ko amfani dasu basu yi ba, wadansu kuma kudin data karba kawai a account ta zuba su ta ajiye.
Sai dai duk wannan abin da take dasu bai saka saka farin ciki a zuciyarta ba, kullum ranta babu dadi zuciyarta bakikkirin musamman inta lissafa taga plans dinta duk babu su, Adam din ma da take ta kokarin ganin ta raba shi da yar uwarta har yanzu abin ya gagara sai kara samun karbuwa yake yi a gurin iyayensu da kuma a gurin Hussain, hatta Hassan din data juya wa ra’ayi akan Adam yanzu ya fara chanjawa dan kwana biyun nan har hira taga suna zama suyi su kuma yi dariya. Ta saka ta warware ta kuma saka wa ta kuma warwarewa amma har yanzu ta kasa samun mafita. Then one day, bayan Hussain din ta yayi wata daya a duniya sai taga Hassan yana aiyukan files din staff din da suke dasu a gidan, kowa da file dinsa tun daga kan masu gadi har zuwa masu ban ruwan fulawa. Ta zauna tana taya shi sorting, yana ware wasu wadanda yake so zai yiwa karin albashi a ciki har da Adam, ta miko masa file din ya bude yana going through, anan ne idonta ya sauka akan sunan Adam na gaskiya da kuma address din gidan iyayen sa mahaifa. Anan wani plan ya fara forming kansa a zuciyarta. Bata ce komai ba har suka gama aikin sannan ta tafi dakin ta. Ta kira Minal a waya “Minal ya kike ya nauyi? Dan Allah taimako nake so” Minal tace “taimako? Taimakon me?” Ruqayyah tace “ina neman wanda zan aika kano, a sirri, wanda zan aika din bana son ya san ni zan aike” Minal tayi dariyar “me kika kulla wa?” Ruqayyah tace “ke dai bari, ina ganin na samo hanyar da zan kori wannan yaron daga gidan nan, kuma in raba shi da Sumayya” Minal tace “wanne yaron fa?” Ruqayyah tace “Adam. So nake ki samu wani ki aika shi kano on my behalf, yaje unguwar badawa layout gida mai number 49 ya gaya wa masu gida cewa dansu da suke nema yana kaduna, ya basu address din gidan nan ya gaya musu cewa yana nan ynaa aikin driver”.
Minal tace “ke Ruqayyah! Ji nake kin ce min iyayensa christians ne. In kuma suka tafi dashi suka mayar dashi Christian fa?” Ruqayyah tace “in haka ta faru to na tabbatar dama musuluncin nasa bana gaskiya bane ba, ai in dai da gaske yake to ba zai koma ba. Ni dai ina son in daina ganinsa anan gidan ne kawai, yadda ya gudu daga can ya taho nan haka in suka zo nemansa nan ma zai gudu ya kara gaba” Minal tayi shiru tana tunani, Ruqayyah tace “ni in ba zaki yi min ba ki gaya min in samu wanda zai yi min” Minal tace “babu komai, akwai wani yaron Alhaji Kabiru da nake dan saka wa aiyuka, zan tura shi Kanon” Ruqayyah tayi murmushi “shi yasa nake son ki Aminiya” Minal tace “babu wani Aminiya, yaudhe rabon ki da gida na? Ni kuma kullum ina kan hanyar zuwa gidan ki. Ina son ma zanzo ki raka ni in karasa siyayyar haihuwar nan” daga nan suka cigaba da hirarrakin su.
And so it happened….
Sanda cikin Fatima ya shiga watan haihuwa, a lokacin ne kuma sako ya samu Hussain na dawowar abokin sa Sadiq zuwa garin Abuja tare da balarabiyar matarsa da kuma dan su da suka haifa. Sai Hussain ya shirya da niyyar tafiya yaje ya gano abokinsa da kuma sabon family dinsa, sannan kuma yana son ya ga likitansa daga nan. Tunda yayi maganar tafiyar Fatima take kuka, ita bata so ya tafi, ita so take ta bishi amma kuma cikinta yayi nauyi sosai. “kiyi hakuri Fatima, Abuja ne fa ba wani guri ba, a yau zanje in dawo” amma ta tubure dole ya hakura da tafiyar sai gobe, goben ma ya kuma daga wa sai wata goben a haka har sati, dan haka ya yakice ya tafi da kyar ba wai dan ya damu da ganin abokinsa ba sai dai dan ya damu da zuwa gurin likita, ciwo ya dame shi sosai, ga kuma jini da yake fitarws sosai. Sau da takai shi har bakin mota yayi kissing dinta sannan ya sunkuya yayi kissing cikin sannan ya shiga mota shida Hassan Adam yana tukawa suka tafi.
A hanya suka yi hira sosai da Hassan, hira mai dadi duk da cewa baya jin dadin jikinsa, Adam ma kuma suna sako shi a cikin hirar yana jin labaran irin yarintarsu da kuma abubuwan da suka faru lokacin tasowarsu. A haka har suka iso garin Abuja suka shiga har cikin palace, sai dai kuma fitowa daga mota ya gagari Hussain. Nan take hankalin Hassan ya tashi ainun ya kuma umarci Adam daya juya motar zuwa asibiti, kafin su karasa asibitin jikin Hussain ya rikice gabaki daya dan sai tura shi akayi zuwa dakin likita kuma take aka saka masa oxygen dan numfashin sa sama sama yake fita. In hankalin Hassan yayi dubu to ya tashi gaba ki daya, amma a dole aka cire hannunsa daga na Hussain aka shiga da Hussain ciki shi kuma aka barshi a waje yana jira.